TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

__________
Ali Jita da Sojaboy dukkansu mawaƙan Hausa ne na zamani kuma sun shahara daidai gwargwado a fagagensu na nishaɗantarwa.
A kwanan nan sun yi mabanbantan bayanai game da sana’arsu. A yayin da Ali Jita ya bayyana cewa a matsayinsa na Musulmi, yana da hujja da yaƙinin cewa sana’arsa ta kiɗa, rawa da waƙa HALAL CE. Ya ƙara da cewa yana da yaƙinin zai ma shiga Aljanna a sanadiyar sana’ar tasa.
A ɗaya hannun, shi kuma Sojaboy ya ce shi a matsayinsa na Musulmi, sana’ar da yake ta kiɗa, rawa da waƙa, HARAMUN CE. Ya ƙara da cewa yana son nan gaba ya tuba, ya daina.
Jama’a, shin yaya kuke kallon wannan taƙadda? Kuma a cikin mawaƙan nan biyu, wanne ne ya fi gaskiya? Ku bayyana ra’ayinku a Commercial Section:
👇👇👇













