Malumfashi Mun Yi Babban Rashi
Daga Abdul’aziz Sardaunan Matasa

__________
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!
Jiya Laraba, 06-10-1447 (Hijiriyya), 25-03-2026 (Miladiyya), mun yi rashin aboki na ƙwarai. Mutum mai kyawawan halaye, Army Shehu Ladan.
Rasuwarsa ta bar babban giɓi a zukatanmu, giɓin da kalmomi ba za su iya cike shi ba.
Shehu ya shafe rayuwarsa yana kira zuwa zaman lafiya da haɗin kai. Ya kasance mutum mai gaskiya da riƙon amana, wanda ya sadaukar da kansa wajen koyar da Sunnah ta Musulunci cikin hikima da tawali’u. Halayensa na kirki, haƙuri da tausayi sun sanya kowa yake ƙaunarsa.
A gare ni, Shehu ba kawai aboki ba ne, ya zama ɗan uwa, abokin shawara. Tare muka taso a rayuwa. Mun yi rayuwa tare tun muna yara. Tun daga wancan lokaci, ya kasance mutum mai ladabi, sauƙin kai kuma mai mu’amala mai kyau da kowa.
Bai taɓa neman ɗaukaka ba amma tasirinsa ya bayyana a rayuwar mutane da dama. Ya kasance mai haɗa kan jama’a da yaɗa alheri a duk inda ya je.
Kodayake ya bar duniya, kyawawan ayyukansa da darussan da ya koyar za su ci gaba da rayuwa a cikin zukatanmu.
Allah ya gafarta masa, ya ji ƙan shi da rahama, ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, ya kuma ba iyalansa da mu baki ɗaya haƙurin jure wannan rashi. Ba za mu taɓa mantawa da kai ba.
______________













