• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, June 9, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

TSOKACINMU NA MAKO

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 28, 2025
in Addini
0
Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

Musulunci daban, Ƙungiyanci daban!

47
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Musulunci daban, Ƙungiyanci daban!


                           •••••••
Na zaɓi in ɗan yo tsokaci ne dangane da maganar da na yi jiya, inda na ce na ƙara tabbatar da cewa lallai ƙungiyanci a addini sharri ne ga al’ummarmu, ba alheri ba.

Shin wane dalili ne ya sanya na faɗi haka? Shi ne yadda na ga al’ummarmu ta saki hanya. Maimakon mu gudanar da Musulunci yadda Manzon Allah (saw) ya koyar da mu, sai muka zaɓi bin ƙungiyoyi. A kan haka na ankara da yadda kowane ɗan ƙungiya ke bautar ƙungiya da kare muradunta da malamanta, koda kuwa sun saɓa da muradun Allah da manzonsa.

Misali, na yi nazarin yadda lamura ke kasancewa a ƙungiyance. A duk lokacin da wani alheri ya samu ɗan Izala, to ‘yan Izala ne kaɗai suke murna. Haka kuma idan wani abin alhini ya faru da ɗan Ɗarika, to za ka ga ‘yan ɗarika ne kaɗai suke alhini da jajantawa. Haka abin yake ga ‘yan Shi’a ko ‘yan Ƙur’aniyyun da sauran ƙungiyoyi.

A can baya, al’amura sun gudana, waɗanda suka ƙara tabbatar da haka. Misali, a lokacin da Shiekh Nasiru Kabara ya rasu, ‘yan Ɗariƙa kaɗai suka fi nuna alhini, yayin da ‘yan Izala suka yi ko oho. Wasu ma har suka riƙa munana magana a kansa.

Haka kuma, a lokacin da ‘yan ta’adda suka kashe Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da Sheikh Albani Zariya; ‘yan Izala aka bari da alhini. A lokacin, wasu daga ‘yan Shi’a da ‘yan Ɗarika, ba su nuna damuwa ba. Hasali ma, wasu daga cikinsu murna suka riƙa yi, har suna furta munanan kalamai.

A lokuta daban-daban ibtila’i ya sha faɗa wa ‘yan Shi’a. Misali, a lokacin mulkin Goodluck Jonathan, sojoji sun kashe wa Sheikh Alzakzaki ‘ya’yansa biyu a sakamakon wata hatsaniya a Zariya. Haka ma a lokacin mulkin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, a sakamakon hatsaniya tsakanin sojoji da ‘yan Shi’a a Zariya, an harbi Sheikh Zakzaki da matarsa kuma da dama daga membobinsa suka rasa ransu. A wannan lokacin, ‘yan Izala murna suka yi ta yi, har ma da kausasa kalamai a kan waƙi’ar.

Wani misalin kuma da ya shafi abin alheri shi ne, Gwamnatin Buhari ta naɗa Sheikh Pantami da Malam Adamu Adamu muƙamin ministoci. ‘Yan Izala suka yi ta taya shi Pantami murna, suka yi ta sukar Adamu Adamu, kasancewar shi ɗan Shi’a ne. Su kuma ‘yan Shi’a da ‘yan Ɗarika suka yi ta sukar Pantami. Haka ma a lokacin da aka naɗa Farfesa Ibrahim Maƙari Limamin Babban Masallacin Ƙasa na Abuja, ‘yan Izala suka yi ta gunewa tare da kausasa kalamai a kansa.

Misali na baya-bayan nan shi ne, rasuwar manyan malamai biyu, Sheikh Abdul’aziz Dutsen Tanshi Bauchi da kuma jiya da shi ma Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, Allah ya amshi ransa. ‘Yan Ɗariƙa da ‘yan Shi’a da ma wasu sashi na ‘yan Izala, murna suka yi ta yi tare da kausasa kalamai a lokacin rasuwar Sheikh Abdul’aziz. Yanzu kuma tun daga jiya da aka sanar da rasuwar Sheikh Ɗahiru, wasu ‘yan Izala sun tashi haiƙan da murna da munanan kalamai. Kaico!

Babban abin takaici shi ne, dukkan waɗannan abubuwa suna faruwa ne a sakamakon ƙungiyoyi da ƙungiyanci a addinin Musulunci. Babbar ayar tambaya a nan ita ce, shin haka Musulunci ya tanadi mu yi? Shin Manzon Allah (saw) da sahabbansa managarta, haka suka gudanar da rayuwar Musulunci, a rarrabe, a cikin ƙungiyoyi?

Magana ta gaskiya wacce malamanmu sun sani kuma nagartattun Musulmi sun sani, Musulunci guda ɗaya ne kuma Manzon Allah (saw) da sahabbansa Musuluncin nan guda ɗaya suka yi, bisa hanyar Allah guda ɗaya – ba su rarraba cikin ƙungiyoyi ba. To, mu Musulmin yau, wane dalili ne ya sa muka rarraba cikin ƙungiyoyin Izala, Ɗariƙa, Shi’a, Ƙur’aniyyun da sauransu kuma muke gaba da ƙiyayya da juna? Allah (swt) a cikin Alkur’ani mai girma, Surat Al-Imran, Aya ta 103, yana cewa: “Ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya, kuma kada ku rarrabu.” Shin ina za mu kai wannan mashahuriyar aya?

Kuma Manzon Allah (saw) ya hane mu ga bin ƙungiyoyi da rarrabuwar kai a addini. A hadisin Abu Dawud da Tirmidhi, sun ruwaito Manzo (saw) yana cewa: “Duk wanda ya rabu da jama’a da yatsan hannu kaɗan, ya cire igiyar Musulunci daga wuyansa.” Haka kuma a Sahih Muslim, Manzo (saw) ya ce: “Wanda ya fita daga bin shugabanci, ya rabu da jama’a, har ya mutu, to ya mutu irin mutuwar jahiliyya.”

Kada fa mu manta, shi kansa Musulunci, Allah ya kawo mana shi ne domin ya shiryar da mu rayuwa mai kyau. Allah ya aiko Manzonsa, Muhammadu (saw) a matsayin rahama ga dukkan halittu. Mu duba aya ta 107 a Surat Al-Anbiya, inda Allah (swt) yake cewa: “Ba mu aiko ka ba (ya Muhammad) face rahama ga dukkan duniya.” To, jama’ar Allah, me ya sa muke kore wa junanmu rahama da tausayi? Me ya sa za mu yi ta kyara da la’antar juna a cikin ƙungiyoyin Izala, Shi’a, Ɗariƙa da sauransu?

Magana ta gaskiya, Musulunci addini ne na sassauci da yafiya ga al’umma. A Hadisin Bukhari da Muslim, Manzon Allah (saw) yana cewa: “Masu yi wa mutane rahama, Mai Rahama (Allah) zai yi musu rahama. Ku yi wa mutane rahama, wanda yake sama zai yi muku rahama.” Haka kuma a hadisin Tirmidhi, an ruwaito Manzo (saw) yana cewa: “Ka ji tsoron Allah a duk inda kake kuma idan ka aikata laifi, ka bi shi da kyakkyawa ta share sa, ka mu’amalanci mutane da kyakkyawan hali.”

Wannan ke nuna mana cewa ana buƙatar mu kasance masu yi wa juna rahama, mu zama masu ba juna uzuri da yi masu yafiya a inda suka saɓa mana. Wannan zai sanya mu kasance cikin lumana da juna kuma Allah shi ma ya yafe mana, ya yi mana rahama, tun da mu ma muna saɓa masa.

Kuma wani abu da ya kamata mu ƙara fahimta gane da Musulunci shi ne, addini ne na maslaha da kyawun ɗabi’a. A ƙa’ida, mutum ko ba Musulmi ba ne, babu dalilin da za ka munana masa ko ka kyare shi. Ita kanta nasiha ko wa’azi domin gyara, ana so malami ya yi amfani da usulubi mai kyau, ya kyautata harshe ba da tozarci ba. Kuma Manzon Allah (saw) ya hane mu da tozarta mutane, ya hane mu da tozarta mamatanmu. A Sahih Bukahri, hadisi mai lamba 1393, Manzon Allah (saw) ya umurce mu da cewa: “Kada ku zagi matattu, domin sun riga sun kai ga abin da suka aikata.”

To jama’a, maganar gaskiya mun daɗe da sauka sholda. Mun yi kuskure a baya kuma muna cikin kuskure har yanzu. Ya kamata mu natsu, mu koma ga Allah da Manzon Allah. Mu dawo daga rakiyar ƙungiyanci. Mu kama MUSULUNCI ƊAYA – HANYAR ALLAH ƊAYA – KADA MU RARRABA.

Ya Allah ka amshi uzurinmu, ka yafe mana, ka ɗora mu bisa shiriyarka, shiriyar manzonka (saw) har zuwa ƙarshen rayuwarmu. Amin-Summa-Amin!
_______________

Previous Post

GOBARA DAGA KOGI: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Gwamnatin Amurka

Next Post

Global Standards and Regional Realities: The Evolution of Anti-Money Laundering… Under Review

Related Posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
Addini

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba
Addini

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Mu Ji Tsoron Allah
Addini

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
Next Post
Global Standards and Regional Realities: The Evolution of Anti-Money Laundering… Under Review

Global Standards and Regional Realities: The Evolution of Anti-Money Laundering... Under Review

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

EXTINCTION

EXTINCTION

January 1, 2025
Daura Gidan Tarihin Hausa

Daura Gidan Tarihin Hausa

October 30, 2025
Janar Buratai: Sarki Mai Littafi

Janar Buratai: Sarki Mai Littafi

July 6, 2023

Uƙubar Da Talaka Ke Ciki Ta Isa Haka Nan – ZAINAB AHMAD

August 12, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido
  • Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji
  • Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

June 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.