• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, April 6, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (15)

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
March 23, 2026
in Gizago
0
Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (15)

Al'ummar Musulmi a yayin ibadar Sallar Idi

82
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (15)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

March 29, 2026
Al’ummar Musulmi a yayin ibadar Sallar Idi

 

_______________

√ Mummunan Buri Da Ƙudurin Hausawan Bogi ‘Yan Ba-Zata Ga Al’ummar Hausa/Fulani

Ga duk mai bibiyar rubuce-rubucen ‘Yan Ba-Zata a kafafen soshalmidiya kuma ya riƙa nazari a tsanake, zai fahimci munanan ƙudurori da burace-buracensu a kan al’ummar Musulmi, musamman ma dai Hausa/Fulani. Ba tare da rabe ɗaya biyu ba, mutum zai gane cewa, babbar manufarsu ita ce, su haifar da rikici, ruɗani kuma su ƙulla muguwar gaba, su haifar da gubar ƙabilanci tsakanin waɗannan manyan ƙabilu da suka kasance babban jigon Arewa da ma Najeriya baki ɗaya.

Ta yaya za su cin ma wannan alkaba’i nasu? Tuni suka gano cewa, babban sinadarin da ya haɗa kan al’ummar Hausa/Fulani, shi ne addinin Musulunci, wanda ya ginu a kan kalma ɗaya ta ‘La’ilaha illallahu Muhammadun Rasulullah. Sun daɗe da sanin cewa Musulunci ya daɗe da yin  tasiri a rayuwar Hausawa da Fulani – sun zama ‘yan uwan juna, masu alƙibla ɗaya. Don haka, babban aikin da suka tunkara shi ne, su kawo rarrabuwar kai tsakanin waɗannan al’umma.

Yana daga cikin ƙudurinsu, su haifar da ƙabilanci. Dalili ke nan suke yekuwa da cewa Bahaushe ya zauna a inuwar ƙabilarsa ta Hausa zalla, shi ma Bafulatani ya tsaya ga tasa ƙabilar zalla. Dalili ke nan ya sanya suke bijiro da dalilai da tarihe-tarihen ƙarya, domin su haifar da gaba da tsana tsakanin Hausawa da Fulani. Dalili ke nan suka ɗauki karan tsana suka ɗora wa dukkan manyan malaman Musulunci, musamman Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

A shirme da wautar ‘Yan Ba-Zata, yadda al’ummar Musulmi (Hausawa da Fulani) suke gudanar da ibadar sallolin farilla tare, bisa jagorancin liman guda, buƙatarsa su wargaza wannan tsari. Su a gurguwar dubararsu, so suke wai Musulmi Hausawa su ware masallacinsu su kaɗai, su daina cuɗanyar ibada tare da Fulani.

Hatta ibadar Azumin Ramadan, wanda Musulmi ke gudanarwa sau ɗaya a shekara, ‘Yan Ba-Zata suna baƙin ciki da haka. Dalili ke nan suke laɓaɓowa ta wannan, suna haifar da ruɗani. Su ne za ka ji suna sukar Sarkin Musulmi, suna kira ga Musulmi Hausawa da su daina biyayya gare shi, domin a nufinsu, shi Bafulatani ne. Hatta  fuskar neman ilimi a Islamiyya ko kuma halartar tarukan wa’azi, za ka ji suna suka, suna neman haddasa ruɗani tsakanin ƙabilun nan biyu. Kwata-kwata, ba su son su ga Hausawa da Fulani suna taruwa a islamiyoyi tare. Ba su so su ga ana taruwa a wajajen wa’azi ko bukukuwan mauludi da sauransu. Dalili ke nan suke kaurara muhimmancin al’ada bisa addini. A wautarsu, wai Hausawa su bar tsarin Musulunci, su rungumi gargajiyanci da maguzanci.

A shirmen ‘Yan Ba-Zata, suna buƙatar Hausawa da Fulani su daina haɗuwa a taron ɗaurin aure, su daina haɗuwa a layin gidan mai da kasuwa, su daina musharaƙa da juna a filayen wasanni ko wurin aiki ko kuma su kasance a jam’iyyar siyasa ɗaya. Su a shirmensu, Hausawa su tsaya ya junansu a kowane al’amarin rayuwa!

Su a wautarsu, Bahaushe ya daina auren matan Fulani. Matan Fulanin ma da suke aure a gidajen Hausawa, duk a sake su, a amshe ‘ya’yansu. Haka su ma matan Hausawa da suke aure a gidajen Fulani, duk a sake su. Suna son Bahaushe ya daina cin naman da Bafulatani ya yanka. Shi ma Bafulatani ya daina cin yankan Bahaushe. A taƙaice dai, kowace ƙabila ta ware iya ita kaɗai, ta yi rayuwa.

Babban abin da ‘Yan Ba-Zata suke buƙata shi ne, Hausawa su ƙulla gagarumar gaba tsakaninsu da Fulani, kamar dai yadda ta taɓa faruwa tsakanin ƙabilun Hutu da Tutsi a ƙasar Ruwanda, a shekarun baya. Abin da suke son gani shi ne, duk inda Bahaushe ya gamu da Bafulatani, ya k+she shi, mace ko namiji, yaro ko babba. Wannan shi ne ƙudurinsu, shi ne muradunsu a kullum. A dukkan rubuce-rubucensu, abin da suke kambamawa ke nan.

‘Yan Ba-Zata da iyayen gijinsu, suna amfani da ‘yan bindigar daji wajen shafa wa dukkan ƙalibar Fulani tambarin ta’addanci. Da zarar sun saki bidiyo, su ne kan gaba wajen yaɗawa tare da kiran a tsani ƙabilar Fulani gaba ɗaya, mai laifi da marar laifi. A hannu ɗaya kuma, suna kawar da kai ga laifukan ta’addanci da wasu ƙabilu ke aikatawa.

Misali, suna ba ‘yan ta’addan IPOB kariya, kamar yadda ba su kiran ‘yan ƙabilar Birom da sunan ‘yan ta’adda, duk kuwa da cewa wasu daga cikinsu suna tare hanya suna k+she mutane a garuruwansu. Haka ma, ba su yin jam’i wajen kiran dukkan Kanuri da ‘yan ta’adda, duk da cewa ‘yan ƙabilar ne suka yi ƙaurin suna a Boko Haram.

Ya Allah, muna roƙon ka, ka ƙara haɗa kan al’umma bisa addinin Musulunci. Ka kunyata kafirai da kafirci. Allah ka ba mu zaman lafiya da yalwar arziƙi. Allah ka yi mana maganin dukkan ‘yan ta’adda, manya da ƙananan da dukkan masu ɗaukar nauyinsu. Amin-Summa-Amin.

_______________

Previous Post

YAU TAKE SALLAH!

Next Post

Nigeria 2027: How Viable is Obi/Kwankwaso ADC Ticket?

Related Posts

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso
Gizago

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

March 29, 2026
Shin An Sallami Malam El-Rufa’i Ke Nan Ko Zai Dawo Shari’a?
Gizago

Shin An Sallami Malam El-Rufa’i Ke Nan Ko Zai Dawo Shari’a?

March 28, 2026
Next Post
Nigeria 2027: How Viable is Obi/Kwankwaso ADC Ticket?

Nigeria 2027: How Viable is Obi/Kwankwaso ADC Ticket?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

TSOKACINMU NA YAU (17)

TSOKACINMU NA YAU (17)

March 17, 2025
The Soul of Bukar Usman

The Soul of Bukar Usman

May 11, 2024
An Ƙarfafa Ƙawance Tsakanin Jigawa Da Zinder

Ambaliya: Gwamnan Jigawa Ya Nemi Tallafin Bankin Duniya

July 8, 2023
BIU: A Visit to a City on a Plateau (4)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (4)

January 4, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)
  • JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

April 5, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

April 4, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.