• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 6, 2026
in Gizago
0
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)
29
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Malami da ɗalibansa a Arewacin Najeriya

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

__________
√ Ko Me Ya Sa ‘Ya’Yan Ƙungiyar Hausawa Suke Suka Da Zagin Ɗanfodiyo (RTA)?
Assalamu alaikum, ya ku ‘yan uwa masu bibiyar tsokacin nan da haƙuri. A yau za mu ci gaba da tattauna al’amarin ‘ya’yan Ƙungiyar Hausawa Zalla, Hausawan Bogi, ‘yan Ba-Zata.

Kamar yadda na faro bayani a tsokaci nan kashi na 5, yau ma zan ɗora da tambayar da ta danganci Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo (RTA), wanda ingantaccen tarihi ya yi masa adalci, a matsayin wani babban jigon da ya jaddada Musulunci kuma ya kafa babbar daular da ta yi shuhura a Afrika ta Yamma. Daular a a yau ta shafe sama da shekaru 200 amma har yanzu ruhinta ne ke da tasiri a Musulunci, ba a na gida Najeriya ba, har da sassa daban-daban na nahiyar Afirka.

Har yanzu dai muna tambaya, shin wane dalili ne ya sanya masu ƙumajin kafa Ƙungiyar Hausawa Zalla suke sukar wannan bawan Allah kuma suke ci masa mutunci, suke ƙirƙirar tarihin ƙarya, suna jingina masa? Shin a wannan zamani, wane laifi ya aikata da ya cancanci a ci masa mutunci? Me ya sanya suke sukar tsarin Musulunci da Musulmi kuma suke kira da a koma tsarin Maguzanci a mu’amala ko addini? Me ya sanya suke goyon baya tare da bayar da kariya ga ƙungiyar masu kishin kafa ƙasar Biyafara (IPOB), har ma suke nuna adawa da yadda aka hukunta ɗan ta’addan shugaban ƙungiyar, Nnamdi Kanu? Me ya sanya suke goyon bayan wasu ƙabilun Middle Belt, waɗanda suka yi ƙaurin suna wajen tada hargitsi kuma suke kashe Musulmi a lokuta daban-daban a yankunansu? Me ya sa suke ta ƙoƙarin ɗabbaƙa muguwar aƙidar ƙabilanci a Arewa, musamman tsakanin ƙabilun Fulani da Hausawa, waɗanda su suka fi kusa da juna, musamman saboda ‘yan uwantakar addinin Musulunci?

Ga duk mai tu’ammali da kafafen Soshalmidiya, tabbataccen abu ne cewa, zai ga yadda ‘ya’yan ƙungiyar nan suke zaƙewa wajen cin mutunci ga Mujaddadi da dukkan waɗanda suke da dangantaka da shi, tun daga kan ƙabilarsa ta Fulani; har zuwa kan Sarkin Musulmi na yanzu, Mai Alfarma, Sultan Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III. Haka kuma, mutum zai ga yadda suke kushe addinin Musulunci, kai tsaye ko kuma a kaikaice. Haka kuma suna bin dukkan malaman Musulunci da sharri da cin mutunci. Mun ga yadda suka riƙa tozarta marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da marigayi Sheikh Albani Zariya da marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da marigayi Sheikh Mahmud Gumi da magajinsa, Dokta Ahmad Gumi. Haka kuma Hausawan Bogi, ba su bar Sheikh Ibrahim El-Zakzaki ba, ba su bar Sheikh Bala Lau ko Kabir Gombe ko Sheikh Yahya Jingir da sauransu ba. Suna kunshe su da cin zarafinsu, wai domin su Fulani ne! Anya kuwa Bahaushe kuma Musulmi zai ƙarfafa ƙabilanci a kan Musulunci? Da sake, wai an ba mai kaza kai!

Ko a kwanakin baya, mun ci karo da wani bidiyo yana yawo, inda wata mai suna Kaltume, wacce take kwarmata cewa ita ce shugabar wannan ƙungiya ta Hausawa Zalla ta duniya baki ɗaya, tana furta baƙaƙen maganganu game da Musulunci da Musulmi. A bidiyon, ta fito ƙarara tana faɗin cewa a yanzu ita kafura ce, ta bar Musulunci. Har ma ta yi kira ga Hausawa, wai daga yanzu su daina amfani da kalmomin Larabci wajen sallama. Ta ce, maimakon a riƙa cewa “Assalamu alaikum…” sai dai su riƙa cewa “Gafaran ku dai…” Wannan ke ƙara nuna maka cewa, lallai wannan ƙungiya ba don ci gaban al’umma aka nufa da ita ba. Duk dai wanda ya ga Bahaushe na ƙwarai, to ya ga Musulmi. To me ya sa waɗannan “Sababbin Hausawa” suke son su fitar da al’ummar Hausawa daga addinin Musulunci kuma suke ƙumajin mayar da su zuwa duhun jahilcin Maguzanci da Ƙabilanci?

Ya ku Hausawan Bogi, ‘yan Ba-Zata, ‘ya’yan Ƙungiyar Hausawa Zalla, an fa yi walƙiya, duk wani mai hankali ya gano wallenku. Babbar manufarku dai ita ce, haddasa fitina tsakanin al’umma, musamman al’ummar Hausawa da Fulani, waɗanda tun taletale ‘yan uwan juna ne ta fuskar zamantakewa da addini da ma auratayya tsakanin juna.

Ya zuwa yanzu dai mun gano cewa babban burinku shi ne, ku wargaza al’ummar Arewa, ku haddasa gaba da tsanar juna tsakanin al’umma. Burinku ne kuma ku yaƙi addinin Musulunci da Musulmi. Dalili ke nan kuka ɓullo da alayen kishin Hausawa, domin ku yi ɓadda-bami, ko kuma abin da ake kira”BA-ZATA,” domin ku shammaci mutane, ba tare da sun yi aune ba. Wannan a zahiri yake, domin babu wani Bahaushe na gaskiya da zai fito fili ya zagi Sheikh Ɗanfodiyo da sauran malaman Musulunci. Babu Bahaushe Musulmi da zai aminta da cewa ya koma addinin Maguzanci ko ya ƙarfafa ƙabilanci. Babu Bahaushen ƙwarai kuma ɗan Arewa da zai nuna kishi da goyon baya ga Nnamdi Kanu da ƙungiyarsa ta IPOB, wacce ta yi suna wajen halaka al’ummar Arewa. Haka kuma babu wani Bahaushen gaskiya da zai riƙa jin daɗi da nuna goyon baya ga wasu ƙabilun Middle Belt, waɗanda suka yi suna wajen tare hanya suna kashe Hausawa da Musulmi.

Jama’a, yau ma a nan zan dakata. Ina sha Allahu a kashi na 7, zan ci gaba, inda za mu duba matsayin Fulanin Daji ‘yan ta’adda da kuma dangantakarsu da sauran al’ummar Arewa da kuma matakin da ya kamata a ɗauka a kansu da ma dukkan wani mutum da ya zaɓi ta’addanci, ko shi Balarabe ne ko Bature ko Inyamuri ko Bakatafe ko Birom ko Bahaushe ko Bafulatani; kai ko ma wane ƙabila ne shi kuma komai nasabarsa da ɗaukakarsa.

A ci gaba da bibiyar mu da haƙuri. Ku huta lafiya.
_______________

Previous Post

Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba

Next Post

Bura women Celebrate Bukar Usman at 83

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Bura women Celebrate Bukar Usman at 83

Bura women Celebrate Bukar Usman at 83

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KHALID IMAM: Tattaunawa Da Marubuci Mai Hannu Da Yawa

KHALID IMAM: Tattaunawa Da Marubuci Mai Hannu Da Yawa

October 15, 2023
Sarkin Gobir: ACF Demands Thorough Investigation and Security Overhaul

Sarkin Gobir: ACF Demands Thorough Investigation and Security Overhaul

August 23, 2024
No, Mr. President: An Open Letter to Donald J. Trump

No, Mr. President: An Open Letter to Donald J. Trump

November 1, 2025
Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

October 5, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.