MALUMFASHI MUN ƘARA BABBAN RASHI A YAU

__________
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
A yau Alhamis, 09-09-1447 (Hijiriyya), 26-02-2027 (Miladiyya), mun yi babban rashin ɗan uwa, Injiniya, Dokta Tukur Tingilin .
Allah da ikonsa, ya rasu ne da maraicen yau, a sakamakon haɗarin mota da ya yi a wajen Musawa, Jihar Katsina, a yayin da yake komawa Katsina daga Malumfashi, inda ya je gaisuwar matashi Mubarak da shi ma ya rasu shekaranjiya.
Marigayi, Injiniya Hassan Tingilin, kafin rasuwarsa, shi ne Manajan Darakta na Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina.
Zannan Galadiman Katsina, Tukur mutumin kirki ne na gani na faɗa – Mai kishin al’umma! Allah ya ji ƙan shi da rahama!
____________













