Lionel Messi: Tauraron Da Ya Sauya Tarihin Ƙwallon Ƙafa A Duniya
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
___________
An haifi Lionel Messi a ranar 24 ga Yuni, 1987, a birnin Rosario, ƙasar Argentina.
Tun yana ƙarami ya nuna ƙwarewa ta musamman wajen buga ƙwallo. Sai dai ya fuskanci matsalar ƙarancin sinadarin gina jiki mai sanya girman jiki (growth hormone deficiency). Saboda haka ya koma Makarantar Matasa ta Koyon Ƙwallo Ƙafa ta FC Barcelona Youth Academy (La Masia) a Spain, inda kulob ɗin ya ɗauki nauyin yi masa magani. Daga nan ne ya fara haskakawa, har ya zama ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasa a tarihin ƙwallon ƙafa a duniya.
Messi ya shafe sama da shekaru 20 yana taka leda a matakin ƙoli. Ya yi fice a FC Barcelona kafin daga baya ya koma Paris Saint-Germain F.C., sannan ya koma Inter Miami CF a Amurka.
A duk inda ya taka leda yakan kasance jagora wajen zura ƙwallaye, bayar da taimakon cin ƙwallo da kuma lashe manyan kofuna.
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka bambanta Messi da sauran sa’anninsa, shi ne yawan kambin bahintar da ya kafa. Ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, fiye da kowane ɗan wasa a tarihi. Haka kuma ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan duniya ta FIFA sau da dama, kuma shi ne ɗan wasa mafi yawan lashe Takalmin Zinare (Golden Boots) a nahiyar Turai.
Har ila yau, yana daga cikin ‘yan wasan da suka fi kowa yawan zura ƙwallaye da bayar da agaji domin zura bal, a tarihin ƙwallon ƙafa a duniya.

A tarihin Gasar Kofin Ƙwallon na Duniya (FIFA World Cup), Messi ya fara buga wa ƙasar Argentina a shekarar 2006 (yana matashi). A wancan lokaci ya nuna hazaka amma ƙungiyarsa ta fita a wasan kusa da na ƙarshe. A gasar 2010 kuwa, duk da cewa ya nuna bajinta, Argentina ba ta samu kai wa matakin ƙarshe ba.
A 2014, Messi ne ya jagoranci Argentina zuwa wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya. Ya taka rawar gani sosai, inda ya ci ƙwallaye masu muhimmanci kuma aka ba shi kyautar Gwarzon Ɗan Wasa (Golden Ball). Sai dai Argentina ta sha kashi a hannun Germany da ci 1–0 bayan ƙarin lokaci.
A shekarar 2018, a dai gasar ta Kofin Duniya, wanda aka gudanar a ƙasar Russia, Messi ya sake jagorantar Argentina amma ƙungiyar tasa ta fice tun daga zagayen ‘yan 16, bayan da ta sha kashi a hannun France. Wannan ya sa mutane da dama suka fara tunanin, shin ko zai taɓa lashe kofin duniya.
Sai dai a Gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar, Messi ya rubuta sabon tarihi. Ya jagoranci Argentina zuwa lashe kofin na duniya, bayan doke France a wasan ƙarshe ta hanyar bugun fenareti. Ya ci ƙwallaye bakwai, ya bayar da tallafin cin kwallaye da dama. Haka kuma an sake ba shi kyautar Ƙwallon Zinare (Golden Ball). Wannan nasara ta tabbatar masa da matsayin ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasan da duniya ta taɓa gani.
Zuwa Gasar Kofin Duniya ta 2026, Messi ya ci gaba da kasancewa cikin tawagar Argentina, duk da yawan shekarunsa. Kasancewarsa cikin ƙungiyar na nuna jajircewarsa da kuma ƙwarewar da har yanzu yake da ita. Kwarewarsa wajen jagoranci da gasa wasa, na ci gaba da zama abin koyi ga matasa a faɗin duniya.
Bayan Kofin Duniya, Messi ya kuma lashe Kofin Gasar Copa América tare da Argentina, abin da ya kawo ƙarshen dogon jiran ƙasar na samun babban kofi. An san shi da kwantar da kai, natsuwa da sadaukarwa ga aikinsa. Duk da shahararsa, ya kasance mutum mai nisantar hayaniya kuma yana gudanar da ayyukan tallafa wa marasa galihu ta hanyar gidauniyarsa.
Idan aka yi nazarin rayuwar Lionel Messi gaba ɗaya, za a ga cewa ba hazaƙa kaɗai ta kai shi wannan matsayi ba. Abubuwan da suka samar masa da shahara, sun haɗa da baiwa, aiki tuƙuru, haƙuri, jajircewa da dagewa. Waɗanan halaye ne suka mayar da shi abin koyi ga miliyoyin mutane. Tarihin da ya kafa, kofunan da ya lashe, da tasirin da ya yi a wasan ƙwallon ƙafa, sun sanya sunansa cikin jerin fitattun gwarazan da ba za a manta da su ba a tarihin wasanni, musamman ƙwallon ƙafa a duniya.
__________












