• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 12, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Abin Da Ya Sa Na Naɗa Mataimaka 85 – Ciyaman Mukhtari City

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 18, 2025
in Labarai
0
Abin Da Ya Sa Na Naɗa Mataimaka 85 – Ciyaman Mukhtari City

A dama, Shugaban Ƙaramar Hukumar Malumfashi ne, Alhaji Mukhtar Abdullahi, tare da ɗaya daga cikin SA da ya naɗa a gwamnatinsa

27
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Abin Da Ya Sa Na Naɗa Mataimaka 85 – Ciyaman Mukhtari City

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Wasu daga cikin Mataimakan da aka nada a Ƙaramar Hukumar Malumfashi

 

                           __________

Shugaban Ƙaramar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina, Alhaji Mukhtari Abdullahi City ya bayyana cewa ya naɗa mataimaka manya da ƙanana su 85 a gwamnatinsa ne domin kusanto da al’umma ga gwamnati.

Shugaban ya faɗi haka ne a wata gajeruwar tattaunawa da wakilinmu ta wayar tarho. Ya bayyana cewa ya naɗa mutane 30 a matsayin Manyan Mataimaka (SSA) bisa umurnin Gwamna Malam Dikko Umar Yadda, a yayin da ya naɗa mutane 55 don ƙashin kansa, a matsayin Ƙananan Mataimaka (SA).
“Ita harkar gwamnati ta jama’a ce, don haka na zaɓo mutanen da suke tare da jama’a kuma suke taya mu hidima a siyasa, domin su taimaka wajen tafiyar da sha’anin nan na mulkin al’umma.” Inji Ciyaman Mukhtar.

Ya ƙara da cewa, zai yi aiki da su ne a matsayin mashawarta, yadda su za su kasance idon al’umma a gwamnatinsa. Ya ce, “na umurce su da su yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da dukkan kansilolinmu, yadda za su riƙa binciko mana irin aikin da ake buƙata a kowace mazaɓa. Ta hakan za mu samu sauƙin tafiyar da aiki, tare da bunƙasa al’umma na kowane lungu a ƙaramar hukumar Malumfashi.”

Shin an ɗauke su a matsayin cikakkun ma’aikata da cikakken albashi, kuma nawa ne za a riƙa biyansu? Tambayar da wakilinmu ya yi wa Ciyaman ke nan, inda shi kuma ya amsa da cewa, “Ba cikakkun ma’aikata ba ne. Suna kan tsari ne na mataimaka, kamar yadda al’amarin yake a kowace gwamnatin siyasa. Kuma ba albashi za a riƙa ba su ba. Manyan Mataimakan, za a riƙa ba su alawus na Naira dubu hamsin, yayin da su kuma Ƙananan Mataimaka za a riƙa ba su Naira dubu talatin duk wata.”

Sai dai jim kaɗan da kammala taron naɗin, ɗaya daga cikin waɗanda aka naɗa, Malam Isma’ila A. Sanda ya sanar da ajiye mukamin nasa. Da yake bayyana wannan mataki a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa:

A hagu, Shugaban Ƙaramar Hukumar Malumfashi ne, Alhaji Mukhtar Abdullahi, tare da Malam Isma’il A. Sanda

“Da farko dai ina miƙa saƙon godiya ga mai girma Shugaban Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Hon. Mukhtar Abdullahi City, a kan muƙami da ya ba ni na Mai Taimaka Masa Na Musamman (S.A).

“Na biyu, ina mai sanar da Shugaban Ƙaramar Hukuma na aje wannan muƙami da ka ba ni, bisa ƙashin kaina ba tare da na yi shawara da kowa ba. Amma na so a ce an sanar da ni kafin a ba ni muƙamin, da sai in ba da sunan wani a cikin mutanena; kawai sai na ji kwatsam an aiko mani da takardar. Duk da haka ina godiya da har ka tuna da ni a cikin matasan da suka ba ka gudunmuwa a lokacin yaƙin neman zaɓenka a matsayin Shugaban Ƙaramar Hukuma.”
_______________

Previous Post

Hukumar NDLEA Ta Kama Ɗan Indiya Da Muggan Ƙwayoyi Na Naira Biliyan 3.9

Next Post

Yan Bindiga Sun Sako Miji Da Matarsa Bayan An Biya Naira Miliyan 50

Related Posts

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi
Labarai

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina
Labarai

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Next Post
Yan Bindiga Sun Sako Miji Da Matarsa Bayan An Biya Naira Miliyan 50

Yan Bindiga Sun Sako Miji Da Matarsa Bayan An Biya Naira Miliyan 50

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi

An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi

July 29, 2023
Sojoji Sun Bankaɗo Kamfanin Ƙera Bindigogi A Kafanchan

Sojoji Sun Bankaɗo Kamfanin Ƙera Bindigogi A Kafanchan

September 24, 2023
Minista Ya Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Zuba Jari Don Haɓaka Shirin Iskar Gas Na CNG

Minista Ya Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Zuba Jari Don Haɓaka Shirin Iskar Gas Na CNG

January 2, 2024
Yadda Bikin Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA Ya Gudana A Kabo

Yadda Bikin Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA Ya Gudana A Kabo

May 29, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)
  • Malumfashi An Yi Babban Rashi
  • Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

May 12, 2026
Malumfashi An Yi Babban Rashi

Malumfashi An Yi Babban Rashi

May 11, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.