• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, May 2, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

SATAR AZZAKARI: Gaskiya Ko Ruɗanin Tunani?

Musa A. Bello by Musa A. Bello
October 16, 2023
in Gizago
0
SATAR AZZAKARI: Gaskiya Ko Ruɗanin Tunani?

Ruɗanin Tunani...

139
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

SATAR AZZAKARI: Gaskiya Ko Ruɗanin Tunani?

Daga Musa A. Bello

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

~~~~~~~
Mutane da yawa ba su san TUNANI na da alaƙa da WARKEWA a yayin rashin lafiya ba. Yadda mutum ya sa a ransa yana tasiri wajen aiki.

Shi ya sa ko ruwa ka ɗiba ka ba wani, ka ce masa wani magani ne na musamman da zai taimaka masa wajen warkewa daga wata matsala, sannan ka tabbatar masa da cewa wasu ma sun yi amfani da shi sun dace. To fa in ya sha, sai ya ji alamun fa haka ne, maganin na aiki.

Wannan shi ke tabbatar da irin tasiri da ƙarfin da TUNANI ke da shi ke nan.

Hakazalika, SHA’AWA (Sexual Arousal) ta kwanciyar aure, tana da alaƙa da TUNANIN ZUCIYA (Mind). Shi ya sa namiji ko tunanin matarsa ya yi a wani yanayi, sai ya ji al’aurarsa ta amsa, duk da cewa ba ya ganin ta a lokacin.

Ita matsalar da ɗa namiji zai ji ba ya jin al’aurarsa, ita ake kira da “KORO SYNDROME.” Matsala ce da take da alaƙa da ƙwaƙwalwa ko tunani. Mutum zai ji kamar azzakarinsa na zuƙewa cikin jikinsa ne, wanda hakan zai tada masa hankali.

A ɓangaren mata kuma, za ta ji kamar kan mamanta ko leɓen al’aurarta yana noƙewa ciki.

Duniyar ilimi ta tabbatar da cewa wannan al’amari, matsala ce ta Ƙwaƙwalwa ko Tunani (Psychiatry Disorder), wanda yake samo asali daga mabanbantan dalilai kamar haka:

✓ Yawan tunani a kan girman azzakarin mutum.

Zan iya cewa mutanen da suke yawan yi mani tambaya a kan yadda za su ƙara girman azzakarinsu, sun fi masu tambaya a kan yaya za su yi ƙiba. Hakan ya nuna mutane da yawa sun damu da tunanin ƙara girman azzakari, wanda duniyar ilimi ta tabbatar da babu abin da zai ƙara maka girmansa, in ba aiki na musamman ba (surgery).

Azzakari na iya girma iya ƙarshen girmansa yayin sha’awa amma ba zai wuce ainihin girmansa na asalin halitta ba.

Saboda mutane sun sa wa kansu tunanin ƙanƙancewar gaba, shi ya sa kullum masu maganin gargajiya suke ciniki sosai. In ka gaya wa mutum cewa ba wata matsala game da girman azzakarinsa, sai ya ga kamar kana yi masa baƙin cikin samun ƙatoton kayan aiki ne, duk da cewa shi girman azzakari ba shi da alaƙa da farin cikin da mutum zai ji ko ya bayar.

✓ Yarda Da Cewa An Masa Sihiri.

Mutum na fara tunanin cewa wanda fa ya goge shi yanzun nan, ɗan shafi mulera ne. Nan fa ƙwaƙwalwarsa za ta fara raya masa cewa azzakarinsa fa ya ɓace, wanda a zahiri ba haka ba ne.

✓Yawan Istimna’i.

Wannan shi ne mutum ya riƙa wasa da azzakarinsa da kansa, wanda ake kira *Masturbation.” Wannan shi ma yana haifar da irin wannan tunanin.

✓ Tunanin Cewa Dole Azzakari Sai Ya Kai Inci Sha Biyar.

Kamar yadda ake faɗa a wasu littattafan soyayya na ƙarya (novel), wannan yaudarar kai ce. Duniyar ilimi ta tabbatar da cewa mafi yawancin mutane, azzakarinsu bai wuce inci 5 ko 6. Masu inci 15 a duniya tsiraru ne.

Yayin da mutum ke yawan tunani kan haka, zai raina azzakarinsa, wanda hakan na iya haifar da “Koro Syndrome.”

Wallahi ƘARYA ne, ba wanda ya isa ya sace maka AZZAKARI. Sai dai in wuƙa ya sa ya yanke.

Wasu na nuna bidiyo na wasu da suka ce sun sace wa wani azzakari amma ko a bidiyon za ka gane tabbas KORO SYNDROME ne ya kama wanda aka ce an sace ma wa.

~~~~~~~
Pherm. Musa A. Bello, masani ne kuma ƙwararre a ilimin haɗa magunguna na zamani.
~~~~~~~

Previous Post

KHALID IMAM: Tattaunawa Da Marubuci Mai Hannu Da Yawa

Next Post

FAƊA DA ‘YAN TA’ADDA: Malam Dikko Kada Ka Shiga Daji – Abdullahi Mahuta

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
FAƊA DA ‘YAN TA’ADDA: Malam Dikko Kada Ka Shiga Daji – Abdullahi Mahuta

FAƊA DA 'YAN TA'ADDA: Malam Dikko Kada Ka Shiga Daji - Abdullahi Mahuta

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

UNDP Partners Kaduna Ministry to Build Peace in the State

UNDP Partners Kaduna Ministry to Build Peace in the State

September 20, 2023
Janar Faruk Yahaya Ya Zama Zaruman Sakkwato

Janar Faruk Yahaya Ya Zama Zaruman Sakkwato

August 15, 2023
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (3)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (3)

May 12, 2025
JONATHAN – KWANKWASO: Sabon Lissafin 2027

JONATHAN – KWANKWASO: Sabon Lissafin 2027

August 15, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)
  • General Buratai (A Poem)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

April 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.