ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (1)
Daga Yahuza Malumfashi

Gabatarwa:
Da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (saw).
Bayan haka, na ƙuduri aniyar gabatar da tsokaci game da wannan al’amari mai take a sama, dangane da yunƙurin da na gani, na wasu bayin Allah da suka daddage wajen samar da wata ƙungiya ta “Hausawa Zalla.”
Babban dalilin da ya sa zan tofa albarkacin bakina kan wannan sha’anin, shi ne saboda wasu salelai da na ankara da su daga wasu daga cikin masu ƙumajin samar da ƙungiyar – salelan da na ankara da cewa sun yi bambarakwai, wai kiran Salla da usur.
A wannan muƙala, idan Allah ya yarda zan yi ƙoƙarin bijiro da tambayoyi da tsokaci, tare da sharhi, domin saita hanya. Tambayoyi kamar, shin Bahaushe zalla na da ‘yancin kafa ƙungiya a Najeriya? Shin a yau kuma a wannan zamani na ƙarni na 21, wane ne Bahaushe zalla kuma ta yaya za a tantance shi har ya cancanci shiga wannan mashahuriyar ƙungiya? Haka kuma, shin su wane ne shugabannin wannan ƙungiya kuma a ƙarƙashin tagomashin wa suke tafiyar da zarafofinsu, musamman ta ɓangaren kuɗaɗe da sauransu?
Saboda a samu sauƙin karantawa tare da bibiya cikin natsuwa da tsanani da fahimta, zan riƙa gutsura wannan muƙala ƙima-kima.
Da fatan za a jure biya tare da haƙuri da juriya.
__________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Tsakar Gizago (online)













