Ƙungiyar BUWDA Abin Alfahari Ce Ga Al’ummar Bura Da Duniya Baki Ɗaya
– Dokta Bukar Usman
_______________
Wannan shi ne jawabin Dokta Bukar Usman, a matsayinsa na Babban Baƙo mai jawabi a Bikin Ranar Al’ummar Bura, wanda Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura (Bura Women Development Association – BUWDA), reshen Babban Birnin Tarayya, Abuja ta gudanar tare da ƙaddamar da Bankin BUWDA Microfinance da kuma gyaran gidan saukar baƙi na ƙungiyar a Cibiyar Horar da Sana’o’i da ke Marama, Ƙaramar Hukumar Hawul, Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya, wanda aka gudanar a AGNL Park Apo, Abuja, a ranar 12 ga Afrilu, 2025.
_______________

Gaskiya na ji daɗi kuma na yi alfahari da samun wannan dama don gabatar jawabi ga wannan taro na al’ummarmu da masoya da abokan arziƙi da suka hallara, domin nuna goyon bayansu ga Ƙungiyar Bunƙasa Rayuwar Matan Bura, reshen Babban Birnin Tarayya, Abuja da kuma uwar ƙungiya gaba ɗaya.
Na kasance mai bibiyar ayyukan uwar ƙungiyar tun kafuwarta, kuma ana sanar da ni haka kai tsaye. Na tabbata cewa ƙungiyar tana da kyawawan manufofi don inganta rayuwar jama’armu da ci gaban al’ummar Bura. Har ila yau, ƙungiyar ta dace da shugabanni masu kishi da sadaukar da kai, waɗanda suka ɗauki nauyin aiwatar da waɗannan manufofi kuma da ƙima da tawali’u. Sun gabatar da muhimman ayyuka, waɗanda za a iya kira da gani-ya-kori ji. Ayyukan suna nan a fili, musamman a Marama, inda Cibiyar Horar da Sana’o’i ta ƙungiyar take aiki. Dukkan waɗanda suka samu horo a wannan cibiya, sun amfana. Sun samu ƙwarewa da koyon sana’o’in dogaro da kai. Haka kuma cibiyar a buɗe take ga ƙarin masu son koyon sana’o’i da baƙi masu son kai ziyara. Koyon sana’a wani ɓangare ne na ilimi wanda jama’armu suka runguma tun lokacin da Turawan Mulkin Mallaka da ‘Yan Mishan suka gabatar da shi shekaru da dama da suka gabata.

A bayyane yake cewa ƙungiyar BUWDA, wadda aka kafa a shekarar 2014, ta samar da Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Marama a shekarar 2020. Gwamnatin Jihar Borno ce ta ƙaddamar da cibiyar a hukumance, a ranar 31 ga Disamba, 2022, wadda kuma ita ce ranar da aka yaye ɗaliban farko da cibiyar ta horar kan sana’o’i daban-daban.

Wannan cibiya abin alfahari ce a gare mu, kuma wata shaida ce abin misali kuma abin koyi; wacce take nuna yadda ake gabatar taimakon kai-da-kai a ƙasar Bura, Masarautar Biu, Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya. Har ila yau, wannan wani babban abin tarihi ne da ke nuna kyakkyawar niyya da sadaukarwa daga waɗanda suka assasa wannan aiki – waɗanda cikinsu har yanzu wasu suna raye, wasu kuma sun riga mu gidan gaskiya. Ya dace mu gode wa waɗanda ke raye da jinjina masu, bisa sadaukarwar da suka nuna. Su kuma waɗanda suka rasu, ya kamata mu ci gaba da tuna su ta hanyoyin da suka dace.
Yanzu da ƙungiyar ta samu sababbin shugabanni, suna ɗaukar sabbin matakai domin inganta kayayyakin da ke cikin cibiyar da samar da ƙarin wasu; domin daɗaɗa wa baƙi masu ziyara daga nesa da kusa. Shirin kafa Bankin Microfinance, wanda zai ƙara buɗe ƙauyukanmu ga harkokin kuɗi na zamani domin ci gaba da sauri a zamantakewa da tattalin arziki, abu ne mai kyau ƙwarai. Sai dai kuma kafin a fara, ya kamata a yi bincike mai zurfi na yiwuwar nasararsa da kuma tabbatar da tsayayyen tsarin kula da kuɗi. Wannan nauyi ne mai girma da ke kan shugabannin yanzu da waɗanda za su zo nan gaba. Ina fata kuma ina addu’ar cewa, shugabannin za su ci gaba da yin aiki yadda ya kamata, domin samun amincewar jama’a da ci gaban al’ummar Bura da kuma ɗorewar abubuwan alherin da waɗanda suka kafa ƙungiyar da farko suka sa gaba.

A nan, ina so in jaddada cewa koyon sana’o’i da ayyuka iri-iri, abin buƙata ne matuƙar gaske ga jama’armu, domin su ƙara a kan harkar noma, wadda ita ce babbar sana’ar gargajiya ga al’ummarmu. Ita kanta sana’ar noma, tana buƙatar sabbin dabarun zamani, domin haɓaka amfanin gona da sanar da shi mai yawa, domin biyan buƙatun jama’ar da ke ta ƙaruwa. Muna da filayen noma masu faɗi da suka dace a aikata su da injina da na’urorin noma na zamani, amma muna barin su haka nan. Lokaci ya yi da za mu rage amfani da garma da fatanya na gargajiya, marasa inganci da wahalar da jiki.

Duk da cewa abu ne mai muhimmanci mu adana tsirranmu na gargajiya, ya kamata mu samo hanyar yin hakan ba tare da hana haɓakar amfanin gona ba. Ya dace a dawo da bukukuwan nunin amfanin gona da dabbobi, domin baje kolin nuna sabbin nau’o’in iraruwa da dabbobi, kamar kuma yadda za a riƙa saka wa haziƙan manoma nagari da raba masu kyaututtukan ƙarfafa gwiwa, musamman ma samar masu da sabbin kayan noma masu inganci.

Daga ƙarshe, ina yi wa shugabannin Ƙungiyar BUWDA, reshen Babban Birnin Tarayya Abuja da uwar ƙungiyar fatan nasara a dukkan ayyukan da suka sanya gaba. Sun cancanci goyon baya a kowane mataki kuma a kan lokaci.

Na gode.
Dokta Bukar Usman, OON
Tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.













