Nasiharmu Ta Yau (55)
Malam Ka Dogara Ga Allah Kawai…
__________
A yau, nasiharmu ta fito ne daga Abdul’aziz Abdul’aziz, Sardaunan Matasan Malumfashi, wanda ya ce:
Kai Malam, ya kamata ka sani, mutane za su yi nasara, ko kana son su ko ba ka son su. Amincewarka ba ita ce sharaɗin nasarar wani ba. Ka tuna, Allah ba ya buƙatar izininka kafin ya azurta wanda ya so.
Abin da Allah ya ƙaddara wa mutum, zai same shi a lokacin da Allah ya tsara, ko ka yi farin ciki da hakan ko ba ka yi ba.
Lokaci shi ne babban alƙali. Yana bayyana gaskiya, yana fallasa ƙarya kuma yana tabbatar da abin da Allah ya ƙaddara.
__________













