RAMADAN KARIM: 08-1447

__________
‘Yan uwa, ina yi maku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Bayan haka, a yau Laraba, Allah ya nuna mana rana ta 8 a Ramadan. Yau ma ga ‘yar nasiha:
Har kullum dai za ka ji ana kiran kalmar gaskiya da kuma kishiyarta, watau ƙarya. To, yau za mu jaddada muhimmancinta a kan kishiyar tata. Babu shakka, dukkan alheri yana tattare da gaskiya da ma’abucinta. Haka kuma dukkan sharri na tare da ƙarya da ma’abucinta.
Lallai ne mu jure mu riƙe gaskiya a kowanke lokaci. Allah (swt) ya yi kira a Suratut Tawbah 9:119, yana cewa: “Ku kasance tare da masu gaskiya.” Haka ma Manzon Allah (saw), a Bukhari, Hadisi mai lamba 6094 da Muslim, a Hadisi mai lamba 2607 sun ruwaito yana cewa: “Gaskiya tana kai wa ga alheri.”
Ya Allah, ka sanya mu kasance masu gaskiya da ƙaunar ta kuma ka tseratar da mu daga ƙarya a kowane lokaci. Amin-Summa-Amin!
__________













