RAMADAN KARIM: 21-1447

__________
‘Yan uwa, ina yi maku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Yau Talata, Allah ya nuna mana rana ta 21 a Ramadan. Yau ma ga nasiharmu:
Babu shakka matsalolin rayuwa sun yawaita a al’ummarmu. Yunwa ta yawaita ga talakawa, akwai rashi na komai na rayuwa. Nasiharmu a yau zuwa ga al’umma gaba ɗaya, musamman waɗanda Allah ya hore wa dukiya, ita ce su ciyar da mabuƙata.
Allah (swt) a Suratul Insan 76:8 yana cewa: “Suna ciyar da abinci saboda son Allah.” Annabi (saw), a Hadisin Bukhari mai lamba 5373, yana cewa: “Ku ciyar da mabuƙata…”
Haka kuma, muna kira ga shugabanni da su ƙaunaci Allah, su sassauta wa talakawa a mulkinsu. Allah sa mu dace, Amin!
__________













