TAURARON GIZAGAWA: NURA ADAMU AHMED

A wannan lokaci, wanda ya samu nasarar ɗarewa a kujerar Taurarin Gizagawa, shi ne Alhaji Nura Adamu Ahmad, Bunun Sharaɗa. Mai Lambar Gizago GZG-032-KNO.
Wane Ne Nura Adamu Ahmed?
An haifi Nura Adamu a garin Kano, kuma ya yi karatunsa tun daga matakin firamare har zuwa jami’a, kuma a yanzu haka yna karatun Digiri Na Biyu (Masters) a Jami’ar National Open University of Nigeria Kano Study Centre. Yana aiki a Ma’aikatar Kula Da Ilmin Bai Ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB). Yana a matakin Deputy Director. Bayan haka kuma, yana riƙe da sarautar gargajiya a matsayin BUNUN SHARAƊA.Yana da mace ɗaya da ‘ya’ya 4. Mutum ne shi mai son tafiye-tafiye, karatu da kallon wasannin ƙwallon ƙafa kafa.
Muƙaminsa A Gizago:
Shi ne tsohon Shugaban Gizago na Jihar Kano har karo biyu, tsohon Shugaban Riƙo na Ƙasa.
A yanzu haka kuma mamba ne a cikin Kwamitin Amintattu.
Ma’anar Zumunci:
A fahimtar Nura, zumunci wata al’ada ce mai girma a tsakanin mutane wadda kan ƙara haɗa hulɗar dangantaka da yarda da juna. Zumunci kan ƙara ilimi a tsakanin masu sada shi kuma zumunci abu ne da addinanmu suka umarce mu da mu sada shi saboda falalarsa.
Fahimtarsa Da Ƙungiyar Gizago:
Faɗakarwa, nishaɗantarwa da kuma sada zumunci na daga cikin jigon kafa ƙungiyar Gizago.
Shawara Ga Gizagawa:
1-Mu kasance masu mutunta juna.
2-Mu kasance masu neman na kanmu.
3-Mu kasancewa masu karimci da girmamawa a cikin jama’a.
4-Mu ƙarfafa zumunci a tsakanin mu ta hanyar kai ziyara ta taimakon juna.
5-Mu kasance masu juriya da fuskantar rayuwar yau da kullum.














Tabbas Alhaji Muntaka Abdul-Hadi Dabo ya yi ƙoƙari sosai don shi ne ya tabbatar da haduwar fuskokinmu bayan haduwa da muka yi a Jaridu da kiran waya.
Allah Ya ƙarawa rayuwa albarka, mutum ne mai karamci da Zumunci.
Madalla da wannan tsokaci. Allah kara hada kan Gizagawa, Ya tabbatar da alherin zumunci. Amin Amin. Mun gode.