BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (3)
Bashir Yahuza Malumfashi
Arangama Ta Da Mai Kishin Addini A Masallaci:
Bayan na sauka a masaukina, na ajiye kayana kuma na yi sallama da abokina Malam Umar Mohammed Midala, sai na shiga bayi na yi alwala domin gabatar da sallolin Magariba da Isha’i. Kasancewar Otel ɗin Yamele babu masallaci kuma ba na son yin Salla a ɗaki sai na fito daga harabar Otel ɗin, domin a tsallaken hanya na ga wani ƙayataccen masallaci, matsakaici.
Koda na isa masallacin wajen ƙarfe 9:15 na dare, na iske ƙofofinsa a rufe ruf amma na ankara da cewa barandarsa kintsattsa ce, an daɓe ta da tayil sai ƙyalli take. Wani abin mamaki shi ne, ta fuskar Arewa na zo masallacin kuma garin sauri na kasa tantance kusurwar Gabas. Cikin rashin sani, sai kawai na ajiye wayata a gabana, na yi iƙama, na tayar da Salla, abina.
Na yi raka’ar farko ke nan, na miƙe domin kawo ta biyu, sai na ji tattaki a bayana. A zato na, wani masabuƙi ne irina, wanda ya rasa Salla a jam’i yake son ya bi ni, don haka sai na gyara ƙafata ta dama, domin in ba shi tazara ya haɗa sahu da ni. Maimakon mutumin nan ya haɗa sahu, sai dai kawai ji na yi ya kama kafaɗuna, yana ƙoƙarin juya ni zuwa wata kusurwa ta daban.
A daidai wannan lokaci, a matsayina na baƙo, abubuwa biyu suka zo mani a zuciya. Na farko dai na tuna cewa a Jihar Borno nake, inda batun ‘yan ƙungiyar Boko Haram ke yankan ƙauna, duk da cewa a lokacin nan al’amura sun daidaitu, zaman lafiya ya kankama. Kan haka sai na yi zaton cutar da ni zai yi, kasancewar ni kaɗai ne a barandar masallacin, duk kuwa da cewa akwai hasken lantarki ƙwanyar kuma ga shi a bakin baban titi ne (hanyar Damaturu).
Abu na biyu da ya ƙara zuwa mani a tunani, shi ne ko mutumin nan babbar wayata da na aje a gabana yake son ɗaukewa. Na yi wannan tunanin ne saboda na tuno abin da ke faruwa a birnin Kano, inda matasa, musamman masu shaye-shaye suka fito da yayin ƙwacen wayoyin mutane, ta hanyar amfani da ƙarfi da makami. Shi ne sai tunani ya bijiro mani, ko a Biu ma akwai masu ƙwacen waya.
Jin yadda mutumin nan ya kama kafaɗuna yana ƙoƙarin juya ni, sai na yanke Salla gaba ɗaya. Na duƙa ƙasa, na kai wa wayata rida. A lokaci ɗaya kuma na tuno da tsimin atisayen Judo da Kareti. Nan da nan na banƙara gwiwar hannuna, ina nufin dukan bakinsa da ita. Cikin tsawa, na ce masa “kai lafiya?”
Inda na gane cewa mutumin nan ba da nufin mugunta ya zo ba, shi ne yadda na ji ya bushe da dariya tare da kauce fuskarsa daga gwiwar hannuna da na so doka masa. Cikin sauri ya ce mani: “Yi haƙuri, Kudu kake kallo ba Gabas ba, shi ya sa nake son in juya ka zuwa alƙibla sosai.” Jin haka sai na saki jikina, hankalina ya kwanta. Na ce masa, “madalla, na gode.” Na saka wayata cikin aljihun wando. Na juya kusurwar Gabas, na sake tada sabuwar iƙama, na gabatar da sallolina.
Mutanen Biu Suna Da Kishin Addini:
A ziyara ta ta kwanaki bakwai a garin Biu da kuma mu’amala da na yi da al’ummar Babur/Bura da maƙwabtansu, na fahimta da cewa su mutane ne masu kishin addini. Misali, tun kafin ma in je Biu, mafi yawan waɗanda na gamu da su a wajen aiki ko wata hulɗa, nakan same su masu daraja addininsu da kuma martaba addinin abokan zaman su.
Misali, kamar Zainab Musa da A’isha Umar Yusuf da Musa Salihu da Malam Gambo Isa (mutumin Miringa), waɗanda mu’amalar aiki ta haɗa mu a kamfanin jaridar Daily Trust da na Public Agenda, dukkansu Musulmi ne masu ibada da mutunta abokan zama, mabiya addinin ko


Kirista. Haka ma Dokta Bukar Usman, dukkan mu’amalarsa, za ka ga yadda yake daraja abokansa waɗanda ba Musulmi ba, kamar kuma yadda ba za ka taɓa jin shi yana aikata wani abu da ya saɓa wa Musulunci ba. Haka shi ma Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai (mai ritaya), na kula da mu’amalarsa, kamar kuma yadda na karanta tarihinsa, mutum ne mai kiyaye addinin Musulunci, kamar kuma yadda yake daraja sauran mabiya wasu addinai.
Wani abu da ya ƙara burge ni da mutanen Biu shi ne, yadda suke kimtsa masallatai. A ziyara ta a garin Biu da kewaye, dukkan masallatan da na gani, manya da ƙanana, za ka same su da tsafta kuma da tsari. Hatta almajirai da nake gani cikin ƙazanta a biranen yankunan Arewa, a Biu da wuya ka samu almajirai cikin ƙazanta ko kuma ka ga suna ƙwazzabar yawace-yawace.
Suna da jituwa da son zaman lafiya ta fuskar addini. A Biu za ka iya samun gidan iyali guda, amma suna bin addinai daban-daban. Misali, wasu Musulmi, wasu kuma Kirista, amma duk da haka suna zaune lafiya da fahimtar juna da zumunci. Akwai wani mutumin Kano da ke zaune a Biu, mai suna Malam Jafaru Babban Yaya, wanda na haɗu da shi a wurin wani mai shayi, a gefen hanyar Damaturu. Ya ce mani ya shafe sama da shekara 25 a Biu kuma yana cikin ‘yan banga dake kare unguwarsu.
Da yake shaida mani irin zaman amana da zumunci da ke tsakanin mabiya addinan Musulunci da Kiristanci a Biu, ya ce: “A nan, duk tsawon zama na, ban taɓa ganin rashin jituwa ko hatsaniya tsakanin mabiya addinin Kirista da na Musulunci ba. Wasu ma za ka tarar ‘yan uwan juna ne na jini amma sai dai zumunci da fahimtar juna.
“Zan iya kawo maka misalin yadda Musulmi da Kirista ke da kyakkyawar zamantakewa a Biu. Misali, a shekarun baya da matsalar ‘yan Boko Haram ta ta’azzara a Biu da kewaye, haɗa hannu muke yi mu kare rayuka da dukiyoyin juna. Duk ranar Juma’a, ‘yan banga Kirista ne suke zuwa su taya mu tsaro har a kammala Salla. Haka kuma mu ma a duk kowace Lahadi, haka muke zuwa mu kare coci, har sai sun kammala ibadarsu,” In ji Malam Jafaru, wanda kuma ya shaida mani cewa akwai ranar da faston cocin unguwarsu ya yi masa kyautar kudi saboda jin daɗin yadda su ‘yan banga Musulmi suke kula da mabiya addinin Kirista.
Tsafta Da Tsarin Garin Biu:
Biu, gari ne da ake yi wa kirari da “Birni A Kan Tsauni.” Kuma hakan gaskiya ne, domin duk inda mutum ya ɓullo wa garin, daga Gabas ko Yamma, Arewa ko Kudu, tun daga nesa zai riƙa hango gidaje da gine-gine. Gari ne wanda ya dace da tsari mai inganci, inda aka tsara komai bisa mazaunin da ya dace. An fitar da manyan hanyoyi masu faɗi, wasu an daɓe da kwalta, wasu kuwa ƙanana da ke lungunan unguwanni, babu kwalta amma a kintse suke. Haka ma an fitar da magudanan ruwa kuma a share suke cikin tsafta. Da wuya ka ga magudanar ruwa tana fitar da kwatami mai wari, kamar yadda ake samu a wasu birane. Mutane a Biu suna kula da magudanan ruwa, ba su cika su da shara da tarkacen bola.
Wani abu muhimmi da ya ɗauki hankalina a garin Biu, shi ne yadda suke da wadatar wutar lantarki. Tun da na je garin na lura da cewa ba a ɗauke masu wuta, dare da rana. Koda an ɗauke, to akwai dalili kuma ba a jimawa, sai ka ga an dawo da ita. Na tambayi Malam Midala cewa, “shin ko don ana gagarumin bikin naɗin sarautar manyan mutane, shi ya sa ba a ɗauke wuta?” Ya ce mani ko alama, haka al’amarin yake a kowane lokaci, rani da damina.
_______
Wannan shi ne kashi na uku na rohoton ziyara ta garin Biu. A kashi na 4 na rahoton nan, zan maida hankali wajen muhimman wuraren tarihi da na ziyarta da muhimman al’adun gargajiya da sarauta na al’ummar Babur/Bura. Haka kuma zan kawo tsari da halayen mutanen Biu, musamman abin da ya shafi neman ilimi, sana’a, noma da kiwo da kuma tsarin kaɗe-kaɗe da raye-rayensu na gargajiya.












