Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Batun da a yanzu yake bazuwa shi ne, idan Allah ya kai mu gobe Litinin, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso zai canja sheƙa daga Jam’iyyar NNPP, zuwa Jam’iyyar ADC. Ana kuma hasashen cewa zai yi haɗaka a takarar shugabancin ƙasa tsakaninsa da Peter Obi. Wannan sabon shiri, yana nuna yadda siyasar Najeriya ke sauyawa cikin sauri, yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Duk da cewa wannan batu na tikitin Obi da Kwankwaso har yanzu jita-jita ne, yana bayyana manyan abubuwa uku: haɗa kan ‘yan adawa, daidaita yankuna da kuma neman samar da adawa mai ƙarfi domin ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Wannan nazari zai duba ƙalubale da damarmakin da ke tattare da wannan haɗaka na manyan ‘yan siyasa biyu daga Kudu da Arewa.
Ɗaya daga cikin manyan ƙarfinsu shi ne haɗuwar yankuna. Obi yana da ƙarfi sosai a Kudu maso Gabas da wasu sassan Kudu maso Kudu, yayin da Kwankwaso yake da babban tasiri a Kano da yankin Arewa maso Yamma. A zaɓen 2023, Kwankwaso ya nuna ƙarfinsa a Kano, yayin da Obi ya samu goyon bayan matasa da masu ilimi a faɗin ƙasa. Haɗuwar waɗannan masu ƙarfi da tasiri a siyasance, yana iya samar da babban canji a zaɓen 2027.
Sai dai babban ƙalubale shi ne batun haɗin kai da tsari. Jam’iyyar ADC har yanzu tana tasowa kuma tana fuskantar saɓani a cikin gida. Domin wannan tikiti ya yi nasara, dole ne a samu fahimta tsakanin Obi, Kwankwaso da sauran masu ruwa da tsaki, musamman ma dai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, wanda babban jigo ne a siyasar ƙasar nan. Muddin bai jingine bukatarsa ta takara ba, to wannan tikiti na su Obi/Kwankwaso ba zai tabbata ba. Rashin wannan haɗin kai na iya haddasa rikici kafin ma a kai ga zaɓe.
Wani ƙalubale kuma shi ne wanda zai jagoranci takarar a matsayin Shugaban Ƙasa. Magoya bayan Obi suna son ya tsaya takarar Shugaban Ƙasa, haka shi ma Kwankwaso, nasa mabiyan masu ƙarfi, shi suke so ya jagoranci takarar. Wannan batu yana iya jawo saɓani mai tsanani, wanda zai iya rusa shirin haɗin gwiwar gaba ɗaya.
Haka kuma akwai matsalar yadda magoya baya za su karɓi juna. A siyasar Najeriya, ba lallai ba ne magoya bayan mutum su bi sabon shirin kai tsaye. Wasu magoya bayan Obi na iya jin shakku game da ‘yan siyasar Arewa, yayin da wasu na Kwankwaso ba za su ga Obi a matsayin wanda ya dace ba. Don haka akwai buƙatar gina aminci da yarda tsakanin ɓangarorin biyu.
Duk da haka, akwai dama idan aka duba yadda ‘yan adawa ke ƙoƙarin haɗa kai. Idan aka tsara wannan haɗin kai yadda ya kamata, zai iya zama babbar dama da za ta haɗa sauran ‘yan siyasa da masu goyon baya daga sassa daban-daban na ƙasa.
Amma ƙalubalantar Shugaban Ƙasa, wanda yanzu haka yake a kan mulki kamar Bola Ahmed Tinubu, ba abu ne mai sauƙi ba. Tinubu sanannen ɗan siyasa ne mai dabaru da ƙarfi a tsarin siyasa. Jam’iyyar APC tana da ƙarfin iko da gwamnati. Ita ke da mafi rinjayen Sanatoci da ‘Yan Majalisar Wakilai da Gwamnoni. Haka kuma ita ke riƙe da dukiyar ƙasa. Waɗannan za su yi matuƙatar tasiri da fa’ida sosai a zaɓe.
Haka kuma, ƙuri’un Arewa suna da matuƙar muhimmanci. Duk da cewa Kwankwaso yana da ƙarfi a Kano, ba a tabbatar zai iya samun cikakken goyon bayan Arewa baki ɗaya ba. Idan ba a samu cikakken goyon bayan Arewa ba, zai yi wuya su yi nasara.
Batun lokaci ma yana da muhimmanci. Har ya zuwa yanzu wannan haɗaka tana cikin jita-jita, kuma rashin yanke hukunci da wuri na iya ba jam’iyyar APC damar ƙara ƙarfafa kanta da kuma raba kan ‘yan adawa.
Duk da waɗannan ƙalubalen da aka zayyano a baya, yanayin tattalin arziki da yadda rayuwar al’umma ke cikin walagigi suna iya ba su dama. Matsin rayuwa da rashin jin daɗin jama’a na iya sa mutane su nemi sauyi. Haɗin Obi da Kwankwaso na iya jan hankalin waɗanda ke son shugabanci mai nagarta da kuma kusanci da talakawa.
A ƙarshe, haɗakar Obi da Kwankwaso na da jan hankali amma nasararta ba tabbatatta ba ce. Tsarin yana da damar canza siyasar ‘yan adawa a Najeriya amma tabbas yana fuskantar manyan ƙalubale. Nasarar Obi/Kwankwaso a 2027 za ta dogara ne da yadda za su iya haɗa kai, gina ƙarfi a faɗin ƙasa da kuma samun goyon bayan al’ummar ƙasa, su fito su yi masu ruwan ƙuri’u a ranar zaɓe.
__________













