• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

TA’AZIYYAR PAPAROMA FRANCIS: SHIN INA LAIFIN PANTAMI?

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
April 22, 2025
in Addini
0
TA’AZIYYAR PAPAROMA FRANCIS: SHIN INA LAIFIN PANTAMI?

Shin Mene Ne Laifin Sheikh Pantami?

111
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TA’AZIYYAR PAPAROMA FRANCIS: SHIN INA LAIFIN PANTAMI?

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Shin ina laifin Pantami?

 

                             _____
Hankalina ya ɗauku ga wani al’amari da ya sanya ni tunani, cewa shin wai mu al’ummar Musulmin Arewa, me yake damun mu ne kuma shin anya kuwa muna cizawa tare da hurawa a yadda muke gudanar da mu’amalolinmu na addini?

Tsakanin jiya da yau, wasu mutane da suke ganin kansu a matsayin alƙalan Musulunci, masu raba wuta da aljanna ga mutane, suna ta kumfar baki a soshalmediya, musamman a TikTok da Facebook, suna ta kyara da kushe Sheikh Professor Isa Ali Pantami. Saboda me, wai laifinsa shi ne, ya nuna alhini da ta’aziyya ga al’ummar Kirista saboda rasuwar Paparoma Francis.

Kamar yadda suke cewa, babu dalilin da Sheikh Pantami zai yi haka, saboda wai shi Paparoma ba Musulmi ba ne, alhali shi Sheikh Musulmi ne kuma babban malamin Musulunci.

Ga masu irin wannan tunanin, ga wasu ‘yan tambayoyi: Shin Sheikh Pantami addu’ar neman gafara ya yi wa Paparoma ko kuwa kawai alhini ya nuna? Shin addinin Musulunci ya haramta mu’amalar rayuwa (ba addini ba) tsakanin Musulmi da Kirista? Shin addinin Musulunci ya buƙaci mu yi gaba tsakaninmu da Kirista? Shin Annabi Muhammadu (saw) bai yi rayuwa da Kiristoci da Yahudawa ba? Shin yaya ya mu’amalance su?

Idan mun duba sosai, Sheikh Pantami ya nuna kyakkyawar mu’amala ce ga abokan zaman mu na rayuwa – Kirista, ya taya su alhinin mutuwar shugabansu na addini na duniya. Haka kuma ya ce ya yi haka ne musamman saboda shi Paparoma Francis, kafin rasuwar shi, ya yi ta nuna alhini, yana ƙyamatar yadda ake zaluntar al’ummar Musulmin Gaza. Ba addu’ar neman gafarar Allah ya yi masa ba. (Akwai kalamansa a hoton nan).

A mu’amala tsakanin Musulmi da Kiristoci ko Yahudawa, Musulunci ya sahale mana mu yi zaman tare, sannan ya sanar da mu cewa mu kyautata masu mu’amala, mu yi masu adalci.

Baya ga haka, Allah Ya halatta mana Musulmi mu auri Kirista ko Bayahudiya, kuma mu yi zaman aure da su, duk kuwa da cewa suna cikin addininsu. Wannan ke nuna cewa, lallai ne akwai zamantakewa da kyautatawa da nuna tausayi da alhini ga juna a tsakaninmu.

Haka kuma, akwai tausayawa da jin ƙai a tsakanin Musulmi da Kirista. Idan mun duba tarihi, Manzon Allah ya taɓa amsar baƙuncin Kiristoci a Masallacinsa mai albarka kuma ya mu’amalance su da kyakkyawar mu’amala da kyautatawa. A farkon Musulunci, Kiristocin Ethiopia sun taimaka wa al’ummar Musulmi, inda suka amshi baƙin Manzon Allah da suka yi gudun hijira zuwa ƙasar. Sun ba su kariya daga azzaluman arnan Makka a zamanin Manzon Allah (saw).

Shin ina laifin Pantami a nan? Mu duba waɗannan hujjoji daga Alƙur’ani Mai Girma. A Suratul Al-Mumtahanah (60:8): Allah (swt) yana cewa: “Allah ba ya hana ku daga yin kyautatawa da adalci ga waɗanda ba su yi yaƙi da ku ba saboda addini, kuma ba su kore ku daga gidajenku ba. Lalle Allah yana son masu adalci.”

Haka kuma a cikin Suratul Baƙara (2:62), Allah yana cewa: “Lalle ne waɗanda suka yi imani, da Yahudawa, da Kiristoci, da Sabi’awa — duk wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, kuma ya aikata ayyukan alheri — to, suna da lada a wurin Ubangijinsu…”

Don haka, babu shakka, bisa waɗannan hujjoji, lallai akwai kyautata mu’amala tsakanin Musulmi da Kirista kuma Sheikh Pantami bai yi laifi ba don ya taya alhini ga Kiristoci bisa rasuwar limaminsu. Lallai ya kamata al’ummar Musulmin Arewa, mu taƙaita tsaurarawa a al’amarin Musulunci, musamman dangane da al’amarin da ya danganci mu’amalar rayuwa tsakaninmu da Kiristoci, abokan zaman mu.

ALLAH SA MU DACE DA DAIDAI, AMIN!
                               _____

Previous Post

ƊAN IYA MAI ALLAH

Next Post

GWAMNAN JIHAR NIGER YA ƘADDAMAR DA YAƘI DA TSAGERU DA ƁATAGARI

Related Posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
Addini

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba
Addini

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Mu Ji Tsoron Allah
Addini

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
Next Post
GWAMNAN JIHAR NIGER YA ƘADDAMAR DA YAƘI DA TSAGERU DA ƁATAGARI

GWAMNAN JIHAR NIGER YA ƘADDAMAR DA YAƘI DA TSAGERU DA ƁATAGARI

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

TSOKACINMU NA YAU (05)

TSOKACINMU NA YAU (05)

March 5, 2025
Natasha/Senate President Tango: My Take on Senator Dandutse

Natasha/Senate President Tango: My Take on Senator Dandutse

March 8, 2025
Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Tumbu-Madalla

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Tumbu-Madalla

July 21, 2023
A New Dawn for Agricultural and Technological Education in Malumfashi/Kafur

Sabuwar Kwalejin Ilimin Noma A Ƙafur/Malumfashi Za Ta Bunƙasa Ilimi a Jihar Katsina

June 19, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.