Wata Mata Ta Haifi “Hatsabiban Jarirai” A Ofishin Hukumar NDLEA
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta cafke wata mata wacce take ɗauke da juna biyu a Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano, Kano bisa zargin fataucin miyagun ƙwayoyi.
Tun da farko dai, a yau Litinin, jami’an na NDLEA suka kama matar, wacce ‘yar kasuwa ce, mai shekaru 35 da ke zaune a Kano, mai suna Rabi Muhammad.
Matar tana ɗauke da ciki niƙiniƙi, kamar za ta haihu, sai dai da aka tsananta bincike sai aka gano cewa ba juna biyu bane, cikin na bogi ne.
Binciken jami’an ya gano cewa ƙoƙo ne mai ruwan hoda ta ɗaura a cikin nata. Ana kwance ɗaurin ƙoƙon sai aka gano ‘ya’yan kapsul guda 3,200 na muguwar ƙwayar Tramadol.
Dillaliyar ta ce za ta kai su zuwa birnin Kwatano na Jamhuriyar Benin domin ta sayar.
_________













