• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

CANJIN ZAMANI: Rayuwar Mata A Ƙarni Na 21

MUƘALA

Abubakar AbdurRahman Dodo by Abubakar AbdurRahman Dodo
January 7, 2025
in Gizago
0
CANJIN ZAMANI: Rayuwar Mata A Ƙarni Na 21

Wasu mata da suka shahara a fagen ilimin zamani a wannan lokaci

102
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

CANJIN ZAMANI: Rayuwar Mata A Ƙarni Na 21 Dangane Da
Neman Ilimi, Ƙwadago Da Ɗawainiyar Iyali
Daga Abubakar AbdurRahman Dodo

Wasu mata da suka shahara a fagen ilimin zamani a wannan lokaci

Sharar Fage:
Wannan maƙala ta yi nazarin halin da mata suka tsinci kansu a ƙarni na 21, musamman ganin yadda suke karakaina wajen fafutikar neman ilimin zamani da aikin ƙwadago da raino da tarbiyyar ’ya’ya. Sannan an bijiro da shawarwarin shawo kan manyan matsalolin da ke tattare da fitar MATA da zamani ya zo mana da su. Saboda haka, sai a tausaya wa mata a cikin al’umma, ta yadda za su ji daɗin raino da tarbiyyar manyan gobe. Sannan a halin matsin rayuwa, lokaci ya yi da iyalai za su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ceton kansu da sauran al’ummar da suka rataya a kansu.

Related posts

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

January 13, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)

January 9, 2026

’Yan shekarun da suka gabata, a wannan ɓangaren na duniya, abin kawai muke iya yi a mtsayinmu na mata, shi ne kula da ayyukan gida da rainon jarirai, amma sauran al’amura (baya ga waɗannan da aka lissafo), tamkar mafarki ne kawai. Yanzu haɗakar dunƙulewar duniya a wannan zamani, inda kimiyya da fasahar ƙere-ƙere ke da tasirin juya akalar al’amuran bunƙasar rayuwar ɗan Adam, shi ya sa a wannan ƙarni na 21, mata da dama ke samun bin hanyoyi da dama, don ci gaban rayuwasu da cin ma burikansu, musamman yadda suke ta kai-kawo tsakanin makaranta da wajen aiki da kula da yara da ayyukan gida, har ma da sauran al’amura. Kina aiki ne na tsawon lokaci ko na wucin-gadi, a ofis ko a gida, duk muna yin aiki fiye da ɗaya a ’yan kwanakin nan; haƙiƙa fasahar ƙere-ƙere ta sahale mana. Tara ɗimbin ayyuka ga mutum a wani lokacin na tattare komai-da-komai. Don haka sai a tuna a ware lokacin hutu daga wannan kanainayewar alamura da suka tare wa mutum ko’ina-da-koina. A huta ko da kwanaki biyu ne, a ziyarci manyan kantunan sayen kayayyaki ko wuraren motsa jiki. A yi abin da zai shawo kan dugunzumar damuwa da wargaje wahalar gajiya ko kasalar jiki, ta hanyar motsa jiki irin na yoga.

Ga matasa (mata) da ke da zimmar shiga cikin hada-hadar rayuwa fiye da kasancewarsu uwar yaya da ke zaune a gida kawai, sai in ce, yi ƙoƙarin yin karatun dogon zango daga nesa (a wajen makaranta), wadda za ki iya samun gurbin karatun a mafi yawan jami’o’in da ke faɗin ƙasar nan, don kina da ƙarfin inganta rayuwarki ta kasance mafi kyau. – Hajiya Hadiza M. Bello, a maƙalarta mai taken, “Aikin gida da tarairayar ’yaya da aikin ofis, wadda aka wallafa a Mujallar Hukuma/Majalisar Matan Arewa, wato a harshen Ingilishi, ‘Arewa Women Commission (AWC)’ bugun farko da ya fito na Janairu/Maris, 2011.

Farfesa A’isha Sani Maikuɗi, Shugabar (Riko) ta Jami’ar Janar Yakubu Gowon, Abuja

Ƙasashen Musulmi da dama sun samu kansu a halin ƙaƙa-ni-ka-yin fitar iyaye mata, don fafutikar neman ilimin zamani da aikin ƙwadago, al’amarin da matan da ke gidan aure ke gwamawa da raino, har ma da tarbiyyar ’ya’ya. Wannan al’amari dai, tun farkon ƙarni na 19 bayan da aka samu juyin juya halin bunƙasar masana’antu a Turai ya zama ruwan dare a gare mu. Kodayake a irin ƙasashenmu na Afirka da Asiya, mulkin mallaka ne ya yi tasirin rinjayar mu. Sannan masu hangen nesa sun aminta da cewa, “juyin zamani,” a iya taka tafarkinsa ba tare da an kauce wa dokar Mahallicci ba. Yanayin zamantakewar zamanin nan ya zo mana da muhimman buƙatun mata masu kula da lafiyar majinyata da malaman makaranta, har ma da sauran fannonin ilimin inganta rayuwa. Saboda haka sai mu tsince tsaba da tsakuwa, ta hanyar tantance dabarar da ba ta ci karo da al’ada da addininmu ba.

Mujallar Newsweek ta ranar 27 ga Nuwambar 2006, a maƙalarta mai taken THERE’S NO ‘I’ IN ISLAM (BABU CEWA, ‘NI KAƊAI NE’ A MUSULUNCI), ta ruwaito a shafi na 41 cewa: “Tsarin tunanin karkata akalar bin tafarkin siyasar Turai ya yi tasiri a duniyar Musulmi. Lamari ne da ya samo asali tun cikin ƙarni na 19, inda Musulmi suka tsunduma ka’in da na’in wajen aiwatar da tsare-tsaren zamani irin na Turai, wato wajen kafa makarantu da asibitoci, al’amuran da suka kawo sauyi tattare da ƙungiyoyin Musulmin zamani, waɗanda suka shawarci Musulmi su yi haƙuri da shigowar Turawa yankinsu. Sannan suka riƙa aiwatar da sauye-sauye tattare da tunanin Tafiyar Musulunci da zamani, ta hanyar ijtihadi, saɓanin biyayya (ga tsarin Turawa) a makance ko fatawoyin malaman ƙarnonin da suka gabace su (wataƙila ganin cewa ba su riski zamanin ba, ko gudun taƙlidil a’ama).

Azyumardi Azra, wata shugabar Jami’ar Musulunci ta Hidayatullah, mallakar Jihar Jakarta da ke ƙasar Indonesiya, wadda ta rubuta wa Mujallar Newsweek maƙalar, ta ambaci wani masani da ya ƙware wajen nazari kan Musulmin Indonesiya, Robert Heifner, wani Ba’amurke da ya yi gargaɗin cewa: “Ƙungiyoyin fafutikar haƙƙoƙin al’umma na addini, dole ne a tafi tare da su, domin yasar da su ba ƙaramar illa ba ce, musamman ganin yadda irin waɗannan ƙungiyoyi da ba na gwamnati ba, waɗanda ke da alaƙa da addini ke daɗa bunƙasa, kuma suna aiwatar da ayyukan da ba na addinin ba. Sannan matuƙar shugabannin waɗannan ƙungiyoyin suka jajirce wajen tafiya da haɗakar mabambantan al’umma, tare da bin dokokin ƙungiyoyin fafutikar haƙƙoƙin al’umma, Musulunci zai yi matuƙar bayar da muhimmiyar gudunmuwa wajen ingantawa da kyautata wannan duniyar.” Kodai wane irin ci gaban rayuwa ake hanƙoron tabbatarwa, Musulmi kan yi ƙoƙarin tantance haram da halal. Domin mace ba za ta shiga gasar Sarauniyar Kyau ba, duk da cewa an samu irin su “Shatu Garko” (Allah Ya shirye ta).

Farfesa Azyumardi Azra

Mujallar WAMY ta Yunin 2006, a shafinta na 8, ƙaraƙshin maƙalarta mai taken: Ilimin Mata Na Gaskiya, ta ruwaito cewa: “A matsayinmu na mata Musulmi sai mu ƙudurce a zuciyarmu tun kafin mu fara fafutikar neman ilimin boko ko zamani (wanda aka zare addini a ciki) cewa, muna buƙatar tantance manufar da muke son cin mawa a rayuwa, saɓanin a ce, burin son ɗaukaka kawai, don a ce mace ta zama hamshaƙiya “wadda ta kai ga gacin nasara.”

Macen ƙarni na, 21 haƙiƙa ta sha bamban da matan da zamanin da ya shuɗe shekaru aru-aru, musamman ma ganin yadda zamani ya bijiro musu da hada-hadar harkokin rayuwa da suka zama tilas su riƙa fita suna gogayya da maza wajen neman abin gudanar da rayuwa; ko ayyukan yau da kullum, a ofisoshin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu. To matar aure dai malaman Musulunci sun yadda za ta iya zama malamar makaranta ko jami’ar kula da lafiyar al’umma da dai makamantansu, musamman ma ganin buƙatar da ake da ita a wannan zamanin. Sai dai dole ne ta kame kanta kada ta yi abin da zai iya ɓata ƙimar mutuntakarta. Kuma ta taƙaita kanta da yin wannan fitar ga muhimmin aiki da ya kai ta. Duk da wannan dama da zamani ya bijiro wa matanmu da ita ta fita, ya kamata su san cewa yawan fitar babu tsari na iya kawo wa aurensu tarnaƙi. Don haka sai a kula.

Farfesa Robert Heifner

Bisa la’akari da yawan fitar mata zuwa makarantu don ƙaro ilimi da ayyukan yi a ofisoshin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, Doka Sa’idu Ahmad Dukawa, a maƙalarsa mai taken, Matsalolin Yawaitar Fitar Mata Da Hanyoyin Warware Su, wadda Mujallar Muryar Malamai ta wallafa cikin watan Yunin 2013, a shafi na 25 zuwa 26, ya bijiro da ƙalubalen zamani game da fitar mata kamar haka:
* Sakacin maza wajen riƙon aure.
* Wahalar samun mijin aure.
* Yawaitar mutuwar aure.
* Riƙon marayu.
* Riƙon ’ya’ya bayan mutuwar aure.
* Buƙatar karatu mai zurfi.
* Buƙatar al’umma ta samar da mata a wuraren da suka dace (kamar asibiti da makaranta, ko fita don kaɗa kuri’a).
* Buƙatar aikin albashi don rage raɗaɗin talauci.
* Buƙatar tallafa wa miji talaka.
* Neman ’yanci da rage dogaro da miji.
* Yaƙi da fatara da talauci.
* Son tafiya da zamani.

Sai ya kasa dalilan gida uku, wato:
* Na wajibi, kamar samar da ma’aikata a wasu wurare don amfanin Musulmi,
* Masalahar fitar, kamar don neman abin riƙe marayu;
* Sai kuma na sa kai ko al’ada, kamar son tafiya da zamani ko zuwa biki ko suna.

Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa

Shehun malamin a cikin maƙalar tasa ya ce: “Ko ma mene ne dalilin fitar, matsalolin da suke biyo baya ba su bar kowa ba, ta yadda fita da niyyar ibada ita ce kaɗai za ta samar da wata riba da ake fatan ta rufe illar da take cikin fitar.”

Ina ganin malam bai taƙaita wajen abin da muke tunanin shi ne ibada, kamar Aikin Hajji ko zuwa Masallaci ba. Domin ya yi bayanin cewa, ‘akwai wuraren ayyuka da ake sanya mata don masalahar Musulmi. Wannan ma ibada ce, tun da ma’aikaciyar asibiti da malaman makaranta suna da ladar ayyukansu, musamman idan har sun nuna tausayi da jin ƙan al’umma, a wajen mu’amalar aiki, don sauke nauyin da ya rataya a kansu. Don haka Malam ya kawo matakan da ya kamata a bi, a tsakanin ɗaiɗaikun al’umma da hukumomi, wato kamar haka:

* A kauce wa ɗora wa mata nauyi da ya zama na maza a wuraren aiki.
* A yi ƙoƙarin ware wuraren maza daban da na mata.
* A kauce wa mu’amalar da ba ta aiki ba tsakanin maza da mata.
* A riƙa tausaya wa mata kan titi da wuraren cunkoso.
* A riƙa rage ba su izinin zuwa biki da bai wajaba ba.
* A samar da zaurukan jama’a don tattaunawa game da ɗaukar nauyin masu takaba da zawarawa da marayu.
* Su yawaita istigifari.

A hukumance:

* Su rage lokutan aiki ga mata.
* Su tsara wuraren zaman maza daban da na mata.
* Su ƙara lokutan hutun haihuwa da na aure da na takaba da sauransu (kwanan nan ikitoci a Asibitin Malam Aminu Kano suka ce ana buƙatar jariri ya samu aƙalla wata shida yana tare da mahaifiyarsa awa ashirin da huɗu).
* Su tanadi hukuncin da ya dace game da duk wanda ya yi wani abu da zai cutar da mata a wurin aiki ko kasuwa ko kan hanya.
* Su tanadi hukuncin da ya dace game da mazajen da suke wofintar da haƙƙin da Allah Ya ɗora musu game da mata.
* Su tanadi shirin tallafi don marayu da masu takaba da sauran masu rauni.
* Su samar da da yanayi na ƙananan sana’o’i a cikin gidaje da samar wa irin waɗannan sana’o’i kasuwanni.
* A tanadi horon da ya dace da Shari’a ga duk matar da aka samu a kwararo ba tare da hujja karƃaƃƃiya ba.
* Shugabanni su yawaita istigifari.

Ɗaukacin waɗannan matsaloli da Dokta Dukawa ya bijiro da su, har ma da hanyoyin shawo kansu, sun yi daidai da abin da jaridar Saudi Gazette ta ranar Litinin 8 ga Afirilun 2013 ta bayyana a shafinta na 4, cikin maƙalarta mai take: Al’umma Ba Su Shirya amincewa da Malaman Jinya ’Yan Saudiyya ko Larabawa ba. A cewarta: Malamar Jinya (NURSE) al-Harbi ta ce; “Ina son hidima ga marasa lafiya, in tattauna da su (don jin abin da ke damun su), sannan in taimaka musu don biyan buƙatunsu, musamman tsofaffi. A duk lokacin da na shiga shirin horar da jami’an kula da lafiya sai in ga iyayena ba sa farin ciki. A hankali, a hankali, na fara nusar da iyayena nasarorin da jami’an kula da lafiyar mata ’yan Saudiyya suka samu, waɗanda suka zaburar da ni na fahimci wani abu game da marasa lafiya, na taimake su, suka yi mini fatan alkhairi.

“Na nuna musu cewa zan iya yin aikina alhali ina sanye da Hijabi,” a cewar al-Harbi.

A da iyaye a Saudiyya ba sa son ’ya’yansu mata su yi karatun kula da lafiyar majinyata, musamman saboda cuɗanya da maza. Amma a halin yanzu an shawo kansu sun gane muhimmiyar buƙatar da ake da ita a tsakanin Musulmi. Mu ma a nan wani malami Sheikh Abdallah Gadon Ƙaya ya taƃa nuni da munin aikin, bisa wani rahoto da aka taƃa kawo masa, amma duk duk da haka sai da ƙungiyar likitoci ta sa ya janye kalamansa.

Farfesa Ruƙayya Ahmad Rufa’i, tsohuwar Ministar Ilimi a Najeriya

A wata maƙalar mai taken Mata Sun Koka da Direbobin Tasi: Wasu na ɗaukar lambobin wayarsu don su aike musu da saƙonnin Whatsapp na soyayya ko neman ƙulla abota da dai makamantansu. Ɗaukacin irin waɗannan matsaloli matanmu, musamman waɗanda ke gidan aure na cin karo da su. Saboda haka sai a yi taka-tsan-tsan.

Ƙarƙarewa:
Haƙiƙa mun fahimci ƙalubalen zamani, tun daga zamanin mulkin mallaka zuwa yau, tattare da buƙatar da ake da ita ta mata ƙwararru a fannonin inganta rayuwar al’umma, musamman kula da lafiya da ilimantar da yara ƙanana, kai har manyan ma. Duk da haka akwai buƙatar mata su ɗamfaru da tunani ko su ƙudurce a zuciya manufarsu ta addini da kyautata mu’amala a tsakaninsu da abokan zamansu. Uwa-uba, waɗannan dabaru da Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa ya bijiro da su, na ɗaukar matakin kula da mata a daina ɗora musu nauyin da ya kamata a ce, magidanci ya ɗauka. Sannan hukuma ta yi dokar kare mutuncin mata, tare da ɗaukar nauyin marayu da zawarawa, musamman matan da mazajensu suka rasu.

Muhimmin al’amari dai, na san mata za su ga cewa tamkar an fi damuwa da halin da suke ciki ko suka tsinci kansu fiye da abokan zamansu maza. Tabbas haka lamarin yake, domin mace ita ce uwar al’umma, kuma addini ya siffanta ko kwatanta ta da gona. Kun ga ke nan idan ta bayar da yabanya mai kyau, ko tantama babu sanadiyyar ban ruwan da zubin takin tarbiya ne da iyaye suka sha gumun gudanarwa, har kuma aka samu maigida nagari wanda ya ɗora daga inda iyaye suka tsaya. To ita ma uwa, uwargida ko amarya wajibi ne ta zage damtse wajen yin raino da bai wa ’ya’yan da ta haifa, har ma da waɗanda ba nata ba (’ya’yan al’umma, waɗanda suka haɗa da na maƙwabta ko waɗanda ta ci karo da su a wajen sana’arta, musamman malaman makaranta da masu kula da marasa lafiya) tarbiyyar ladabi da biyayya don amfanin al’umma.

Farfesa Suwaiba Ahmad, Ministar Ilimi (Ƙaramar) ta Najeriya

Zage damtse uwa ya zama dole, musamman kan al’amuran da suka jiƃinci kula da gida, wajen tarbiyyar iyali. Domin mata su san cewa, mu nan ƃangaren na ƙasar Hausa da kewayenta, da zarar ɗa/ko ’ya sun yi wata tarƃargaza, har suka jawo wa kansu tir da Allah tsine, sai ku ji an ce, WANE KO WANCE ƊAN/’YAR KUKA NE; ɗan kuka mai jawo wa uwarsa zagi (ko jifa). Saboda haka mun haƙaƙƙe cewa, “kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.” Da wannan ake ganin ƙoƙarin tarbiyyar iyaye, musamman uwa, za ta daƙile haihuwa da rainon ‘yan daba ko ‘yan sara-suka da dai ɗaukacin bara-gurbi a cikin al’umma.

Shawarwari:
Aiwatar da managartan dabarun kyautata rayuwa, waɗanda ba su ci karo da addini da al’ada ba. Don haka yana da matuƙar muhimmanci a cikin wannan yanayi da muka smau kanmu a ciki. Juyin zamani sai a yi taka-tsan-tsan a wajen fafutikar neman ilimi da aikin ƙwadago, tare da inganta dabarun tarairayar raino da tarbiyyar ’ya’ya.

Ya ke ’yar uwa, idan Allah ya ƙaddara kin zama matar masu faɗa a ji, musamman mahukunta masu jagorancin al’umma, kai ko matar Alhaji wane, wani hamshaƙin attajiri, wajibi ne ki yi ƙoƙarin ganin an kyautata yanayin da zai bai wa mata halin yi wa ’ya’ya tarbiyya tagari, musamman ma muhimmai daga nau’ukan shawarwarin da aka zaƙulo daga cikin maƙalar rubutun Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa, har aka gabatar muku da su a wannan bagire.

Ƙarshe dai zan ƙarƙare maƙalata da ’yan baitukan Marigayi Malam Sa’adu Zungur, wato Arewa Mulukiyya Ko Jamhuriya, inda ya rera kamar haka:

“Shehu Laminu da Shehu Mujadaddi,
Sun bar mana gadon gaskiya.

A Landan ko a Arebiya,
Mu dai ilimi muka tambaya.”

Waɗannan baituka hujja ne, cewa “kar mu sake mu mance, mu bi al’adunmu na gargajiya,” a cewar Alhaji Musa Ɗanƙwairo. Kun ga waɗanda suke ganin bai kamata a ɗauki fatawowin magabata ba, to sun yi kuskure, domin Hadisin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu (SAW) ya nusar da mu cewa: Ku ji tsoron hasashen mumini.” Saboda haka ko da muna jin cewa, magabata ba su riski wannan zamanin ba, lallai mu sani fatawowinsu za su yi mana amfani. Abin da kawai za mu yi shi ne, mu duba mahangar aiwatar da su a aikace, yadda za su hau doron gadon bayan tafiyar zamani. Yin hakan zai ba mu damar tsira a duniya da lahira.

Allah Ya yi mana dace da muwafaƙa.
_______________________

Wannan maƙalar ta Malam Abubakar Dodo, ya gabatar da ita a gaban taron mata masu niyyar yin aure, cikin watan Satumbar 2024; a taron da aka gudanar a Kwalejin Kimiyya da Fasahar Nau’urorin Ƙere-ƙeren Kula da Lafiya ta Aminu Dabo da ke Civic Centre, Kano

Previous Post

Na Zaune Bai Ga Gari Ba

Next Post

Generals Adeosun, Mukokomani Clinch 2024 TY Buratai Excellence Award in Military Leadership

Related Posts

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

January 13, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (7)

January 9, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)

January 6, 2026
Next Post
Generals Adeosun, Mukokomani Clinch 2024 TY Buratai Excellence Award in Military Leadership

Generals Adeosun, Mukokomani Clinch 2024 TY Buratai Excellence Award in Military Leadership

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

BATUN SULHU DA ‘YAN TA’ADDA A JIHAR KATSINA: Abin Da Ya Kamata A Fahimta

BATUN SULHU DA ‘YAN TA’ADDA A JIHAR KATSINA: Abin Da Ya Kamata A Fahimta

September 19, 2023
Yadda Ƙungiyar NAL Ta Karrama Dokta Bukar Usman A Legas

Yadda Ƙungiyar NAL Ta Karrama Dokta Bukar Usman A Legas

August 18, 2024
A Review of Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria

Sharhin Littafin Boko Haram Da Sauran Ƙalubalen Tsaro A Najeriya (Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria)

May 9, 2024

Ɗan Kasuwa Ya Koka Da Rusau A Kano

June 25, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.