• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Barkwanci

Barkwancin Ƙarshen Mako

Ku Zo Mu Ƙyaƙyata

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 22, 2023
in Barkwanci
6
Kishin Ƙasa Ne Tubalin Farko Na Gina Rayuwar Al’umma (2)

© Bashir Yahuza Malumfashi

76
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Barkwancin Ƙarshen Mako

~~~~~~~
Jama’a, barkan mu da hutun ƙarshen mako. Ku zo mu ƙyakyata da waɗannan labarun daga Bashir Yahuza Malumfashi, a Jaridar Taskar Gizago:
~~~~~~~

Related posts

Barkwancin Ƙarshen Mako

Barkwancin Ƙarshen Mako

July 30, 2023
Barkwancin Ƙarshen Mako

Barkwancin Ƙarshen Mako

June 25, 2023

(1) Mun Yi Magana

Wani Badakkare ne ya je yawon neman karnuka a Arewacin Sakkwato. Ya kuwa dace ya samo, a kan hanyarsa ta komawa gida Zuru sai ya bi ta wani garin Zamfarawa. Shi ne gardama ta shiga tsakaninsa da wani Bazamfare. Shi Badakkaren yake ce wa Bazamfare: ”Kai ko a Sakkwato da aka yi magana mun yi magana bare nan umu-umu.” Bazamfare ya ce: “Can Sakkwato me aka ce maka? Kai kuma me ka ce?” Badakkare ya ce: “Cewa aka yi ‘ku tafi daga nan!’ Mu kuma muka ce, mun tafi!”

~~~~~~~

(2) Kinayar Bahaɗeje

Wani Bahaɗeje ne talauci ya kama shi, ya rasa abin da zai yi ya samu kuɗi, sai dubara ta zo masa. Sai da ya bari an biya ma’aikatan gwamnati albashi a Haɗeja, sai ya tafi banki, ya samu wurin na’urar ATM an cika makil ana ta hada-hadar cirar kuɗi. Bahaɗeje kawai sai ya farashe ƙasa, ya yi kamar ya suma, kumfa na fita daga bakinsa. Nan fa mutane suka yo kansa domin taimakonsa, cikinsu sai wani ya riƙa cewa: “Ku samo ruwa a zuba masa domin ya farfaɗo!” Jin za a kwara masa ruwa sai Bahaɗeje ya maƙe murya ya ce: “Ku ƙyale wancan wawan mai batun samo ruwa, idan da agajin ruwa nake so ai bakin Gidan Ruwa zan suma. Ba ku lura da wurin da na suma (banki) ba? Ku agaza da abin da ya dace kawai amma ba da ruwa ba!”

~~~~~~~

(3) Hali Zanen Dutse

Wani ɗan sanda ne yana duba littattafan makarantar ’ya’yansa domin ganin irin ƙoƙarinsu ko akasi, sai ya fara da babban ɗansa. Saboda ɓacin rai sai da ya yi wa yaron bulala 30. Da ya zo kan littafin ƙaramin sai suka ga ya kalli littafin ya fita kawai daga ɗakin. Bayan ya fita sai babban yake tambayar ƙaramin cewa: “Yaya na ga Baba bai doke ka ba, bayan na san kai ma ba ka yi ƙoƙari ba?” Sai ya ce: “Ai Naira ɗari biyu na saka masa a tsakiyar littafin, shi ya sa ya kyale ni.”
~~~~~~~

Previous Post

NASIHA: Waƙen Ƙarfafa Gwiwa

Next Post

Da Albarkar Littafi Na Je Saudiyya – Sa’adatu Kankia

Related Posts

Barkwancin Ƙarshen Mako
Barkwanci

Barkwancin Ƙarshen Mako

July 30, 2023
Barkwancin Ƙarshen Mako
Barkwanci

Barkwancin Ƙarshen Mako

June 25, 2023
Kar Nake Ganin Ka
Barkwanci

Kar Nake Ganin Ka

May 29, 2023
Next Post
Da Albarkar Littafi Na Je Saudiyya – Sa’adatu Kankia

Da Albarkar Littafi Na Je Saudiyya - Sa'adatu Kankia

Comments 6

  1. Isyaku Idi says:
    3 years ago

    A gidan ma sai da ya ɗana 😃😃😃

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Hahahhahahahahaaha!

      Reply
  2. Abubakar Yarima says:
    3 years ago

    Wani Bafulatani ne ya shigo gari, kai tsaye sai ya wuce teburin mai shayi, yace a kulla masa ruwan-bunu a Leda. Ana bashi sai ya wuce shagon probishan yace a bashi abin nan na Leda, da kan shi ya nuna…..mai shago kuwa ya bashi…
    Gogan naka ya samu gindin bishiya ya zazzage sachet din nan ya din ga kumbuda baki na kumfa…..Ashe Omon Clean ne!!

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Hahahhahhaha! Gaskiya Ɗanfulani ya sha daɗi!

      Reply
  3. Guna niyoss pkm says:
    10 months ago

    allah me iko yau sebayan shekara 2 da lbr nikuma zanyi comment

    malumfashi gsky barawo yafada duk inda kadau uwa aidole yayanta subita inabayanka barawo

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      10 months ago

      Haka ne, ai komai sai Allah ya yi. Ga shi mu ma har yanzu ba mu saka sabon labari ba. Amma ina sha Allahu za mu dawo da zafafan labarai. Mun gode.

      Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

December 5, 2025
Kaduna State Pilgrims are to Deposit ₦2.5 Million

Kaduna State Pilgrims are to Deposit ₦2.5 Million

October 6, 2023
TSOKACINMU NA YAU (08)

TSOKACINMU NA YAU (08)

March 8, 2025
SADAUKARWA: Tinubu Tsaye Yake Ga Manufofin Najeriya Da Afirka – Minista Idris

SADAUKARWA: Tinubu Tsaye Yake Ga Manufofin Najeriya Da Afirka – Minista Idris

October 22, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?
  • Mu Ji Tsoron Allah
  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.