Gombe 2027: Kotu Ta Soke Takarar Pantami…
Daga Wakilinmu

__________
Kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta soke takarar Sheikh Isa Ali Pantami na zama Gwamnan Jihar Gombe a zaɓen shekarar 2027 da ke gabatowa.
Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito, kotun ta umarci Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ta sake gudanar da zaɓen fitar da ɗan takarar Gwamna na jam’iyyar a Jihar Gombe.
Mai Shari’a, Amina Aliyu Mohammed ce ta jagoranci zaman kotun, wadda ta bayar da umarnin a cikin ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar, inda yake ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP.
Garry ya ƙalubalanci fitowar Pantami ne bayan da jam’iyyar ta sanar da shi a matsayin ɗan takararta tilo a ranar 26 ga Yuni, 2026, yana mai cewa ba a gudanar da zaɓen fitar da gwani yadda doka ta tanada ba.
Pantami, wanda ya kasance ɗan takarar neman tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a baya, ya koma PDP ne bayan Jam’iyyar APC ta amince da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takararta.
Daga bisani, Pantami ya samu tikitin PDP, a lokacin zaɓen fitar da ɗan takarar Gwamna na jam’iyyar da aka gudanar a watan Mayu da ya gabata.
Sai dai a hukuncin da Mai Shari’a ta yanke a yau Alhamis, ta umarci PDP da ta sake gudanar da sabon zaɓen fitar da ɗan takarar Gwamna, bisa ƙa’idojin jam’iyyar da kuma dokokin zaɓe da suka dace.
__________












