Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (11)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
√ Wane Ne Zai Iya Raba Al’ummar Hausawa Da Fulani:
Jama’a masu bibiyar wannan dogon tsokaci da haƙuri, ina yi maku sallama da gaisuwar da ta dace da natsuwar mutunci – Assalamu alaikum warahnatullahi wabarakatuhu! Bayan haka, a tsokacinmu kashi na 10, mun tattauna tambayar da ke cewa wane ne Bahaushe zalla a wannan zamani? A yau kuma za mu duba batun da ke cewa, shin wane ne a yau zai wayi gari ya ce zai iya raba alaƙar Hausawa da Fulani? Shin wai ma a wannan zamani na ci gaba, ƙabilanci muke buƙata ko haɗin kan al’umma?
Kamar yadda muka tattauna a tsokacinmu na baya, a wannan zamani na ƙarni na 21, zamanin da duniya ta zama wani dunƙulallen bagire, al’umma ba ta buƙatar ƙabilanci a tsarin rayuwa, muddin dai ana son ci gaba, muddin dai ana son walwala da rayuwa cikin al’ummu mabambanta. Wannan tabbas ne, musamman ganin yadda kowane mutum yake buƙatar musharaƙa ko tarayya da mu’amala da kowa, ba tare da la’akari da yarensa, ƙabila ko yankin da ya fito ba – kowa yana buƙatar kowa.
Bari mu sake tambaya, shin wane ne zai iya raba al’ummar Hausawa da Fulani, musamman a Arewacin Najeriya? Wannan abu ne mai kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Dalili kuwa shi ne, a yau waɗannan al’ummu biyu sun zama ɗaya, a sakamakon doguwar zamantakewa da ta zarce ɗaruruwan shekaru. An yi auratayya, an hayayyafa ta yadda kusan duk wani gidan ƙabilar Fulani, sai ka samu jinin Hausawa a cikinsu, haka kuma abin yake a kusan kowane gidan Bahaushe, sai ka samu jinin Fulani.
Wani babban al’amari kuma shi ne, a wannan zamani, kusan kowa ma Bahaaushe ne a Arewa, domin kuwa Hausa ya zama “Yaren Dole” ga kowa, musamman a Arewa. A yau idan aka ce a yi “A Ware” Hausawa su keɓe a wuri guda, ina da tabbacin za a samu kaso mafi yawa daga al’umma da za su shiga rukunin Hausawa, duk kuwa da cewa yaren iyayensu na asali ba Hausa ba ne, amma a yau su ba su ma iya kowane yare ba sai Hausa.
Haka kuma, akwai wata babbar ƙugiya mai matuƙar muhimmanci, wacce ta haɗa al’ummun Hausawa da Fulani, musamman a Arewa. Wannan ƙugiya kuwa ita ce MUSULUNCI. A Arewa, kusan kowane Bahaushe Musulmi ne – sai ƙalilan da suke cikin Kiristanci da Maguzanci. Haka abin yake ga Fulani, kusan kowa Musulmi ne, duk da cewa akwai kaso mafi ƙanƙanta daga cikinsu da suke Kiristanci da Maguzanci.
Tun da dai Hausawa da Fulani akasari Musulmi ne, to ta kwana gidan sauƙi. Ba su da buƙatar su koma cikin jahiliyya – Ƙabilanci da Maguzanci. Addinin Musulunci ya ɗinke su zuwa gida ɗaya, ‘yan uwa ɗaya, ɗabi’a ɗaya. Ya ƙwato su daga duhun jahilci, ya haramta masu ƙabilanci, sun zama ‘yan uwan juna, kasancewarsu Musulmi. Don haka Hausawa da Fulani ba su buƙatar wariyar ƙabilanci. Idan suka yi haka, sun ci baya, sun bar haske sun faɗa duhu, sun bar Musulunci sun koma Maguzanci.
Hausawa da Fulani, waɗanda mafi yawansu Musulmi ne suna da jagora, wato Musulunci. Allah (swt) da Manzonsa Muhammadu (saw) sun haramta ƘABILANCI saboda muninsa ga al’umma. Ƙabilanci bai haifar da komai na alheri sai rabuwar kai da gaba a tsakanin al’umma.
Ya kai Bahaushe da Bafulatani Musulmi, ga abin da Allah ya ce a Alkur’aninsa mai girma: A cikin Suratul Hujurat , watau sura ta 49, aya ta 13, Allah ya sanar da mu dalilin da ya sanya ya halicce mu cikin ƙabilu da yaruka mabambanta, inda ya ce: “Ya ku mutane! Lallai ne mun halicce ku daga namiji da mace kuma muka sanya ku al’ummomi da ƙabilu domin ku san juna. Lallai mafi ɗaukaka daga cikinku a wajen Allah shi ne mafi tsoronsa. Lallai Allah masani ne, mai ƙwarewa.”
Ma’ana: Allah ya bayyana cewa ya halicci mutane ne daban-daban, ya sanya su cikin mabambantan ƙabilu ne domin su san juna, ba don su yi gaba da juna ba. Mafi daraja a wajen Allah shi ne mai tsoronsa, ba ƙabila ba. Hakan shi ke nuna cewa babu wani dalili da zai sa Bafulatani ya ƙyamaci Bahaushe kuma babu dalilin da zai su yi gaba, babu wanda ya fi wani sai mafi tsoron Allah daga cikinsu. Ke nan babu abin da ya kamace su, face su haɗa kai da juna su yi hidimar rayuwarsu cikin fahimtar juna.
A cikin Suratu Aal-Imran, wato sura ta 3, aya ta 103, Allah yana cewa: “Kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya, kada ku rarrabu. Ku tuna ni’imar Allah a kanku, a lokacin da kuke maƙiya, sai ya haɗa zukatanku, kuka zama ‘yan uwa da ni’imarsa…”
A bisa ma’anar wannan aya, Fulani da Hausawa da dukkan Musulmin duniya na kowace ƙabila ‘yan uwan juna ne. An umurce su da su watsar da ƙabilanci, su kasance cikin inuwa ɗaya ta Musulunci bisa haɗin kai da ƙaunar juna.
Har ila yau dai, Manzon Allah (saw), shugaban masu shiryar da al’umma zuwa nagarta, a cikin hadisin da Abu Dawud ya ruwaito, mai lamba 5117, ya ce: “Ba ya daga cikinmu, wanda yake kiran mutane zuwa ga ƙabilanci ko ya yi yaƙi saboda ƙabilanci ko ya mutu a kan ƙabilanci.”
Wannan ke nuna cewa haramun ne Bafulatani ko Bahaushe ko Balarabe koma wace ƙabila ce shi ya ce zai ɗauki makami ya kashe wani da ba ɗan ƙabilarsa ba. Don haka a Musulunci babu gaba, babu faɗa, babu ƙyamatar juna saboda ƙabilanci.
A wani hadisin na Sahih Muslim mai lamba 2584, an ruwaito cewa: “Wani lokaci sahabbai sun fara jayayya bisa ƙabilanci (Ansar da Muhajirun), sai Annabi (SAW) ya ce: “Ku bar wannan (ƙabilanci), ƙazanta ce!”
A Musulunci, an hana kafa ƙungiyoyi ko haɗin kai bisa ƙabila idan dai hakan zai kawo rarrabuwa ko ƙin juna. Allah da ManzonSa sun fi son haɗin kai da gaskiya fiye da dangantakar jini ko ƙabila. Don haka wannan ishara ce da ke nuna cewa FULANIN DA SUKA ƊAUKI MAKAMI suna kashe mutane, suna kan ɓata. Haka ma ba daidai ba ne Bahaushe ko Bature ko Bayarabe ko Igbo ya ce zai kafa ƙungiya domin gaba ko don ya kashe wata ƙabila.
A nan nake kira ga Hausawa Musulmi da Fulani Musulmi, su fahimta da cewa Musulunci shi ne jagoransu, ba ƘABILANCI ba. Kuma su kiyaye duk wani baragurbi da zai karkatar masu da tunani, su ce za su yi faɗa da juna. Allah sa mu dace da daidai, mu ƙaunaci juna don Allah, Amin!
_______________













