• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, April 15, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 17, 2026
in Gizago
0
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

Dakarun Daular Usmaniyya a fagen daga

33
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

March 29, 2026
Dakarun Daular Usmaniyya a fagen daga

 

                           __________

√ Yadda Ɗanfodiyo Ya Taimaki Al’ummar Musulmi Gaba Ɗaya

Jama’a masu bibiyar wannan sharhi da jimiri, Assalamu alaikum; da fatan dai muna fahimtar yadda wasu muggan mutane suke ƙoƙarin haddasa mana tsintsinar tsiya, amin.

A wannan sharhi kashi na tara, da yardar Allah za mu duba kaɗan daga cikin muhimman gudunmowa ko taimakon da Mujaddadin Musulunci, Shehu Usman Ɗanfodiyo (RTA) ya ba al’ummar Hausawa a ɓangare ɗaya da ma al’ummar Musulmin duniya baki ɗaya.

Babban taimako mafi tasiri da Mujaddadi Shehu ya ba al’ummar Hausawa, shi ne ƙwato su daga hannun duhun jahilci da shirka. Kafin jihadinsa, tarihi ya tabbatar da cewa ƙasashen Hausa, duk da cewa sarakunansu Musulmi ne amma sun gurɓata kansu da al’ummarsu da ayyukan da suka yi hannun riga da koyarwar Musulunci.

A wancan lokaci, babu abin da ke tashe sai zalunci da ƙeta daga mulaka’u. Haka ma ta fuskar mabiya, al’umma ta fitsare ƙafarta, babu abin da ke tashe sai bori da tsafi da ashararanci da rashin kunya. Allah cikin ikonsa, a sakamakon wannan jihadi na Shehu, an samu gamsassar nasarar kafa Babbar Daular Musulunci mai ƙarfi da tasiri a faɗin Nahiyar Afirka ta Yamma.

Kamar yadda na ambato wasu littattafai a muƙala ta baya da ta gabata, har yanzu dai daga gare su, mutum zai iya tsinkayar sahihan hujjojin da za su tabbatar masa da wannan bayani nawa.

Wani abin farin ciki da alfahari, a sanadiyyar wannan jihadi, an samu nasarar ƙwato al’umma daga duhun jahilci. An dakatar da zalunci, wanda ya zama ruwan dare daga sarakunan wancan zamani. An samu nasarar dawo da al’umma bisa koyarwar Musulunci na gaskiya, kamar yadda Allah da manzonsa suka umurta.

A sakamakon wannan jihadi, Bahaushe ya samu ‘yanci, ya samu izza kuma buwayarsa ta fito sarari a duniya. Harshen Hausa ya samu ɗaukaka da kulawa ta musamman a sakamakon jihadin Ɗanfodiyo saboda yadda shi Shehu da almajiransa suka duƙufa wajen rubuce-rubuce da wa’azi, ta hanyar amfani da harshen. Kafin wannan jihadi, harkar rubuce-rubuce da harshen Hausa (Ajami) ba ta bunƙasa ba sosai.

Shehu Mujaddadi, a sakamakon jihadinsa, ya kafa tsarin shugabanci mai ƙarfi da tasiri ga al’ummar Hausawa, bisa koyarwar Musulunci. Tsarin shugabancin da ya haifar da tsarkake al’umma. Ya dawo da su bisa hanya madaidaiciya.

Bahaushen da aka sani da al’adar bori da tsafi, aka canza masa tunani da ɗabi’a zuwa kaɗaita Allah ɗaya. Jihadin Ɗanfodiyo ya canza rayuwar Bahaushe daga fitsararre zuwa mutum mai kunya, mai gaskiya, mai son zumunci da ƙarfafa ‘yan uwantaka. Bahaushe ya zama Musulmi na ƙwarai, mai son Allah da manzonsa, mai neman ilimi da bunƙasa shi; maimakon a da can baya da ya kasance matsafi kuma marar tarbiyya. Hatta tsarin tufafin Bahaushe na kamala, duk sun samu ne a sakamakon faɗakarwar da jihadin Ɗanfodiyo ya kawo.

Ya kamata a nan gaɓar, mu sake tunasar da al’umma cewa, Ɗanfodiyo ba yaren Fulatanci ko ƙabilarsa ya jaddada ba. Musulunci da kyawawan al’adun addinin ya jaddada kuma ya ilimantar da al’ummar Hausawa da maƙwabtansu na ilahirin Afirka ta Yamma. Wannan Daula ta Musulunci da ya kafa, ta yi tasiri sosai, tun daga wancan zamani har zuwa yau. Dalili ke nan ma a lokacin da Turawan Mishan suka zo ƙasar Hausa, suka rasa yadda za su kafa tsarin addininsu na Kirista. Dole sai da suka fito da Tsarin-Bayan-Gida (Indirect Rule), sannan suka yi nasarar mulkar ƙasar Hausa. Amma duk da haka, Turawa ba su samu yadda suke so ba, idan aka kwatanta da yadda suka samu nasarar kai tsaye a Kudancin Najeriya, ta fuskar kafa addinin Kirista.

Ke nan, Shehu ba al’adun Fulani ya jaddada ba – Musulunci ya jaddada. Kuma ba yaren Fulatanci ya ɗaukaka ba amma ya ba yaren Hausa muhimmanci sosai, domin shi da almajiransa, sun yi rubuce-rubuce masu yawa da Hausa. Da a misali kishin Fulatanci Shehu ya jaddada, da ya tursasa al’umma ta koyi Fulfulde a kan dole kuma da ya sanya yaren nasa ya zama “Yaren Mulki” a daular da ya kafa. Wato kamar dai yadda Turawa suka tursasa harshen Ingilishi a Najeriya da sauran ƙasashen da suka yi wa mulkin mallaka.

Daga dukkan alamu, masu yaƙi da Musulunci ne suka jefo dasisar ruguza al’ummar Musulmi da Musulunci, musamman a Arewa, shi ne suka biyo ta hanyar makircin BA-ZATA; da sunan kishin Hausa da Hausawa. Babban burinsu shi ne, su haddasa gaba da ƙyamar juna tsakanin al’ummar Hausawa da Fulani, waɗanda tuni suka zama al’umma ɗaya – saboda ‘yan uwantakar Musulunci da auratayya da kuma zaman tare na tsawon lokaci.

Haka kuma, abu ne sananne cewa, a sanadiyyar jihadin Ɗanfodiyo, akasarin yawancin al’ummomin Arewacin Najeriya har zuwa wasu ɓangarorin ƙasashen Nijar da Kamaru da Chadi, duk sun zama Hausawa saboda mamayewar da yaren Hausa da al’adunsa suka yi wa nasu yarukan na asali.

Jama’a, a kashi na 10 na muƙalar nan, idan Allah ya yarda, za mu bijiro da tambayar: Shin wai ma a duniyarmu ta yau (ƙarni na 21), wane ne Bahaushe zalla?

Kafin sannan, ga saƙo zuwa gare ku, masu ƙumajin haddasa fitina tsakanin Hausawa da Fulani, ku ci gaba da zagin bayin Allah da sunan kishin Hausa. Hakan shi ke ƙara tona maku asiri da bankaɗo mugun ƙudurinku ga al’ummar Musulmi. Kuma ku sani, yadda iyayen gidanku TURAWA suka gaji da makirci suka bar DAULAR USMANIYYA don dole, haka ku ma za ku bar ta komai girman makircinku – Shi me jiya ta yi, bare yau?

_______________

Previous Post

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Next Post

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Related Posts

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso
Gizago

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

March 29, 2026
Shin An Sallami Malam El-Rufa’i Ke Nan Ko Zai Dawo Shari’a?
Gizago

Shin An Sallami Malam El-Rufa’i Ke Nan Ko Zai Dawo Shari’a?

March 28, 2026
Next Post
Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut'a

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Jihar Katsina Ta Samu Ministoci Biyu A Gwamnatin Tinubu

Jihar Katsina Ta Samu Ministoci Biyu A Gwamnatin Tinubu

July 27, 2023
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (3)

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (3)

June 22, 2025
BIU TO LAGOS: An Adventurous Journey to Honour Dr. Bukar Usman

BIU TO LAGOS: An Adventurous Journey to Honour Dr. Bukar Usman

August 24, 2024
Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

March 29, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
  • MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.