TAKAICI: Waɗannan… Duk A Cikin Mako Ɗaya?
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
A Najeriya muna ganin ta kanmu! Abubuwan takaici suna ta faruwa babu ƙauƙautawa kamar gilmin walƙiya. Shin yaya za mu kira waɗannan abubuwan takaici na rashin tsaro da suka faru cikin mako ɗaya a jihohin Kano da Zamfara da Kwara da Kebbi?
A cikin mako ɗaya, ‘yan ta’adda suka halaka shugaban Jam’iyyar APC, Umar Moriki a Jihar Zamfara.
A cikin ɗan tsakani kuma sai ga mummunan labarin yadda ‘yan ta’addar ISWAP suka kama Birgediya-Janar, suka halaka shi kuma suka yaɗa hotunansa a intanet.
Ana cikin wannan jimami, kuma sai ga labarin ‘yan bindiga sun kai samame makarantar mata a Jihar Kebbi, suka kashe Mataimakin Shugaban Makaranta, suka yi awon gaba da yara 25.
Duk dai a cikin wannan mako ɗaya, ‘yan ta’adda sun shiga garin Patigi a Jihar Kwara, suka kashe jami’in ɗan sanda da ɗan banga, sannan suka kama shugabannin al’umma biyu, suka tafi da su.
Wani abin ƙarin takaici kuma shi ne, labarin sakacin da ke tattare da lamarin ‘yan ta’adda a ƙasar nan. Misali, shin wane dalili zai sa gwamnati ta zura wa mutanen da ke kashe mutane ido? Maimakon a kama su, a hukunta su, sai a ce wai za a yi sasanci da su. Muna gani za su shigo wajen sasanci da makamansu, cikin kakin soja. A gama magana da su, su tarkata makamansu, su koma daji da su.
Haka kuma, mun samu labarin irin sakaci da wasa da rayukan mutane da aka yi, a yayin da aka gaza ceto Janar M. Uba, har sai da ‘yan ta’adda suka kama shi suka halaka. Abin tambaya shi ne, wane ne ya yaɗa saƙon maɓoyar Janar a Soshalmidiya, har ta kai ga ‘yan ta’adda sun cin masa?
Mun samu labarin cewa akwai babban sakacin tsaro a Makarantar Mata ta Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu. An samu tabbacin cewa jami’an tsaro sun bar makarantar kimanin minti 30, sannan ‘yan ta’addar suka mamaye makarantar kuma suka yi ɓarnarsu ba tare da wani mataki ba. Kuma kamar yadda Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya faɗa, ya ce an sanar da jami’an tsaro bayanan sirri, cewa akwai barazanar tsaro a makarantar, amma suka ƙi ɗaukar mataki, har sai da ɓarnar ta faru. Wannan sakaci daga jami’an tsaro, irinsa ne ya faru a Gidan Mantau na Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina a kwanakin baya, kamar yadda Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya tabbatar.
Ya kamata dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tashi tsaye da gaske, ya yi duk mai yiwuwa, domin kawo ƙarshen wannan kashe-kashe na al’umma.
_______________













