• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, May 30, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

Tarihin Ƙungiyar Hamas

Umar Labdo Muhammad by Umar Labdo Muhammad
October 13, 2023
in Addini
0
Tarihin Ƙungiyar Hamas

Dakarun Ƙungiyar Hamas

36
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Tarihin Ƙungiyar Hamas

Daga Umar Labdo Muhammad

Related posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026

~~~~~~~
Ƙungiyar Hamas ta samo asali daga Ƙungiyar Ikhwanul Muslimun ta ƙasar Masar.

A shekara ta 1935, Ƙungiyar Ikhwan ƙarƙashin jagorancin Hassan Albanna ta fara gudanar da tuntuɓa a yankin Falasɗinu da nufin kafa reshenta a yankin.

Bayan tattaunawa da matasa da ɗalibai, wanda ya ɗauki shekaru, an kafa reshen ƙungiyar na farko a shekarar 1945 a birnin Ƙudus. Kuma a ranar 25 ga watan Nuwamba, 1956 an buɗe babban ofishin ƙungiyar a birnin Gazza.

Bayan sama da shekaru 60 tana gudanar da ayyukanta, a matsayin reshe na yKungiyar Ikhwan da cibiyarta take a ƙasar Masar, Ƙungiyar Hamas ta yi shelar tsinke alaƙarta da Ikhwan a shekara ta 2017, don ta samu damar ci gaba da aikinta na jihadi da cikakken ‘yanci.

Ana ɗaukar Sheikh Ahmad Yasin a matsayin wanda ya assasa Ƙungiyar Hamas. Daga cikin sanannun shugabanninta akwai Khalid Mish’al, wanda ya daɗe yana jagorantar ɓangaren ƙungiyar na siyasa da Yahya Sinwar da Abdul Aziz Rantisi da Isma’il Haniyya.

Ƙungiyar Hamas tana da ɓangarori biyu: ɓangaren siyasa, wanda yake shiga zaɓe a Majalisar ƙasa ta Falasɗinu da ɓangaren soji, da suke kira da sunan Bataliyar Izzuddeen Alƙassam, wanda sunan wani dakare ne da ya fara ƙaddamar da gwagwarmaya da makami a kan Daular Bani Yahudu, tun farkon kafa ta. Wannan sashe na Hamas, shi ke ƙaddamar da aikin jihadi a kan ƙasar Isra’ila, ciki har da yaƙin da ake ciki yanzu, wanda aka yi wa laƙabi da Ambaliyar Aƙsa.

Ɓangaren Hamas na siyasa yana tafiyar da al’amuransa a bayyane, saɓanin Bataliyar Izzuddeen Alƙassam, wacce take tafiyar da ayyukanta a sirri.

A yau shi ke mulkin Zirin Gaza kuma yana cikin siyasar Daular Falasdyinu mai ƙwaryaƙwaryan cin gashin kai. Yana cikin wannan siyasa tsundum kuma a Majalisar Ƙasar Falasɗinu, shi ya fi kowace ƙungiya da jam’iyya yawan wakilai, ciki har da Ƙungiyar Fatah ta Shugaba Mahmoud Abbas.

Babu taƙamaimai dangane da adadin mayaƙan Hamas amma majiyoyi da yawa suna nuni da cewa ƙungiyar tana da zaratan mayaƙa kimanin 15,000, ban da wasu daban da ake iya kira su ɗauki makami idan buƙata ta gilma.

Hamas ta mallaki makamai nau’i dabam-daban, musamman rokoki masu cin zango mai nisa da matsakaici da manyan bindigogi da ƙananan jirage da ake sarrafawa daga nesa da kuma abin da ta ba Isra’ila mamaki da shi a wannan yaƙin, watau baburan sama masu ɗaukar mayaƙa kuma su yi wa na’ura mai hangen jiragen sama (radar) layar zana.

Babbar manufar Ƙungiyar Hamas ita ce ‘yanta kafatanin ƙasar Falasɗinu da fito-na-fito da manufar Sahyuniyya ta ƙwace ƙasa da kore Falasɗinawa daga ƙasarsu ta gado.

Kamar yadda mai karatu zai yi zato, wasu manyan ƙasashen duniya suna ɗaukar Hamas a matsayin ƙungiyar ta’addanci. Waɗannan ƙasashe sun haɗa da babbar algunguma, ƙasar Amurka da Burtaniya da Tarayyar Kasashen Turar da Japan da Usturaliya, da sauransu.
~~~~~~~

Previous Post

PROMOTION GALORE: PSC Promotes 5718 Senior Police Officers

Next Post

A REVIEW: Nigeria @ 63 Independence Day Anniversary Celebration

Related Posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
Addini

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba
Addini

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Mu Ji Tsoron Allah
Addini

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
Next Post
A REVIEW: Nigeria @ 63 Independence Day Anniversary Celebration

A REVIEW: Nigeria @ 63 Independence Day Anniversary Celebration

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

UEFA 2025: WACE ƘUNGIYA CE ZA TA ƊAUKI KOFIN ZAKARU?

UEFA 2025: WACE ƘUNGIYA CE ZA TA ƊAUKI KOFIN ZAKARU?

April 28, 2025
TAURARON GIZAGAWA: NURA ADAMU AHMED

TAURARON GIZAGAWA: NURA ADAMU AHMED

August 3, 2023
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025
Attajiran Arewa Ku Zuba Jari A Arewa

Attajiran Arewa Ku Zuba Jari A Arewa

June 8, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.