• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Sakatare Ibrahim Dasuƙi Abubakar: Al’ummar Malumfashi Ta Samu Ƙaruwa

TAYA MURNA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 21, 2025
in Gizago
0
Sakatare Ibrahim Dasuƙi Abubakar: Al’ummar Malumfashi Ta Samu Ƙaruwa

Alhaji Ibrahim Dasuƙi Abubakar

77
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Sakatare Ibrahim Dasuƙi Abubakar: Al’ummar Malumfashi Ta Samu Ƙaruwa

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi

September 26, 2026
SUNANTA UMMU-KHULSUM

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026
Alhaji Ibrahim Dasuƙi Abubakar


                     _______________
A ranar Asabar da ta gabata (18-10-2025), sanarwa ta gabata daga mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, inda ya naɗa muhimman mutane takwas a matsayin Manyan Sakatarori (Permanent Secretaries). Cikin waɗannan mutane takwas, har da Alhaji Ibrahim Dasuƙi Abubakar (Ɗan Madawakin Galadiman Katsina).

Wane Ne Ibrahim Dasuƙi Abubakar?
Bayan da al’umma suka ji an ambata sunansa a matsayin Babban Sakatare, wasu sun taya shi murna da addu’ar Allah taya shi riko. Wasu kuwa, musamman waɗanda ba su san shi ba, tambayoyi suka yi ta jefawa: Shin shi ɗan wane gari ne? Daga wace ƙaramar hukuma yake?

A cikin masu tambayoyin nan, akwai masoya, waɗanda suna tambaya ne kawai domin neman sani, ba da wata mummunar manufa ba. Haka kuma akwai maƙiya kuma mahassada, waɗanda ba kawai tambaya suke ba, har ma suna ƙoƙarin kore shi daga ƙaramar hukumarsa.

Shi dai Malam Dasuƙi, cikakke kuma halaltaccen ɗan Ƙaramar Hukumar Malumfashi ne, a Jihar Katsina. Haka kuma, ta ɓangaren uwa da uba, shi jinin Sarautar Galadancin Katsina ne.

Ta ɓangaren uba, Ibrahim Dasuƙi Abubakar jikan-jika ne ga marigayi Galadiman Katsina Abu, wanda ya yi mulki a shekarar 1925. Wasu daga cikin ‘ya’yan da shi Galadiman ya haifa, sun haɗa da: 1-Kogo Abdullahi (mahaifin marigayi Galadima Mamman Nasir). 2-Alhaji Ibrahim Na-Yabiri, Madawakin Maigora kuma mahaifin shi Ibrahim Dasuƙi. 3-Alhaji Garba Ɗangoggo. 4-Alhaji Umaru Chajinas (ya zauna a Unguwar Galadanci Katsina). 5-Alhaji Alu Gizanda (mahaifin Dokta Halima Adamu). 6-Alhaji Abdulƙadir ‘Yammama, Danejin Katsina-I (mahaifin Danejin Katsina-II). 7-Alhaji Maishanu (mahaifin Sarkin Fadan Galadiman Katsina). 8-Alhaji Ahmed Nashehu (mahaifin Zayyana Ahmed, tsohon Kwamishina). 9-Alhaji Yusuf Audi (mahaifin Justice Abdullahi Yusuf).

Ta ɓangaren uwa kuwa, Ibrahim Dasuƙi jikan-jika ne ga marigayi Magajin Garin Malumfashi Aliyu. Cikin ‘ya’yansa, akwai Ruwan Sanyi Abdullahi da kuma Hajiya Karime.

Hajiya Karime, kakar Ibrahim Dasuƙi, ita ce ta haifi waɗannan ‘ya’yan: 1-Alu Gizanda. 2-Alhaji Abdulƙadir ‘Yammama. 3-Alhaji Maishanu. 4-Alhaji Sanin Gora (Magajin Gora). 5-Alhaji Tukur Ƙofar Gardi (mahaifin Anas Tukur). 6-Hajiya Indo (mahaifiyar Zailani Tijjani. 7-Alhaji Usman Mai-Nagari. 8-Hajiya Hassana. 9-Hajiya Hassana (mahaifiyar Ibrahim Dasuƙi Abubakar).

Mahaifin Sakatare Ibrahim Dasuƙi Abubakar, shi ne Alhaji Ibrahim Na-Yabiri kuma ga sunayen ‘ya’yansa maza da ya haifa: 1-Alhaji Lawal Nadadaye. 2-Alhaji Abdullahi Ibrahim (marigayi Madawakin Maigora kuma mahaifin KB-Lama). 3-Alhaji Usman Jariri. 4-Alhaji Abubakar Mai-Ɗanja (Member, State Assembly Commission). 5-Farfesa Adamu Ibrahim Malumfashi (Sashen Harsunan Najeriya, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya). 6-Alhaji Aliyu Ibrahim. 7-Alhaji Ibrahim Dasuƙi Abubakar. 8-Yusuf Ibrahim.

Wannan shi ne cikakken jadawalin iyayen Babban Sakatare Ibrahim Dasuƙi Abubakar ta ɓangaren uwa da uba. Shi cikakken ɗan Ƙaramar Hukumar Malumfashi ne. Duk mai shakka sai ya daina.

A yayin da ya samu wannan babban matsayi a Gwamnatin Jihar Katsina, muna taya shi murna, tare da addu’ar Allah ya taya shi riko. Allah ya sa aikinsa ya zama mai amfani ga al’ummar Malumfashi, Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya. Amin-Summa-Amin.
_______________

Previous Post

Matsalolin Arewa: Lallai Ne Mu Yi Karatun-Ta-Natsu

Next Post

RAYUWA

Related Posts

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi
Gizago

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi

September 26, 2026
SUNANTA UMMU-KHULSUM
Gizago

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026
HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1
Gizago

HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

September 12, 2026
Next Post
RAYUWA

RAYUWA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

July 9, 2023
WATER PROJECT IN MALUMFASHI: COMMUNITY URGED TO SUPPORT GOVERNMENT

WATER PROJECT IN MALUMFASHI: COMMUNITY URGED TO SUPPORT GOVERNMENT

June 16, 2025
Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afirka (PAWA) Ta Buƙaci Marubuta Su Koma Yin Rubutu A Harsunan Gida

Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afirka (PAWA) Ta Buƙaci Marubuta Su Koma Yin Rubutu A Harsunan Gida

March 21, 2024
Tarihin Rayuwar Sabon Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa Na Najeriya Rear Admiral Idi Abbas

Tarihin Rayuwar Sabon Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa Na Najeriya Rear Admiral Idi Abbas

October 28, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne
  • NASIHARMU TA YAU (18)
  • Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne

Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne

October 11, 2026
NASIHARMU TA YAU (18)

NASIHARMU TA YAU (18)

October 11, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.