Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
√ Anya Kuwa Ba Hausawan Bogi Ba Ne Suke Satar Mutane Zuwa Kudu?
An daɗe ana sace yara daga Arewa, ana kai su Kudancin Najeriya, musamman ma yankunan Ibo, inda ‘yan Ƙungiyar IPOB ke gudanar da aika-aikarsu. A makon nan ma ‘yan sanda a Jihar Kaduna sun kama mutane uku da ake zargi: Jonathan John, mai shekaru 25, Oliver Magaji, mai shekaru 27 da Bitrus Sawaba, mai shekaru 23.
Kafin tsunduma cikin sharhi, bari mu karanta cikakken labarin yadda al’amarin ya faru, kamar yadda CSP BENJAMIN HUNDEYIN, anipr, mipra, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Abuja ya bayyana, a ranar 7 ga Janairu, 2026. Ga labarin:
•••••••
Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya ta daƙile wani yunƙurin kai hari tare da shirin sace yara a yankin Kasuwanlr Magani na Jihar Kaduna.
A ranar 5 ga Janairu, 2026, da misalin ƙarfe 8:00 na dare, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna ta samu sahihin bayanan sirri cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suna shirin kai hari tare da sace yara daga cikin motocin da ke wucewa ta yankin. Bayan an samu wannan bayanin sirri, nan take aka tura Jami’in ’Yan Sanda mai kula da sashen (DPO) na Kasuwan Magani tare da tawagar jami’an ’yan sanda zuwa wurin.
Da isar su, ’yan sandan sun yi artabu da waɗanda ake zargi, inda suka samu nasarar korar su tare da ceto yara 76, maza da mata, masu shekaru tsakanin 7 zuwa 20. Dukkan yaran da aka ceto ba su samu wata illa ko rauni ba.
A yayin wannan aikin, an kama mutane uku da ake zargi: Jonathan John (namiji) mai shekaru 25, Oliver Magaji (namiji) mai shekaru 27, da Bitrus Sawaba (namiji) mai shekaru 23.
Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna jigilar yaran ne zuwa wasu sassan ƙasar nan domin aikin bauta da sauran ayyukan gida. A halin yanzu, waɗanda ake zargin suna tsare a hannun ’yan sanda, yayin da yaran da aka ceto ake kula da su cikin tsaro a Hedikwatar Rundunar Jihar, har zuwa lokacin da iyayensu ko masu kula da su za su iso domin tantancewa da tabbatar da su yadda ya kamata.
A halin da ake ciki, an fara bincike domin gano cikakkun bayanai game da lamarin da kuma kama sauran masu hannu a ciki. Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya ta sake jaddada ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyi, tare da roƙon jama’a da su ci gaba da bai wa ’yan sanda haɗin kai ta hanyar bayar da sahihin bayanai a kan lokaci domin taimaka wa aikin tsaro.
√ Abubuwan Lura:
Daga wannan babban aiki da ‘yan sanda suka gudanar a Jihar Kaduna, akwai abubuwan lura da ke nuna cewa idan aka zurfafa bincike, akwai yiwuwar a gano hannun ‘yan ƙungiyar IPOB da Hausawan Bogi a ciki. Wannan kuwa saboda ganin yadda ƙungiyoyin biyu ke musharaƙa da juna.
Haka kuma, misali da a ce ba a tono asirin mutanen nan ba, da nan da nan za su fara yaɗa farfaganda suna ɗora wa ‘yan bindigar Fulani laifi. Amma sai Allah ya taimaka aka kama su kuma dukkansu ba Fulani ba ne kuma ba Musulmi ba.
Wannan ya tuna mani da wata muƙala da shafin “Hausaland Magazine” ya wallafa a Facebook. A muƙalar, wacce aka rubuta da Ingilishi, an yi tsokacin cewa wai lokaci ya yi da Matasan Hausawa za su fara ɗaukar makami, domin wai kare kansu daga barazanar Fulanin Daji. A muƙalar, an wallafa hotunan wasu matasa, suna rataye da bindigogi. Da zarar mutum ya nazarci hotunan matasan nan, gane cewa lallai ba Hausawan gaske ba ne, wasu ƙabilu ne dai suka yi basaja, domin shafa wa Hausawan gaskiya kashin kaji. (Akwai hotunansu a ƙasan sharhin nan).

Ya zuwa yanzu dai muna ta ƙara samun ingantattun bayanan da ke tabbatar mana cewa lallai mutanen nan da suke ta ƙumajin zagin Mujaddadi Ɗanfodiyo, ba mutanen kirki ba ne, ba Hausawan gaskiya ba ne, ba Musulmi ba ne. Shi ya sanya suke liƙa wa kansu sunayen bogi na Hausawa Musulmi, domin yaudara da Ba-Zata. Shi ya sa suke kulle bayanan shafukansu a Soshalmidiya. Haka kuma wasu da yawa daga cikinsu, ba ma a nan Najeriya suke zaune ba.

√ Addu’armu A Kan Dukkan ‘Yan Ta’adda:
Muna roƙon Allah ya ƙara ba jami’an tsaronmu sa’a, su kawo ƙarshen duk wasu ‘yan ta’adda da ke ɗaukar makamai suna cutar da al’umma a ƙasar nan, kowane ne su – ko Fulani ne, ko Larabawa ne, ko Turawa ne, ko Yahudawa ne, ko Hausawa ne, ko Birom ne, ko Katafawa ne, ko Ibo ne, ko Yarabawa ne, ko Angas ne, ko Bajju ne, ko Musulmi ne, ko Kirista ne, ko Maguzawa ne. Amin-Summa-Amin!
_____________












