RAMADAN KARIM: 13-1447

__________
‘Yan uwa, ina yi maku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Bayan haka, a yau Litinin, Allah ya nuna mana rana ta 13 a Ramadan. Yau ma ga ‘yar nasiha:
A yau nasiharmu jan hankali ne dangane da rayuwa da mutuwa. Musamman dai a kullum mu sani, Allah ya halitta mu ne domin bautarsa a nan duniya kuma zaman duniya jarabawa ne. Komai shekarun mutum a cikinta, akwai ranar mutuwa.
Allah (swt) a cikin Alkur’ani mai girma, Suratu Ali-Imran 3:185 yana cewa: “Kowane rai zai ɗanɗani mutuwa.” Haka kuma Annabi Muhammadu (saw) a Hadisinsa, ruwayar Tirmizi mai lamba 2307, yana cewa: “Ku yawaita tuna mutuwa.”
Wannan shi ke nuna mana cewa, a duk abin da za mu aikata a rayuwa, mu tuna da cewa akwai ranar da za mu mutu. Idan mun mutu kuwa, to akwai hisabi, na ƙididdigar abubuwan da muka aikata a duniya, na alheri ko akasinsa.
A lokacin da muke raye, idan muna tunawa da mutuwa, hakan zai saita mana rayuwa, mu lizimci aikata alheri, ba sharri ba.
Ya Allah, ka ɗora mu bisa hanyar daidai, hanyar shiriyarka da ta manzonka (saw). Allah ka sa mu cika da imani, idan lokacinmu ya zo. Amin-Summa-Amin.
__________












