• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, March 5, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sinadarin Rayuwa

Kishin Ƙasa Ne Tubalin Farko Na Gina Rayuwar Al’umma (1)

webmaster by webmaster
May 29, 2023
in Sinadarin Rayuwa
0
Kishin Ƙasa Ne Tubalin Farko Na Gina Rayuwar Al’umma (1)
15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Kamar yadda aka tanadar da shafin Sinadarin Rayuwa, zai riƙa kawo nazarce-nazarce da za su riƙa sassaita tunaninmu da kaifafa ƙudurorinmu da yi mana jagora wajen fuskantar rayuwa, ta yadda za mu gudu tare kuma mu tsira tare. Bayan haka, maudu’inmu na yau zai yi mana tambihi ne game da kishin ƙasa da kuma muhimmancinsa ga al’umma.

Shin ko mun lura da cewa a duk ranar ɗaya ga watan Oktoba na kowace shekara, ana gudanar da bukukuwan taya murna ga ƙasarmu Najeriya bisa samun mulkin kai? Dangane da haka, a matsayinmu na ’yan ƙasa, ya dace mu gane muhimmanci da tasirin kishin ƙasa da kuma dangantakar da ke tsakanin ƙasar tamu da kuma mu kanmu.

Related posts

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

November 30, 2025
Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

November 24, 2025

Abu na farko da ya kamata kowane ɗan ƙasa ya gane shi ne, ƙasarka ita ce alƙiblar rayuwarka. Abin nufi a nan shi ne, duk dai inda kake zaune, a cikin ƙasar nan kake. Ya Allah kana cikin ƙauye ne ko a birni, kai ɗan ƙasa ne, domin kuwa kana zaune ne a unguwarku, wacce ke a ƙarƙashin ƙaramar hukuma, a ƙarƙashin jiharku; waɗanda su kuma suke a cikin Najeriya.

Kasancewar ba ka da wata ƙasa da ta kai ƙasarku, lallai ne ka maida hankali wajen nuna kishinta da kare martabarta, domin kuwa idan ta kasance mai muhibba da martaba, to kai ne ka zama mai martaba da muhibba. Idan kuma ta zama ballagaza, marar ƙima a idanun duniya, to ka sani kai ma haka kake.

Domin ganin ka zama mutum nagari, mai ƙima da martaba, sai ka tashi tsaye, ka yi ƙoƙari iya yin ka, wajen bunƙasa ƙasarka. Dalili na farko ke nan da ya sanya za ka zama mai kishin ƙasa. Amma idan zan ƙara yin wata tambayar kuma, ta yaya za ka zama mai kishin ƙasa? Ta yaya kishin ƙasarka zai amfane ka, ya amfani al’ummar ƙasarka da kuma ita kanta ƙasar?

Yana daga cikin kishin ƙasa, ka kasance mai gaskiya da amana a cikin al’amuranka. Idan ka kasance mai faɗar gaskiya kuma kana aiwatar da al’amuranka cikin gaskiya; sannan kuma ka kasance mai riƙon amana wajen mu’amalarka da mutane, to kuwa ƙasarka za ta zama mai gaskiya da amana, abar ƙauna ga al’ummar duniya. Dalili shi ne, a matsayinka na ɗan ƙasa, ka zama jakadanta mai gaskiya da amana. Idan kai ka zama haka, wancan shi ma ya zama haka, ita ma waccan ta zama haka; shi ke nan an samu abin da ake so. Ƙasarmu za ta cika da masu gaskiya da amana ke nan, wanda haka zai sanya ta zama amintatta kuma mai aminci a cikin ƙawayenta na sassan duniya.

Kishin ƙasa ne ga ɗan ƙasa ya kasance mai neman na kansa, wato kada ya kasance mai zaman banza, wanda ba ya aiki ko sana’ar komai. Da zarar ɗan ƙasa ya zauna durshan ba tare da yana wata harka ba, babu wanda zai zame masa aboki sai Shaiɗan. Wannan zaman banza zai bijiro masa da tunane-tunane marasa kyau, sannan su ingiza shi zuwa aikata munanan ayyuka, waɗanda za su kasance halaka a gare shi kuma waɗanda za su cutar da sauran al’umma. Daga nan kuma sai al’amarin ya shafi ƙasarsa, domin kuwa sunanta zai ɓaci ta hanyar munanan ayyukansa.

Don haka, ya dace mutum ya miƙe tsaye ya sama wa kansa abin yi. Kada mutum ya ce zai zauna sai ya samu wani babban aiki ko babbar sana’a. Koda ka gama jami’a ne, idan ba ka samu aiki ba, yi ƙoƙari ka fara koda aikin ƙarfi ne na ƙwadago. Ɗan abin da za ka samu, zai iya zama mai albarka kuma ka biya buƙatarka da shi. Kada ka yi mamaki, ta hanyar wannan yunƙuri da ka yi na aikin ƙarfi, Allah na iya haɗa ka da wata sila, wacce za ka iya samun aikin da ya fi shi.

Haka kuma, za ka iya fara kasuwanci koda da ƙaramin jari ne. Misali, za ka iya fara sayar da katin waya. Sannu a hankali, daga ’yar ribar da za ka riƙa samu, madamar kana adanawa da kaɗan-kaɗan; jarinka yana iya zama mai girma. Idan dai har ka riƙa gudanar da harkarka cikin gaskiya da tsare haƙƙin jama’a, kasuwancin naka yana iya zama mai albarka. Domin kuwa, akwai mutane da yawa da suka fara kasuwanci da ƙanƙanen jari kuma suka bunƙasa har suka zama hamshaƙan ’yan kasuwa.

Ala-ayyi-halin dai, zaman kashe wando, ko zaman jiran mai yawan da ko alamarsa babu, alhali babu tabbas, ba abin dogaro ba ne. Don haka, kishin ƙasa ne ga mutum ya hana kansa zaman kashe wando, ya cire girman kai daga zuciyarsa, ya yunƙura domin neman na halal komai kanƙantarsa.

Previous Post

Soyayya: Yadda Wata Budurwa Ta Samu Mijin Kirki

Next Post

Kar Nake Ganin Ka

Related Posts

Kada Ka Karaya Da Rayuwa
Sinadarin Rayuwa

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

November 30, 2025
Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara
Sinadarin Rayuwa

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

November 24, 2025
A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne
Sinadarin Rayuwa

A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne

November 11, 2025
Next Post
Kar Nake Ganin Ka

Kar Nake Ganin Ka

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

SASSANYAN AMINCI (5)

SASSANYAN AMINCI (5)

September 12, 2025
Dogo Na Magayaƙin Kano Ya Angwance

Dogo Na Magayaƙin Kano Ya Angwance

July 16, 2023
Marubuta Bakwai Mafi Tsufa A Duniya Da Har Yanzu Suke Rubutu

Marubuta Bakwai Mafi Tsufa A Duniya Da Har Yanzu Suke Rubutu

February 17, 2026
I was a security guard – Tinubu addresses Nigerians in India

I was a security guard – Tinubu addresses Nigerians in India

September 8, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)
  • RAMADAN KARIM: 16-1447
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (7)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 16-1447

Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)

March 5, 2026
RAMADAN KARIM: 16-1447

RAMADAN KARIM: 16-1447

March 5, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.