• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, September 23, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Ƙungiyar Matan Al’ummar Bura Sun Karrama Dr. Bukar Usman Bisa Cika Shekaru 83

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 9, 2026
in Labarai
0
Bura women Celebrate Bukar Usman at 83

Ayarin Wakilan Ƙungiyar BUWDA, ƙarƙashin jagorancin Muƙaddashiyar Shugabar Ƙungiyar, Uwargida Ladu Chimwasu Gali, a gidan Dokta Bukar Usman da ke Unguwar Maitama, Abuja, a yayin da suka miƙa masa Kanbin-Zayyana (Roll-up banner), domin taya shi murnar cika shekaru 83. Hagu-Dama: Mrs Rejoice Rufus Ngada - Ma'ajiyar Ƙungiya, Mrs. Hassana Gana Dibal - Mai Ba Da Shawara, Mrs Ladu Chimwasu Gali - Muƙaddashiyar Shugabar Ƙungiyar, Dr. Bukar Usman, Mrs. Sheri Arhyel Ibrahim - Jami'ar Walwala da kuma Mrs. Violet Haman Ndahi - Sakatariyar Yaɗa Labarai (Hoto: Disamba 14, 2025)

86
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ƙungiyar Matan Al’ummar Bura Sun Karrama Dr. Bukar Usman Bisa Cika Shekaru 83

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Hoton Dokta Bukar Usman, OON, a ranar da ya cika shekaru 83 (10-12-2025).

 

                      __________

Ƙungiyar Bunkasa Rayuwar Matan Al’ummar Bura (Bura Women Development Association – BUWDA), ta ziyarci shahararren marubuci kuma ƙwararren masanin tsaro, Dokta Bukar Usman, OON domin taya shi murna da farin cikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Marubucin, wanda a ranar 10-12-2025 ya cika shekaru 83 a duniya, ya amshi baƙuncin shugabannin ƙungiyar matan ta BUWDA a gidansa da ke Unguwar Maitama, Abuja, waɗanda suka miƙa masa kyautar kanbin-zayyana (roll-up banner) mai ƙayatarwa a matsayin abin tunawa da taya murna.

A rahoton Hukumar Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN), Bukar Usman wanda aka haifa a shekarar 1942 a Biu, Jihar Borno, tsohon Babban Sakataren ne a Fadar Shugaban Ƙasa kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Adabin Gargajiya ta Najeriya (Nigerian Folklore Society – NFS), sannan kuma Shugaban Gidauniyar Dr. Bukar Usman.

Uwargida Ladu Gali, Muƙaddashiyar Shugabar Ƙungiyar BUWDA, yayin miƙa kyautar a Abuja, ta yaba wa Usman bisa jajircewarsa wajen tallafa wa rayuwar mabuƙata da masu rauni a cikin al’umma da kuma gudunmawar da yake bayarwa wajen karewa da bunƙasa al’adu masu tarin daraja na ƙasar Bura.

Rubutun da ke jikin zayyanar, shi ne: “Ya ranka ya daɗe, Dr. Bukar Usman, Ubanmu, Kawunmu kuma Jagoranmu, mutum mai dattaku da gaskiya. Muna taya ka murnar wannan babbar rana ta zagayowar haihuwarka.

“Kai wata kyauta ce daga Allah ga ƙasar Bura. Mutum mai tsoron Allah kuma mai halaye abin koyi. Shugaba nagari, jajirtacce kuma abin dogaro, mai kulawa da tausayi.

“Yayin da kake bikin wannan rana ta musamman, muna roƙon Allah ya yi maka dukkan nau’o’in albarka, fiye da abin da zuciyarka ta taɓa muradi.

“Allah Maɗaukakin Sarki ya ƙara maka lafiya da kwanciyar hankali. Ya kuma cika maka burin zuciyarka, yayin da kake tsufa cikin yalwar rahamarsa. Amin.”

A nasa ɓangaren, yayin da yake tattaunawa da Hukumar Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN), Usman ya nuna godiyarsa ga wakilan Ƙungiyar BUWDA, bisa kyakkyawar ƙauna da sadaukarwar da suka nuna wajen taya shi murna.

Usman ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa tsawaita masa rayuwa zuwa wannan lokaci da kuma albarkar da Allah ya yi masa da iyalansa gaba ɗaya. Ya shawarci abokan zamaninsa da su kasance masu godiya ga Allah bisa ni’imar tsawaita rayuwarsu, duk da ƙalubalen da duniya ke fuskanta a yau.

Ya jaddada cewa suna buƙatar ƙarin albarka daga  Allah a ranaku, watanni da shekarun da Allah Ya ƙaddara musu nan gaba. Ya yi addu’ar Allah ya zuba albarka mai yawa a kan matasa. A cewarsa, duniya na ƙara zama kamar ƙauye guda ɗaya kuma tasirin da ke fitowa daga muhalli na kusa da na nesa, mai kyau da mara kyau, na iya zama mai ƙarfi ƙwarai.

Ya ce: “Babban nauyin gwamnati ne ta magance wasu matsalolin da ke shafar tsaro da jin daɗin al’umma. Ina kira ga gwamnati da ta ba da fifiko ga walwalar jama’a da tsaron rayukansu, tare da tabbatar da  samar da cigaba na bai ɗaya ga kowa da kowa a ƙasar nan.”

Ambasada Abdullahi Shehu, a nasa saƙon girmamawa ga Dr. Usman, ya bayyana ranar a matsayin wani muhimmin mataki a cikin fiye da shekaru 80 na rayuwarsa. Ya ce: “Cikar shekaru 83 abin ban sha’awa ne, domin abu ne mai wuya mutum ya kai waɗannan shekaru har 83 cikin armashi kuma abin koyi.

“Ina taya ka, iyalanka da masoyanka wajen gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa rahamarsa a kanka da iyalanka. A matsayinka na shugaba a hidimar jama’a, ka bar gagarumin tarihi a fagen aikin gwamnati da kula da tsaro musamman a Najeriya kuma sunanka ya riga ya shiga cikin shafukan tarihin ƙasa.

“A matsayinka na jagoranmu, ba za mu taɓa gajiya da gode maka bisa tarbiyya da koyarwar da kake ba mu ba. Allah ya ci gaba da yi maka albarka da tsawon rai cikin ƙoshin lafiya da lafiyayyen hankali.”

NAN ta ruwaito cewa daga cikin waɗanda suka taya shi murna, akwai ’yan uwansa na jini a gida da ƙasashen waje, abokai da masu yi masa fatan alheri, ciki har da ƙungiyoyi da kamfanoni daban-daban.

__________

Previous Post

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)

Next Post

A Review of Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

Related Posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)
Labarai

Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)

August 31, 2026
Next Post
A Review of Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

A Review of Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gwamnatin Tinubu Za Ta Fifita Amfani Da Na’urorin Zamani A Gidajen Rediyo Sa Talabijin – Minista

Gwamnatin Tinubu Za Ta Fifita Amfani Da Na’urorin Zamani A Gidajen Rediyo Sa Talabijin – Minista

October 26, 2023

October 5, 2023
Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madallah

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madallah

July 28, 2023
A Review of “Leadership in the Nigerian Civil Service…”

A Review of “Leadership in the Nigerian Civil Service…”

July 8, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.