Batutuwan Dubawa Game Da Kafa ’Yan Sandan Yanki
Daga Dokta Bukar Usman

••••
A ’yan kwanakin nan, an shiga batutuwa daban-daban dangane da samar da rundunar ’yan sanda a jihohin Najeriya, wanda haka ba zai rasa nasaba da hauhawar matsalolin tsaro da ke addabar al’umma ba. Ko a kwanan nan, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya sanar da cewa ƙungiyar tasu ta amince da kafa irin wannan runduna ta ‘yan sandan jihohi. A yau, Mujallar Taskar Gizago ta waiwaya baya, ta lalubo wata muƙala da DOKTA BUKAR USMAN, shahararren marubuci kuma masanin harkar tsaro ya taɓa rubutawa a kan batun, a shekarar 2012, lokacin shugabancin Goodluck Jonathan. Muhimmancin wannan muƙala ya sanya muka bijiro da ita a yau:
•••••
A da can shekarun baya, ’yan doka (’yan sandan yanki) ne suke kula da al’amuran tsaro a yankuna da sassan Najeriya. Wato a wancan lokacin, babu Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (NPF), kuma waɗannan jami’an ’yan doka suna gudanar da ayyukansu da inganci fiye da jami’an ’yan sandan ƙasa na yanzu, ta yadda zaman lafiya da kwanciyar hankali ke gudana a ko’ina.
An kafa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ne bayan da ƙasar nan ta koma Tsarin Mulkin Tarayya, ta yadda aka ɗauki jami’an ’yan sanda daga ko’ina na sassan Najeriya. Ga shi yanzu saboda al’amuran tsaro sun taɓarɓare, manya da ƙananan laifuka sai ta’azzara suke yi a ƙarƙashin wannan tsari na ’yan sandan ƙasa na tarayya. Ni a ganina, lokaci ya yi da ya kamata a koma wa tsarin baya, inda kowane yanki zai kafa rundunar ’yan sandansa, waɗanda za su kula da al’amuran tsaron yankunansu.
A lura, ni ina son a kafa rundunar ’yan sandan yankuna ne, ba ’yan sandan jiha ba, domin kuwa wasu za su ga cewa, idan aka ce ‘jiha’ ana ganin gwamnoni za su iya amfani da ƙarfin mulkinsu, su juya su zuwa amfanin kansu, maimakon al’umma. Idan kuwa aka kafa na yanki, ina ganin abin zai fi yin tasiri, domin kuwa jami’an da ke yanki, su suka fi sanin sirrin yankunansu; ta yadda za su iya magance kowace irin matsala da za ta taso ta fuskar tsaro, maimakon baƙi.
Ba zan taba mancewa ba, a shekarun 1950 zuwa 1960, lokacin ina makarantar firamare, na lura da yadda jami’an ’yan doka suke gudanar da aikinsu cikin ɗa’a da kishin ƙasa. Jami’an, suna aikinsu ne bisa ƙauna da kishin al’umma, ganin cewa yankinsu ne kuma al’ummarsu ce suke wa aiki. Haka kuma, jami’an za ka ga suna tsoma kansu cikin aiki wurjanjan, musamman ma idan wata masifa kamar gobara ta tashi. Za ka same su suna aikin kashe gobarar tare da sauran al’umma cikin nuna kishin al’umma a zukatansu.
Wani abin lura kuma shi ne, gudanar da rundunar ’yan sandan yanki tana da rahusa, musamman saboda babu buƙatar gina bariki, kasancewar kowane jami’i yana zaune a garinsu ne, cikin al’ummarsa. Wannan kuma zai ba shi damar sanin duk wani abu da ke faruwa a yankinsa, ta yadda da zarar an samu labarin wani mugun baƙo ko wani mai nufin tada hankali, cikin lokaci za a magance ƙudurinsa.
Babu shakka, kamar yadda zan iya tunawa, akwai zaman lafiya sosai a wancan zamanin, duk da cewa ana samun ƙananan ɓarayi nan da can, kamar kuma yadda a wasu lokutan ake samun ’yan fashi da makami, waɗanda cikin lokaci asirinsu ke tonuwa, ’yan doka ke daƙile hanzarinsu. A wancan lokacin, akawi wani gagararren ɗan fashi a yankinmu, mai suna Malam Gulani. Yakan yi fashi kamar irin yadda Robin Hood yake yi, amma daga bisani ’yan doka suka gano maɓuyarsa, suka kama shi, suka raba al’umma da ja’ibarsa.
Wannan ingantaccen aiki na kare lafiya da dukiyar al’umma ya faru ne a can shekarun baya, yadda ’yan doka suka riƙa aiki wurjanjan, suna daƙile ayyyukan maɓarnata cikin izza da jaruntaka. Haka suka riƙa aiki har zuwa shekarar 1972, inda aka ƙiriƙiri Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (NPF).
Sannu-sannu sai aka yi ta karkasa ta zuwa shiyyoyi, jihohi da kuma yankunan ƙananan hukumomi. Har zuwa yanzu, wannan tsari ne ke gudana, amma abin tambaya a nan shi ne, wannan tsari yana da tasiri ga al’umma kuwa?
A yau da tashe-tashen hankula da aikata laifuka suka zama ruwan dare a Najeriya, mutane na ta neman a duba yanayin aikin ’yan sanda a ƙasar nan. An ba da shawarar a kafa rundunonin ’yan sanda na jihohi. Bisa ga wannan koke, a kwanakin baya da Shugaban Ƙasa ya ziyarci Jihar Kwara, ya bayyana cewa Majalisar Zartarwa Ta Ƙasa ta nuna cewa a bar wannan batu har sai lokacin da kan al’umma ya ida wayewa, ta yadda tsarin zai yi tasiri. Kwanakin baya ma Gwamnan Jihar Yobe ya ce a taronsu na Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, gwamnoni biyu ne kaɗai suka amince da batun. Wannan kuwa abin mamaki ne da gwamnonin suka ƙi amincewa da wannan batu.
Ni kuwa a nawa ra’ayin, akwai buƙatar a sake duba yadda ake gudanar da al’amuran tsaro a ƙasar nan, musamman ma ta fuskar aikin ’yan sanda. Ga shi dai al’umma sai ƙaruwa take, don haka akwai wahala tsarin da ake gudanarwa na aikin ’yan sanda ya zama mai tasiri. Wannan tsari da ake ciki na ’yan sandan tarayya, yana haifar da rige-rigen samun muƙami ne kawai a tsakanin jami’an, sannan kuma ga tsadar gudanarwa. Don haka, kamata ya yi a kakkafa rundunonin ’yan sanda na yanki-yanki, kamar yadda yake a can baya.
Waɗanda ke ƙin wannan batu na ’yan sandan yanki, suna tsoron kada ’yan siyasa su riƙa amfani da jami’an ne wajen biyan buƙatunsu na siyasa, kamar kuma yadda shugabannin ’yan sanda na yanzu ke ganin za a rage musu martaba da girma ne idan tsarin ya canza zuwa na yankuna.
Ni kuwa ina ganin waɗannan ba su isa dalilai na ƙwarai ba, domin kuwa hatta yadda wasu ƙungiyoyi ke mallakar makamai a yankuna, suna tada hankali, idan wannan tsarin ake gudanarwa, za a iya maganinsu cikin sauri.
Lallai ne akwai tsananin buƙatar a jaraba wannan tsari na rundunar ’yan sandan yanki, musamman idan aka inganta tsarin yadda zai dace da wannan zamani da ake da wadatar na’urori. Mafi yawan matsalolin da ake fuskanta a furkar tsaro a wannan zamani sun dogara ne da cewa, mafi yawan jam’ian ’yan sanda baƙi ne a yankunan da suke aiki. Da a ce jami’an haifaffun yankunan da suke aiki ne, da za su iya gudanar da aikinsu cikin sauƙi da inganci, ganin cewa suna da masaniyar lunguna da saƙo-saƙon yankunansu. Idan aka kafa su, sai kuma a tanadar musu da ingantattun kayan aiki na zamani, wanda haka zai tallafa masu su gudanar da aikinsu cikin kwarewa da inganci.
Masu tsoron cewa wai ’yan siyasa na iya amfani da ’yan sandan yankin wajen cin ma manufofinsu, ai ko a wannan tsarin ma ana amfani da jami’an tsaro a siyasance. Domin kuwa ga EFCC nan ma, wacce ta Gwamnati Tarayya ce, amma a shekarun baya aka samu cewa ta haɗa baki da wasu ’yan majalisar jihohi, suka tsige gwamna! Babu abin da zai maganin irin wannan sai gaskiya da amana daga ɓangaren shugabanni. Don haka, lallai ne a maida hankali wajen kafa rundunonin ’yan sandan yanki, musamman a yanzu da ake batun sake fasalin tsarin mulki.
Ba tare da ɓata lokaci ba, lallai ne a tanadar da dokar da za ta ba jihohi ikon kafa rundunar ’yan sanda, tare da tanadar musu da sharuɗɗa da dokoki masu inganci, ta yadda duk wanda ya saɓa waɗannan ƙa’idoji wajen gudanarwa da tafiyar da rundunar, sai a janye izinin. Ke nan ita Gwamnatin Tarayya za ta zama mai kula da yadda ake tafiyar da rundunonin, ta yadda ba za a saɓa ƙa’idar tafiyar da su ba. Haka kuma, ya zamanto majalisun ƙasa za su iya amsar rahotannin yadda ake tafiyar da rundunonin daga lokaci zuwa lokaci, duk dai domin kada a samu saɓani ko karya tsarin.
Karin maganar nan da ke cewa wuƙar nesa ba ta iya taimako, gaskiya ne. Al’ummar yanki su suka san abin da ke faruwa a yankunansu, don haka ’yan sandan da aka ɗauka aiki a yankin, su za su fi aiwatar da aikinsu cikin inganci da biyan buƙata fiye da na nesa. Ga shi kuma tsarin zai kasance mai sauƙi da rahusar gudanarwa. Lallai ne a jaraba kafa wannan runduna ta ’yan sandan yanki a yanzu, domin a ceci al’ummar da wasu karkatattun miyagu ke cuta a kullum.
_____________
Dokta Bukar Usman, tsohon Babban Sakatare ne a Fadar Shugaban Ƙasa kuma masanin harkokin tsaro. Ya rubuta wannan muƙala ce a ranar 06-01-2012












