BELLO GALADANCHI: Burina In Ƙwato Wa Talakawa ‘Yanci Daga Azzaluman Shugabanni
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
~~~~~~~
Marubuci ne, wanda ya zuwa yanzu ya wallafa littattafan Hausa guda 11. Shi ɗan jarida ne kuma mai shirya finafinai, manya da ƙanana. Shi marubucin waƙoƙi ne. Shi malamin makaranta ne, kamar kuma yadda yake babban ɗan kasuwa. Taskar Gizago ta samu tattaunawa da zaƙaƙurin ma’abucin fasaha – Malam Bello Habib Galadanchi.
~~~~~~~

TG: Kana ɗaya daga cikin marubutan Hausa a wanann zamani. Ko za ka gaya mana tarihinka a taƙaice?
BELLO: Sunana Bello Habeeb Galadanchi. An haife ni a wani ɗan ƙaramin gari da ake kira State College, a Jihar Pennsylvania da ke Amurka. Na yi makaranta a Ulul Albab Katsina, sannan na yi digiri a Jami’ar Penn State University. Daga nan na yi aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka. Daga nan na zo China na yi digiri na biyu (Masters) a Ilimin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration). Na yi digirin-digirgir (PhD) a Harkar Ilimi (Comparative Education).
Daga nan na yi aiki a BBC Hausa, sannan yanzu ina koyarwa a wata makarantar firamare da ke birnin Beijing, China kuma ni ne shugaban malamai ‘yan ƙasashen waje da ke aiki a makarantar.
TG: Tun yaushe ka fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinka ga harkar rubuce-rubuce?
BELLO: Na fara rubutu tun ina JSS 3, a shekarar 2001 ke nan, lokacin da na rubuta wani ɗan ƙaramin littafi. Tun daga nan na fara rubuta waƙoƙi (Poetry), sannan da na shiga jami’a, na fara rubuta ƙananan finafinai daga nan har ci gaba da rubuta dogaye.
Bayan na fara aiki a VOA Hausa, a nan na ƙara kwyarewa wajen harshen Hausa. Shi ne na fara rubutun adabin Hausa a shekarar 2014 da littafin Labarin Ahmad da Aisha.
TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa ka rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa ka buga a intanet?
BELLO: Na rubuta na Hausa guda goma sha ɗaya, kuma duka a shafukan zumunta na buga su saboda yanzu ai waya ita ce littafin mutum. Wannan zai sawwaƙe wa mutane fitar da kuɗi ga sayen littafi, tun da dai har sun sayi data.
TG: Waɗanne irin matsaloli kake fuskanta a matsayinka na marubuci?
BELLO: Rashin lokaci shi ne babban ƙalubale saboda a kusan koyaushe ina da abubuwa da yawa da nake yi, musamman na neman kuɗi, wanda hakan kuma yakan ɗauki lokaci ko ya gajiyar da mutum.
TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori ka samu ko kuma akasin su?
BELLO: Ma sha Allah! Babbar nasarar ai ita ce ƙara iya ƙago labarai da amafani da harshen Hausa ta hanyoyi da dama. Musamman rubuce-rubucen da na yi a shekarun baya. Ma sha Allah, sanadiyyar su na ci na ɗaya da na biyu a gasar fim a ƙasashe daban daban-daban, sannan na samu tallafin karatu da ya sa har na kawo inda nake yanzu.
Sannan kuma nakan ji daɗi, idan na haɗu da masoya waɗanda suka ji daɗin labaraina, har za ka ga suna ambato wasu abubuwan daga ciki.
TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenka, da kake koyi da rubutunsu?
BELLO: Ina jin daɗin rubuce-rubucen Bashir Yahuza Malumfashi da Gimba Kakanda da Ibrahim Abubakar.
TG: Ya zuwa yanzu wane sabon littafi kake kan rubutawa kuma zuwa yaushe zai fita ga al’umma?
BELLO: Ina rubuta labarin ƊAN FILINGE DA BABANSA BASAMUDE amma ban yi nisa ba kuma na jinginar. In sha Allah, zan zo kansa nan ba da jimawa ba.
TG: Ga shi kana shirya gajerun finafinan bidiyo. Ta yaya ka faro kuma me ya ba ka sha’awar yin haka? Yaya batun shirya babban fim a nan gaba?
BELLO: Babu shakka, na fara tun a shekarar 2009, lokacin da wani ɗalibi da nake kula da shi ya koya mank yadda ake sarrafa da kyamara. Abun ya matuƙar ba ni sha’awa. Tun lokacin na ce in sha Allah, har ƙarshen rayuwata zan riƙa shirya fim. To na yi ƙoƙari na koya kuma abin ya ɗauki lokaci matuƙa amma godiya ta tabbata ga Allah da Ya sa a farkon wannan shekarar, sai jama’a suka fara son bidiyoyin.
Ina da finafinai da nake so na yi a Arewa amma sai in sha Allah na koma Najeriya da zama.
TG: Mene ne babban burinka dangane da rubutu?
BELLO: Babban burina shi ne, in yi rubutun da zai taimaka wajen ƙwato wa ‘yan Najeriya ‘yancinsu daga wajen mugayen shugabanni da suka shashantar da komai a ƙasar. Da fatan ni ma zan taka rawar da wata rana mutanenmu za su daina zama da yunwa da rashin aikin yi, da rashin ilimi.
TG: Ko kana da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanka da kuma al’umma masu karanta littattafanka?
BELLO: Allah Ya shirya mana gwamnatinmu, su kuma al’ umma, sai mun tashi a tsaye domin gyara kanmu da al’ ummarmu kafin komai ya gyaru.
Ga marubuta kuma, ina kira da su ci cegaba da aikin alherin da suke yi.
~~~~~~~













