• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, August 14, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Nasiru Adamu El-Hikaya by Nasiru Adamu El-Hikaya
April 20, 2026
in Gizago
0
Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Martani ga Shugaban Hausawan Bogi

21
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Daga Nasiru Adamu El-hikaya

Related posts

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

August 13, 2026

Tsakanin Rarara Da Pantami: Yayin Da Maroƙi Ya Zaci Shi Wani Ƙusa Ne…

August 2, 2026
Martani ga Shugaban Hausawan Bogi

 

__________

Shugaban gungun ‘yan ƙaryar Hausa Zalla dai ya jijjiga Alkur’ani amma sam bai rantse da Alkur’ani ba. Kazalika, sam ba shi da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da aya ta 61 ta Al-Imran da ya karanta ba tajwidi, ba ta’awuzi, ba tahamidi. Shin akwai Musulmi da ke ɗaga Alkur’ani da hannun hagu? Wannan sai madugun gungun ‘Yan Bazata!

Na ga wasu sun ja hankalina da duba rantsuwa da shugaban gungun ƙaryar Hausa Zalla ya yi, wai da Alƙur’ani don ba da kariya ga haramtacciyar turba da ya ɗauka ta kwangilar yaƙi da Musulunci, Hausawa da Arewa. Akwai wani sullutun yaro da ya ƙalubalance ni da wai ni ma na yi irin wannan rantsuwa kan tabbatar da kwangilar nan. Ba ni da lokacin martani ga yara marar sa kunya.

Ga abubuwa 7 da zan yi sharhi ko tsokaci a kai kan faifan bidiyon:

1-Babu inda shugaban gungun nan ya ce ya rantse da Alƙur’ani, ko a gargajiyance, don irin wannan rantsuwar ma ba ta samo asali daga tushe ba. Ya ce Alƙur’ani ya ci shi in kwangila ya karɓo, kazalika in ba ya shirga karya. Misali ya rantse cewa Alƙur’ani ya ci shi in ƙarya ya tabka a kaina cewa an kore ni daga aiki a VOA. Wallahi in ya yi haka zai yaba wa aya zaƙi.

2-Mun ga ya yi ta jijjiga Alƙur’ani kamar littafin Iliya Ɗan Mai Karfi, ba girmamawa ko ta misƙala zarratin, don da alamu ba ma layinsa ba ne, basaja ce kawai.

3-Maimakon ya tsaya kan batun kwangila sai ya shiga babin wai ana kore samuwar Hausawa ko ana kashe Hausawa da sauran bayanan da ba su da alaƙa da rantsuwa ma, balle har ya kai ga neman wulaƙanta Alƙur’ani; ta hanyar jijjiga shi da buɗe shafukan war-war-war, tamkar fallen yadin shaddar wa-gambari.

4-Ita wannan aya ta 61 ta Suratu Al-Imran, tana magana ne kan Kiristocin Najran, waɗanda suka ƙaryata matsayin Annabi Isa (as) na mutum kuma Annabin Allah, kamar yadda ya zo a Alƙur’ani. A wajensu Isa (alaihis salam), ɗan Allah ne. Sun ƙalubalanci wahayin da aka yi wa Manzon Allah (saw), kan kasancewar Annabi Isa manzo ne na Allah amma sam ba ɗan Allah ba ne. A nan Allah ya umurci yin mubahala da waɗannan Kiristoci, cewa Musulmi su fito da ‘ya’yansu, matansu da ma kawunansu, haka nan su ma Kiristoci su yi irin wannan fita, sai a yi addu’ar la’ana mai zafi ta neman Allah ya tsine wa duk mai ƙarya.

To, shi shugaban wannan gungun Kiristoci ‘yan ƙungiyarsa zai kira a yi wannan la’ana, ko yana da membobi Musulmi ne? Shin mubahalar tsakanin Musulmi da Musulmi za a yi ko tsakanin Musulmi da Kirista? Ina membobin ƙungiyarsa masu rufaffun shafuka da sunayen ƙarya, masu wuni suna la’antar Shehu Mujaddadi da malaman Musulunci a soshalmidiya? Shin za su bayyana a yi mubahalar da su, ko su sojojinsa na ɓoye don aikin aibanta mutanen kirki?

5-Shugaban gungu ya ce kar a damu da tajwidinsa lokacin karanta ayar. Shin wa ya tambaye shi batun tajwidi ma a nan? Shi ya yi karatunsa kuma ya tsargu da karatun, don bai iya ba. Ba ma tajwidi ne damuwar ba, a’a, kafa hujja da ayar wajen jijjiga Alƙur’ani da ya yi ba tare da sanin dalilin saukar ayar ba da muhallin da take aiki.

6-Me ya sa shugaban gungu bai rantse cewa Alƙur’ani ya ci shi in shi ba Bahaushe ba ne? Duk nazari na nuna wannan mutumin ba Bahaushe ba ne, daga yadda tarbiyyar maganarsa take da furucin harshensa. Muna son ya fito ƙarara ya yi bayanin nasabarsa da yadda ya zama Bahaushe da a taƙaice irin gudunmawar da ya ba wa harshen Hausa waje da ƙabilanci a rayuwarsa kakaf.

7-Shin me ya sa yana ganin ‘yan gungunsa suna cin zarafin mutane da jifar su da zama ‘yan zina da ƙazafi iri-iri amma bai taɓa tsawatawa ba? Me ya sa bayan muhawararsa da Farfesa Abubakar Usman Ribah, ya bar yaransa suna zayyana Farfesa da na kwali da miyagun kalmomi amma bai taɓa tsawatawa ba? Wa zai ɓata lokacinsa ya yi muhawara da shi, alhali ga ɗabi’ar gungunsa na cin mutunci da raina manya?

KAMMALAWA: Wannan rantsuwa, sam ba ta yi ba kuma ba buƙatar kafa hujja da aya ta 61 ta Al-Imran, don ba ta da alaƙa da abun da ya aikata. Kazalika ya fara karanta ayar ba TA’AWUZI ba TAHAMIDI, don ba ladabin hakan. Akwai ƙalubalen ya sake ɗaga Alƙur’ani ya rantse cewa ƙabilanci halal ne. Ba ma buƙatar hujjar wai Bahaushe koya masa ƙabilanci aka yi. Waye Bahaushen da suke magana a kai? A dukkan matakai, Bahaushe ke mulkin kansa da tsara duk abun da yake buƙata a rayuwarsa – koma bayan Hausawan Bogi, da suke ɓoye kansu don samun damar surfa ashar da kunna fitinar yaƙin basasa na ƙabilanci.

__________

Previous Post

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

Next Post

Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Related Posts

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?
Gizago

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

August 13, 2026

Tsakanin Rarara Da Pantami: Yayin Da Maroƙi Ya Zaci Shi Wani Ƙusa Ne…

August 2, 2026
Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?
Gizago

Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

July 30, 2026
Next Post
Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (1)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (1)

December 6, 2023
Natasha/Senate President Tango: My Take on Senator Dandutse

Natasha/Senate President Tango: My Take on Senator Dandutse

March 8, 2025
Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai Ya Kafa Kwamitin Wayar Da Kan Al’umma, Cusa Ɗa’a, Kishin Ƙasa Da Kyawawan Ɗabi’u

December 7, 2023
Tinubu Ya Ƙwace Muƙamin Minista Daga Maryam Shatty

Tinubu Ya Ƙwace Muƙamin Minista Daga Maryam Shatty

August 4, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Our Daily Message
  • Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina
  • Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Our Daily Message

Our Daily Message

August 14, 2026
Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina

Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina

August 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.