RAMADAN KARIM: 18-1447

__________
‘Yan uwa, ina yi maku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Yau Asabar, Allah ya nuna mana rana ta 18 a Ramadan. Yau ma ga nasiharmu:
A yau, za mu ja hankalin junanmu ne, domin mu gane girma da tasirin tsarki da tsarkakewa. Tsarki na ruhi da tsarki na zahiri, al’amari ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwar Musulmi. Don haka, aiki ne babba a gare mu, da mu zama masu tsarki a kowane lokaci. Babu wata ibada da za ta samu amsuwa ga Allah sai an yi ta cikin tsarki na haƙiƙa da na zahiri.
Allah (swt) ya yi bayani game da tsarki a cikin Alkur’ani mai girma, Suratul Baƙara 2:222, yana cewa: “Allah yana son masu tsarkake kansu.” Haka kuma a Hadisin Muslim mai lamba 223, an ruwaito Manzon Allah (saw) yana cewa: “Tsarki rabin imani ne.”
Ya Allah, ka sanya mu cikin tsarkakakku kuma masu tsarkakewa a kowane lokaci. Amin-Summa-Amin.
__________













