LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

A farkon watan nan na Yuni ne al’ummar Unguwar Mata da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina suka gamu da wani abin jimami da Allah wadai, inda aka kama wani mutum mai suna Kabir Ja’afar, mai kimanin shekara 30, bisa tuhumarsa da aikata luwaɗi da yara maza 14 a lokuta daban-daban.
Tun da farko dai, mutumin da ake tuhuma, wanda aka fi sani da laƙabin “Kabir Hisba,” asirinsa ya tonu ne a sakamakon samun wasu daga cikin yaran da ya lalata suna tattauna al’amarin tsakanin junansu.
√ Yadda Lamarin Ya Faru:
A yayin binciken wannan al’amari, wakilinmu ya tattauna da wasu daga cikin iyayen yaran da abin ya shafa. Waɗannan kuwa sun haɗa da Shamsuddin Abdulƙadir, mai bi kadin al’amarin. Akwai Abdulkarim Abdulƙadir da Ayatullahi Sulaiman Direba da Malam Zaharaddin Ibrahim da kuma Malam Haladu Injiniya.
Malam Shamsuddin ya shaida wa wakilinmu cewa ɗaya daga cikin yaran da abin ya rutsa da su, ɗan yayansa ne. Ya ce sai da al’amarin ya faru ne bayanai suka yi ta fitowa, cewa mutumin da ake tuhuma ya daɗe yana aikata wannan baɗala. “Mun samu labarin cewa kafin ya zo zama a unguwarmu, an taɓa koro shi daga ƙauyen Mashigi bisa zargin wannan mummunar ɗabi’a. Haka ma, ya taɓa zama a Unguwar Bayan Kotu kuma ya baro ta, a sakamakon kama shi da irin wannan tuhuma.” In ji Shamsuddin, wanda ya yi Allah wadai da al’amarin.
Shi kuwa Abdulkarim Abdulƙadir, a nasa ɓangaren, ya ce akwai ɗansa ɗaya da al’amarin ya rutsa da shi. A cewarsa, ya dawo gida a wata ranar Lahadi da yamma, shi ne ya iske matar Muttaƙa Injiniya a gidansa, tana shaida mata yadda ta gano cewa ɗanta na cikin waɗanda aka lalata. Ta haka muka gano cewa har da nawa ɗan a ciki, kasancewar tare suke yin wannan atisaye na Hisba a ƙarƙashin Kabir Hisba.
“Daga nan na shiga binciken yaran, inda ni da maƙwabtana, muka tattara yara guda biyar. Kowanensu ya shaida mana yadda Kabir Hisba ya riƙa aikata luwadi da su.” In ji Malam Abdulkarim, wanda ya ƙara da cewa sun gano yara 14 da al’amarin ya rutsa da su, waɗanda dukkansu daga ɗan shekara 13 da 14, sai 15 zuwa 16.

A cewarsa, shi da iyayen yaran, sun kai ƙorafin al’amarin zuwa ofishin Hisba Board na Ƙaramar Hukumar Malumfashi, inda daga bisani aka tattara aka miƙa su ga ‘yan sanda na Malumfashi.
“Yan sanda a Malumfashi sun yi abin da ya dace game da al’amarin,” in ji Abdulkarim. Ya bayyana cewa lokacin da ofishin Hisba ya miƙa lamarin gare su, DPO na Malumfashi sai ya miƙa lamarin ga DCO, wato babban jami’in bincike na Hukumar ‘Yan Sanda ta Malumfashi.
“A gabanmu DCO sai da ya binciki yaran nan guda 14 ɗaya-bayan-ɗaya kuma kowanne yaro sai da ya bayyana yadda abin ya faru da shi kuma ya nuna tare da ambata sunan Kabir Hisba, wanda yake zaune a gaban DCO ɗin tare da mu. Kuma shi Kabir da ake tuhuma, bai musa dukkan bayanan da yaran suka yi a kansa ba.” A cewar Abdulkarim, wanda ya ƙara da cewa daga bisani ‘yan sanda suka ɗauke su tare da dukkan yaran 14 zuwa Babban Asibitin Malumfashi, inda aka yi masu gwaje-gwaje dangane da lamarin. Ya ce kuma binciken ya tabbatar da cewa lallai an aikata wannan mummunan al’amari da yaran. Haka kuma ya ce, an gano cewa wasu daga cikin yaran ma sun kamu da wasu cututtuka.
√ Wane Ne Kabir Hisba?
Kamar yadda binciken wakilinmu ya tabbatar, cikakken sunansa Kabir Ja’afar amma ana yi masa laƙabi da “Kabir Hisba” wasu kuma suna kiran shi da “Kabir Izza.” Shi ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Malumfashi ne a Jihar Katsina. Asalinsa ɗan Layin Malam Isa ne, unguwar da ke kusa da Makarantar Firamare ta Dudi.
“Kusan shekararsa ɗaya ke nan yana zaune a Unguwar Mata a nan Malumfashi. Tela ne shi, don haka ya kama hayar shago a unguwar kuma yana ɗaukar yaran unguwar yana koya masu ɗinki.” A cewar Malam Abdulkarim, wanda ya ƙara da cewa kuma Kabir yana koyar da yara darussan Musulunci, a ranakun Asabar da Lahadi a makarantar Alhikma Academy da ke cikin unguwar. Bayan haka kuma shi Kwamanda ne na Hisba a unguwar, wanda ke ƙarƙashin Masallacin Jumu’a na Bilal Bin Raba.
Kamar yadda binciken wakilinmu ya gano, Kabir Hisba, a matsayinsa na Kwamandan Hisba, yakan ɗauki yaran zuwa atisaye a kowace Asabar da Lahadi kuma yana koya wa wasu daga cikinsu sana’ar ɗinki a shagonsa. A shagon nasa, mutanen unguwar sun yi zargin a nan ya riƙa aikata wannan baɗala, kasancewar akwai wani sashi da ya killace da labule, kamar dai yadda masu kemis-kemis ke ware wurin da suke ganawa da marasa lafiya.

Wakilinmu ya tuntuɓi Limamin Masallacin Juma’a na Bilal Bin Raba, Unguwar Mata, Sheikh Yusuf Hussaini, dangane da lamarin. Ya ce babu shakka Kabir Hisba jami’in Hisba Board ne a Ƙaramar Hukumar Malumfashi amma ba a ƙarƙashin masallacin ya fara aikin Hisba ba. Ya fara tun kafin ma a gina masallacin kuma tun kafin ya zo unguwar da zama.
Liman Yusuf ya ce “Kabir ya buƙaci ya riƙa yin hidima a masallaci. Mu kuma saboda mun san shi a matsayin ɗan Hisba, ba mu hana shi ba amma ko kaɗan ba mu san yana da mummunan hali irin wannan ba. Duk abin da ake tuhumarsa da aikatawa, idan ya aikata, ya aikata ne don ƙashin kansa, babu hannun masallaci a ciki.”
Mun tuntuɓi Daraktan Makarantar Alhikma Academy, Unguwar Mata Malumfashi, Malam Muhammad Lawal Umar game da lamarin Kabir Ɗan Hisba. Ya shaida wa wakilinmu cewa babu shakka yana koyar da yara a sashin Islamiyya na makarantar tasu amma dai ba ya da masaniyar cewa yana da mummunan hali, har sai da al’amarin ya fito fili.
“Ban san da lamarin ba, sai da ‘yan sanda suka kama shi, shi ne fa na samu bayani daga mutanen unguwa, cewa an daɗe ana zarginsa da wannan ɓarna. Shi ne na ce amma me ya sa suka ɓoye har abin ya girma haka? Na ce lallai ba a yi mana adalci ba kuma ba a yi wa al’umma adalci ba. Ni dai na san cewa shi Kabir ɗan Hisba Board ne a Malumfashi amma lallai babu ruwan makarantarmu da abin da ya aikata.” In ji Daraktan Makarantar Alhikma.
√ Mece Ce Alaƙar Hisba Da Kabir Ja’afar?
Walikinmu ya yi bincike dangane da alaƙar da ke tsakanin Kabir Ja’afar da kuma Hisba, inda ya gano cewa tabbas shi jami’in Hisba ne, wanda dalili ke nan ma ya samu laƙanin Hisba a sunansa. Kamar yadda iyayen yara a Unguwar Mata Malumfashi suka shaida, idan mutum yana neman shi, sai ya sanya laƙabin “Hisba” sannan ake tantance shi.
Sai dai kuma a tattaunarmu da Ma’ajin Ƙungiyar Hisba Lajna ta Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Malam Nasir Abdullahi, ya shaida mana cewa yanzu a Jihar Katsina, Hisba ta rabu gida biyu, akwai Hisba Board ta Jihar Katsina kuma akwai Lajnatul Hisba, wacce ke ƙarƙashin Ƙungiyar Izalatul Bid’a Wa’iƙamatussunna.

“Shi Kabir, babu shakka mun san shi amma yana ƙarƙashin Hisba Board ta Ƙaramar Hukumar Malumfashi, ba Hisba Lajna tamu ba. Kuma muna takaicin wannan abu da ake zarginsa da aikatawa,” in ji Malam Nasir.
Haka shi ma Shugaban Ƙungiyar Najlatul Hisba Reshen Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Malam Shehu Ladan, ya tattauna da wakilinmu ta waya. Ya nuna rashin jin daɗinsa da faruwar wannan al’amari. Ya ƙara da cewa, irin waɗannan abubuwa na rashin ɗa’a da kuma yadda ake ɗaukar mutane barkatai a cikin aikin Hisba, na daga cikin dalilan da suka sa aka samu rarrabuwar ƙungiyoyin Hisba. Ya ce mutumin da ake zargi da wannan rashin ɗa’a, ba ɗan ƙungiyarsu ba ne, ɗan Hisba Board ne. “Ina kira ga ƙungiyoyi da cibiyoyin da ke wa al’umma hidima da su riƙa tantance mutanen da suke ɗauka, suna binciken halayensu, kafin a amince da su;” in ji Malam Shehu.
√ Ya Al’amarin Yake Ciki A Hukumance?
Wakilinmu ya tuntuɓi Hukumar ‘Yan Sanda a Ƙaramar Hukumar Malumfashi, inda Jami’in Sashen Bincike (DCO) ya shaida masa cewa sun samu ƙorafin wannan al’amari kuma sun kammala bincike a matakinsu. Ya ce ya zuwa yanzu sun mika kundin bincikensu da wanda ake zargi zuwa Hedkwatar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina, domin faɗaɗa bincike da ɗaukar matakan da suka dace a hukumance.

Shi ma Shugaban Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Alhaji Mukhtar Abdullahi, da wakilinmu ya buƙaci jin ta bakinsa dangane da lamarin, ya nuna ɓacin ransa da al’amarin. Ya ce ba ya goyon bayan duk wani da aka samu da aikata mummunan aiki. “Ba zan ce komai ba kan sha’anin da aka ce ya haɗa da irin wannan ɓarna. Lallai idan hukuma ta bincika kuma ta tabbatar da wannan laifi, ina goyon bayan Shari’a ta hukunta shi.” In ji Ciyaman Mukhtar City.
Ta ɓangaren iyayen yaran da abin ya shafa kuwa, a ta bakin Shamauddin Abdulƙadir ya ce “muna roƙon Gwamnan Jihar Katsina, Dokta Dikko Umar Raɗɗa da sarakunanmu da dukkan shugabannin al’umma da su sanya hannu wajen ganin an yi mana adalci, a hukunta mai laifi. Haka kuma muna son gwamnati ta sanya hannu wajen sama wa yaranmu da aka lalata lafiya.” Haka suma al’umma, musamman waɗanda suka ji labarin nan, sun yi Allah wadai da lamarin kuma sun buƙaci hukuma da ta tabbatar an hukunta duk wanda aka samu da laifin aikata wannan ɗanyen aiki.













Kunyi kokari matuka wajen bincike da baiyana barna, Allah ta’ala ya kaura mana irin wadannan musifu acikin al ummarmu. Amma Ina bada shawara Nan gaba irin wannan rahoton bai kamata arinka Kiran sunan iyayen yaran ballantana har a Sanya hotonsu wannan bai daceba domin yanzu Sanya sunan iyayen yaran ya baiyana yaran har mutuwarsu wannan tabon ba zai gusheba, Allah karka jarabcemu da musiba irin wannan.
Tabbas wannan labari na kabir hisbah ya girgizani. AlLah ya tsare Mutuncimu da imaninmu
Assalamu alaikum
ina kira ga hukuma da kuma gwamnatin jihar katsina da ta sanya hannu kan lamarin kabir ja’afar (kabir hisbah)
wajen ganin cewa an hukuntashi daidai da abin da ya aikata kamar yadda addinin musulinchi ya tanada saboda ya chi amanar hisbah da kuma al ummar garin malumfashi a bisa yadda da amincewa da sukai da shi amman kuma ya ci amanar su.
da haka ne nike kira ga gwamnatin jihar katsina da ta taima kawa iya yan yaran wajen ganin an samu lafiyar yaran da abin ya faru da su.
writing by
Usman Auwal
(CAPTAIN MLT)
Alhamdulillah wadannan mutane wadanda suka tsaya tsayin daka, kuma sukayi bincike Allah Madaukaki ya saka masu da ALKHAIRI. Wannan shine abunda ya dace saboda haka muna kira ga shuwagabanni da duk wanda keda alhakin hukunta wannan yaro/matashi to a dubi girman Allah ayi masa hukuncin da ya dace saboda ya gane KUSKURENSA. Su kuma iyaye musamman masu zama a cikin unguwanni da su kara zage DAMTSE dan ganin sun kare hakkin AL’UMMA. Allah yasaka da ALKHAIRI… daga kare muna ma wannan bawan Allah ADDU’A UBANGIJI ALLAH YA SHIRYASHI…