• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 19, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (1)

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
December 26, 2025
in Gizago
0
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (1)

Al'ummar Hausawa

43
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (1)

Daga Yahuza Malumfashi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Al’ummar Hausawa

 

Gabatarwa:
Da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (saw).

Bayan haka, na ƙuduri aniyar gabatar da tsokaci game da wannan al’amari mai take a sama, dangane da yunƙurin da na gani, na wasu bayin Allah da suka daddage wajen samar da wata fitina ko ruɗani a cikin al’ummar Arewa.

Babban dalilin da ya sa zan tofa albarkacin bakina kan wannan sha’anin shi ne saboda wasu salelai da na ankara da su daga wasu daga cikin masu ƙumajin samar da wata ƙungiya wai ta kishin Hausa ko kuma ta Hausawa zalla – salelan da na ankara da cewa sun yi bambarakwai, wai kiran Salla da usur.

A wannan muƙala, idan Allah ya yarda zan yi ƙoƙarin bijiro da tsokaci, tare da sharhi, domin saita hanya. Akwai zargi mai ƙarfi na cewa, ‘yan ƙungiyar Ba-Zata ne suka shirya shigar bututu domin wargaza zaman lafiya da aminci tsakanin al’ummar Arewa. Kan haka za mu bijiro da tambayoyi kamar, shin su wane ne ‘yan Ba-Zata? A wannan zamani, shin Bahaushe zalla na da ‘yancin kafa ƙungiya a Najeriya? Shin a yau kuma a wannan zamani na ƙarni na 21, wane ne Bahaushe zalla kuma ta yaya za a tantance shi har ya cancanci shiga wannan mashahuriyar ƙungiya? Haka kuma, shin su wane ne shugabannin wannan ƙungiya kuma a ƙarƙashin tagomashin wa suka tafiyar da zarafofinsu, musamman ta ɓangaren kuɗaɗe da sauransu?

Wani abin lura shi ne, su waɗannan mutane, ba za ka taɓa ganin su a zahiri suna yaɗa wannan da’awa tasu ba. Sai dai suna nan sun mamaye kafafen sadarwa na zamani. Za ka gan su a musamman Facebook da sunaye iri-iri, waɗanda da ka gani, za ka fahimci cewa ba na zahiri ba ne. An ƙirƙiri sunayen ne bisa wata manufa ta musamman, wacce ba ta alheri ba.

Akwai abubuwan lura daga ayyukan waɗannan mutane a Soshalmidiya, waɗanda ke haifar da shakka a zukatan masu hankali da tsinkaye. Abubuwa kamar yadda suke amfani da sunayen bogi, yadda suke ƙoƙarin haddasa wariya da gaba tsakanin Hausawa da Fulani, yadda suke cika da fushi da zantukar tunzura jama’a, yadda suke zagi da la’antar Malaman Musulunci, matattu da waɗanda suke raye da kuma yadda suke nuna ƙyama ga ƙabilar Fulani gaba ɗaya.

Saboda a samu sauƙin karantawa tare da bibiya cikin natsuwa da tsanani da fahimta, zan riƙa gutsura wannan muƙala ƙima-kima. Da fatan za a jure biya tare da haƙuri da juriya.
_______________

Previous Post

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

Next Post

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

Rasuwar 'Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (3)

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (3)

June 22, 2025
Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Nijeriya Ta Ba Amurka Tabbacin Ci Gaba Da Riƙo Da ‘Yancin ‘Yan Jarida

November 27, 2023
TSOKACINMU NA YAU (22)

TSOKACINMU NA YAU (22)

March 22, 2025
Batun Man Fetur: Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Jan Ido

Batun Man Fetur: Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Jan Ido

May 31, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki
  • Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
  • ALHAMDU LILLAH

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

May 18, 2026
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.