• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, May 30, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Eriya Malumfashi

Mu Kama Sunna Mu Kauce Wa Bidi'a by

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 16, 2023
in Addini
6
Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Eriya Malumfashi
26
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

A yau Juma’a, 27-11-1444 (Hijriyya), 16-06-2023 (Miladiyya), a yayin Sallar Jumu’a a Masallacin Eriya Malumfashi, wacce Liman Malam Mustapha Tahir ya jagoranta, ya gabatar da huɗuba game da muhimmancin Sunna da illar Bidi’a.

Related posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026

Liman ya fara da bayyana ma’anar Sunna a Addinin Musulunci, cewa ita ce duk wani aiki da Manzon Allah (saw) ya aikata ko ya yi umurni da a aikata ko kuma ya gani ana aikatawa amma bai hana ba.

Sannan kuma ya bayyana ma’anar Bidi’a da cewa ita ce wani aiki da Manzon Allah bai yi ba, bai ba da umarni a aikata ba, kuma bai gani ana aikatawa amma ya ƙyale ba.

Malam ya kwaɗaitar da al’umma da su riƙe Sunna ƙamkam, domin kuwa Addinin Allah ya cika, Manzon Allah (saw) ya isar da saƙo dukkansa, bai rage komai ba. Musulunci ya tanadar da tsarin yadda mutum zai yi bauta da yadda zai yi rayuwa. Yadda mutum zai Salla, Azumi, Zakka, Hajji da kuma yadda zai inganta riƙo da Tauhidi, duk an tanadar. Haka kuma daidai da yadda mutum zai yi kashi da fitsari ko yadda zai saka sutura, da yadda zai yi rayuwa dukkanta, Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar. Saura mutum ya tashi ya nemi ilimi kawai.

Malam ya ce duk wanda ya yi riƙo da wata Sunna kuma wani ya yi koyi da shi, to zai tabbata cikin ladar har zuwa tashin ƙiyama. Haka kuma duk wanda ya riƙi Bidi’a har wani ya yi koyi da shi, to zai tabbata cikin girbar zunubi har zuwa ranar tashin ƙiyama, kuma a haɗa masa da kamashon zunubin wanda ya yi koyin da shi.

Malam ya kafa hujja da Hadisin Nana A’isha (ra), cewa duk wanda ya haddasa wani aiki da ba umurnin Allah da ManzonSa ba, to an mayar masa. Don haka ya jaddada cewa, lallai Sunna dukkanta alheri ce, sai mu aikata ta. Sannan dukkan Bidi’a dukkanta sharri ce, sai mu guje mata.

Haka kuma Malam ya ja hankalin al’umma da cewa, Manzon Allah (saw) ya ce a lokacin da al’umma suka lalace, to duk wanda ya riƙi Sunna, yana da wata lada ta musamman.

Ya sanar da mu cewa babu shakka Ajanna gaskiya ce. Allah Ya tanade ta ga bayinSa na ƙwarai masu aikata aikin alheri kuma Ya kwaɗaitar da a neme ta ta aikin ƙwarai. Haka kuma Wuta gaskiya ce, Allah Ya tanade ta domin kangararru, don haka mu guje ta. “Wanda duk ya aikata kyakkyawan aiki daidai da ƙwayar zarra, zai gani. Haka kuma wanda duk ya aikata mummuna, daidai da ƙwayar zarra, zai gani.”

Allah Ka yi mana jagora a rayuwa, Ka tabbatar da mu cikin Musulunci, Ka sa mu cika da imani, idan lokacin mutuwarmu ya zo. Amin!

Previous Post

Tinubu Ya Ba Nuhu Ribadu Muƙami

Next Post

Da Sun Ce Tsohon Nan Auduga Ne

Related Posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
Addini

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba
Addini

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Mu Ji Tsoron Allah
Addini

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
Next Post
Da Sun Ce Tsohon Nan Auduga Ne

Da Sun Ce Tsohon Nan Auduga Ne

Comments 6

  1. Daga usman muhammad bam says:
    3 years ago

    Allah ya sakada alkhairi dan malumfashi BASHIR YAHUZA

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Amin Amin Ya Allah. Ni ma na gode kwarai.

      Reply
      • Ahmad A. Umar says:
        3 years ago

        Masha Allah. Allah Ya sa ka da alheri. Mu na godiya da wannan tunatarwa.

        Reply
        • Bashir Yahuza Malumfashi says:
          3 years ago

          Ma sha Allah.

          Reply
        • Bashir Yahuza Malumfashi says:
          3 years ago

          Madalla. Mu ma mun gode.

          Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Amin Malam.

      Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Dokta Bukar Usman, Sarkin Daura Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya

Dokta Bukar Usman, Sarkin Daura Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya

September 2, 2025
Kar Nake Ganin Ka

Kar Nake Ganin Ka

May 29, 2023
Ambaliya Ce Babbar Ƙalubalen Manoman Jigawa – Isa Billami

Ambaliya Ce Babbar Ƙalubalen Manoman Jigawa – Isa Billami

June 12, 2023
Ɗan Iyan Galadiman Katsina Emerges Chairman of Arewa Consultative Forum

Ɗan Iyan Galadima Ya Zama Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa Ta Arewa

June 19, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.