Al’amuran Tsaro: Musulmin Duniya Sun Taru A Abuja
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
A jiya Talata, Ƙungiyar Musulmin Duniya (Muslim World League) tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) ta Najeriya, ta buɗe wani babban taron ƙasa da ƙasa kan tsaron ƙasa, da nufin lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da dorewar ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a Najeriya.
Ana gudanar da taron ne a Abuja ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Ƙungiyar Muslim World League, Sheikh Dr. Muhammad bin Abdulkarim Al-Issa, inda manyan shugabannin gwamnati, malamai, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki suka hallara domin tattauna ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Daga cikin manyan baki da suka halarci taron akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Haka kuma, gwamnonin Borno, Sokoto, Kaduna da Jigawa da Mataimakan Gwamnonin Yobe da Katsina, sun halarci taron.
Taron ya samu halartar wasu ministocin Gwamnatin Tarayya, ciki har da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; Ministan Lafiya da Jin Ƙai, Farfesa Muhammad Ali Pate da Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu. Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Dijital, Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, shi ma yana daga cikin manyan mahalarta taron.

Haka kuma, manyan malamai da shugabannin addini sun halarci taron, ciki har da Hon. Ali Isah Jesy; Sheikh Ɗalhat Abubakar Hakimi, wanda ya wakilci Sheikh Sani Yahya Jingir; Sheikh Ƙaribullah Nasiru Kabara da Babban Sakataren Jama’atu Nasril Islam (JNI), Dr. Khalid Aliyu. Dr. Ahmed Mahmoud Gumi da sauran manyan malamai da shugabannin addinai ma sun kasance cikin mahalarta.
A ɓangaren sarakunan gargajiya kuwa, taron ya samu halartar wasu manyan sarakuna, ciki har da Sarkin Zazzau, Sarkin Bida, Sarkin Hadejia da Sarkin Maradun.
Taron ya mayar da hankali ne kan nazarin matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta da kuma tattauna hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kan al’umma da tsaron ƙasa.
Masu shirya taron sun bayyana cewa samar da ingantaccen tsaro na daga cikin muhimman ginshiƙan da za su ba da damar samun ci gaba mai ɗorewa a fannonin tattalin arziƙi da zamantakewa, tare da ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummar ƙasar.
__________













