• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, September 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

An Samu Sauƙin Matsalar Tsaro: Yanzu Dukkan Kasuwanninmu Suna Ci

- GWAMNA RADDA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 12, 2026
in Labarai
0
An Samu Sauƙin Matsalar Tsaro: Yanzu Dukkan Kasuwanninmu Suna Ci

Dikkon Katsinawa (07)

13
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

An Samu Sauƙin Matsalar Tsaro: Yanzu Dukkan Kasuwanninmu Suna Ci – Gwamna Radda

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cewa a halin yanzu babu wata kasuwa da aka rufe a faɗin ƙananan hukumomi 34 na jihar, yana mai cewa dukkanin kasuwanni suna buɗe tare da ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci da sauran ayyukan tattalin arziƙi.

Related posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ’yan kasuwa da shugabannin ‘yan kasuwa daga ƙananan hukumomin jihar 34, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Jihar Katsina, Alhaji Aminu Isyaku.

A cewar Gwamna Raɗɗa, wannan ci gaba na da nasaba da ingantuwar yanayin tsaro da aka samu a jihar, wanda ya ba ’yan kasuwa damar komawa kasuwanninsu tare da gudanar da harkokinsu cikin yanayi mai kyau, idan aka kwatanta da shekarun baya.

Ya ce, duk da cewa har yanzu akwai sauran ƙalubalen tsaro da ake fuskanta, an samu gagarumin sauyi idan aka kwatanta da baya, lokacin da matsalar tsaro ta tilasta rufe sama da kasuwanni takwas a hukumance a wasu sassan jihar.

‘Yan kasuwa a Jihar Katsina, yayin ganawa da Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa a gidan Gwamnati

Gwamnan ya jaddada cewa kasuwanni na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziƙin jihar, samar da guraben ayyukan yi, ƙara yawan kuɗaɗen shiga da kuma inganta rayuwar jama’a. Saboda haka, ya buƙaci shugabannin kasuwanni da ’yan kasuwa su ci gaba da ba gwamnati haɗin kai wajen tabbatar da dorewar wannan yanayi.

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Jihar Katsina, Alhaji Aminu Isyaku, ya bayyana cewa haɗin gwiwar da hukumar ke yi da ƙungiyoyin ’yan kasuwa, ya taimaka matuƙa wajen inganta tsarin karɓar haraji, musamman daga ɓangaren tattalin arziƙin da ba na hukuma ba.

Ya ce wannan haɗin kai ya taimaka wa gwamnatin jihar wajen cin ma wasu daga cikin manufofinta na tara kuɗaɗen shiga cikin gida a cikin shekaru uku da suka gabata, tare da samar da kyakkyawar fahimta tsakanin gwamnati da ’yan kasuwa.

Shugabannin kasuwannin daga ƙananan hukumomi 34 na jihar, sun yaba wa Gwamna Radda bisa abin da suka bayyana a matsayin kyakkyawan jagoranci da ƙoƙarin da yake yi wajen samar da yanayi mai kyau ga harkokin kasuwanci. Sun kuma yi alkawarin ci gaba da ba gwamnati haɗin kai wajen inganta tsarin tara kuɗaɗen shiga da bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

Sun kuma yaba da ayyukan raya kasuwanni da gwamnatin jihar ta aiwatar, musamman gina sabbin kasuwanni na zamani a Mashi, Daura da Charanci da kuma sauran wuraren da gwamnati ke shirin fara irin waɗannan ayyuka.

Da yake mayar da martani, Gwamna Raɗɗa ya gode wa shugabannin kasuwannin bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban tattalin arziƙin Katsina, tare da jaddada cewa haɗin kan gwamnati da ’yan kasuwa na da matuƙar muhimmanci wajen samar da tattalin arziƙi mai ɗorewa.

Ya kuma buƙaci shugabannin kasuwanni da su tabbatar da bin ƙa’idojin kasuwanci, taimakawa wajen inganta tsaro da kuma ci gaba da tallafa wa manufofin gwamnati da nufin samar da kyakkyawan yanayi ga harkokin kasuwanci a faɗin jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da mayar da hankali wajen inganta tsaro da abubuwan more rayuwa a kasuwanni, domin ƙara ƙarfafa harkokin kasuwanci da samar da yanayi da zai ba ’yan kasuwa da masu zuba jari damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
__________

Previous Post

Al’amuran Tsaro: Musulmin Duniya Sun Taru A Abuja

Next Post

No, There Is No Global Shortage of Men: Fact-Checking the Viral #UN Claim

Related Posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)
Labarai

Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)

August 31, 2026
Next Post
No, There Is No Global Shortage of Men: Fact-Checking the Viral #UN Claim

No, There Is No Global Shortage of Men: Fact-Checking the Viral #UN Claim

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Ana Tuhumar Malamin Musulunci Bisa Auren Mata 75

Ana Tuhumar Malamin Musulunci Bisa Auren Mata 75

June 24, 2023
RAMADAN KARIM: 30-1447

RAMADAN KARIM: 30-1447

March 19, 2026
KIRA NA MUSAMMAN GA JAMI’AN TSARO A MALUMFASHI

KIRA NA MUSAMMAN GA JAMI’AN TSARO A MALUMFASHI

August 3, 2024
Israel/Palestine Conflict: TY Buratai Foundation Calls for Permanent Ceasefire

Israel/Palestine Conflict: TY Buratai Foundation Calls for Permanent Ceasefire

November 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
  • Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
  • SANATA BELLO MANDIYA: Mun Yi Babban Rashi – Gwamnan Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.