RAMADAN KARIM: 22-1447

‘Yan uwa, ina yi maku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Yau Laraba, Allah ya nuna mana rana ta 22 a Ramadan. Yau ma ga nasiharmu:
‘Yan uwa Musulmi, yau nasiharmu ita ce, mu lizimci koyi da halaye da ayyukan Manzon Allah (saw). Shi ya kasance jagora, limami abin koyi. Ya kasance mai kyawawan halaye, mai kyawawan misalai. Shi haske ne mai haskaka mana rayuwa. Don haka, koyi da shi a dukkan lamurranmu na rayuwa, babban abin kyau ne da kyautatawa.
Allah (swt) a cikin Alkur’ani mai girma, Suratul Ahzab 33:21, yana cewa: “A cikin Manzon Allah akwai kyakkyawan koyi.” Manzon Allah (saw) a Tirmizi, Hadisi mai lamba 2018, ya ce: “Mafi kusanci da ni… mafi kyawun halaye.”
Allah ka sanya mu zamo masu kyawawan ɗabi’u, ka sa mu zamo masu koyi da halayen manzonka kuma ka ba mu lada da albarka a rayuwarmu ta duniya da lahira. Amin-Summa-Amin.
__________













