• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, November 7, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Adabi, Tsaron Ƙasa Da Matsayin Najeriya A Duniya

JAWABIN SHUGABAN TARO

Bukar Usman, OON by Bukar Usman, OON
November 6, 2026
in Adabi
0
Adabi, Tsaron Ƙasa Da Matsayin Najeriya A Duniya

Dakta Bukat Usman, OON, jim kaɗan bayan kammala jawabinsa a wurin taro

6
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Adabi, Tsaron Ƙasa Da Matsayin Najeriya A Duniya

Daga Bukar Usman, OON

Related posts

Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa

Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa

November 1, 2026
Fatima Gana: Marubuciya Mai Alƙalami Biyu

Fatima Gana: Marubuciya Mai Alƙalami Biyu

September 25, 2026
Dakta Bukat Usman, OON, jim kaɗan bayan kammala jawabinsa a wurin taro

 

__________

Wannan jawabi ne da Dr. Bukar Usman ya gabatar a matsayinsa na Shugaban Taron Ƙasa da Ƙasa na 45 na Ƙungiyar Marubuta ta Najeriya (Association of Nigerian Authors – ANA), wanda aka gudanar a Cibiyar Marubuta ta Mamman Vatsa (Mamman Vatsa Writers’ Village), Mpape, Abuja, a ranar 27 ga Oktoba, 2026.

__________

Gabatarwa:

Abin alfahari ne da kuma farin ciki a gare ni, kasancewa wanda zai jagoranci wannan gagarumin taro da ya haɗa fitattun marubuta, masana ilimi da malamai.

Idan muka yi la’akari da muhimman ɓangarori biyu da suka ƙunshi taken wannan taro, zan iya cewa tun da farko, dangane da fannin adabi, matsayin Najeriya a duniya yana da gaurayen sakamako. Wato tana da nasarori da kuma gazawa, musamman idan aka dubi adabi ta fuskar ilimin boko.

A ɓangaren nasarori, Najeriya ta kasance kan gaba wajen kafa ƙungiyoyin marubutan adabi na bai ɗaya da suka haɗa nahiyar Afirka. Abubuwan da suka cancanci ambato sun haɗa da jerin littattafan Heinemann African Writers Series na shekarun 1960; Ƙungiyar Marubutan Al’ummar Afirka (The Union of Writers of the African People – UWAP), wadda aka kafa a ƙasar Senegal a shekarar 1975; sai kuma Ƙungiyar Marubutan Pan-African (Pan-African Writers Association – PAWA), wadda aka kafa a Ghana a shekarar 1989. Fitaccen marubuci ɗan Najeriya, Dr. Wale Okediran, shi ne Babban Sakataren PAWA na yanzu. Haka kuma, akwai wasu fitattun ’yan Najeriya da suka yi fice a fagen adabi ta fuskar ilimin boko.

A ɓangaren gazawa kuwa, akwai ƙarancin yaɗuwar ilimin boko a ƙasar baki ɗaya. Idan aka kwatanta Najeriya da sauran ƙasashen duniya dangane da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, za a ga cewa akwai abubuwa da dama da ya kamata a gyara.

Dangane da ilimin ajami, kaso mai yawa na al’ummar wannan ƙasa sun samu ilimin farko ne ta harshen Larabci, tun kafin zuwan ilimin rubutun boko. Akwai fitattun mutane da suka yi fice a wannan fanni, waɗanda za su iya gogayya da takwarorinsu a sauran sassan duniya.

Wani nau’in adabi kuma shi ne adabin baka, wanda shi ne tushen ilimi a al’ummomin Afirka na gargajiya. Muhimmancinsa ya sa aka samar da kalmar “Orature” a wannan zamani, domin bayyana nazarin adabin da ake isarwa ta hanyar magana.

Tabbas, Najeriya, wadda ita ce ƙasa mafi yawan baƙaƙen fata a duniya kuma mai ɗimbin bambance-bambancen al’adu, tana da tarin al’adu na gargajiya, waɗanda aka fitar da wasu daga cikinsu zuwa ƙasashen waje a zamanin cinikin bayi. An kuma adana abubuwa da dama daga cikin waɗannan al’adu a cikin rubuce-rubucen adabi, waɗanda suka cancanci a kiyaye su da bunƙasa su cikin alfahari. Abin da ake buƙata shi ne, amfani da fasahar zamani ta intanet da sauran sabbin hanyoyin fasaha wajen cin ma wannan buri cikin inganci da armashi.

A ƙasa, zan tattauna muhimman batutuwan da na fahimta cewa taken wannan taro ya ƙunsa, ɗaya bayan ɗaya.

Adabi:

A lokacin da nake ɗalibi, na yi karatun adabi a matsayin ɗaya daga cikin darussan da na ɗauka. Tsarin karatun ya ƙunshi karanta littattafan shahararrun marubuta, galibinsu daga Birtaniya, a fannoni kamar nahawu, waƙa, tarihi, falsafa, rubuce-rubucen tafiye-tafiye da wasan kwaikwayo. Wannan kuwa ya kasance a lokacin mulkin mallaka da kuma farkon shekarun bayan samun ’yancin kai.

Marubutan littattafan sun haɗa da William Shakespeare, Jane Austen, Samuel Taylor Coleridge, Geoffrey Chaucer da Charles Dickens da sauransu. Ana kuma shirya wasan kwaikwayo domin bayyana wasu daga cikin jigogin littattafan da kuma ƙara fito da saƙonninsu fili.

Daga bisani, kishin ƙasa da sha’awar adabi da suka bunƙasa bayan samun ’yancin kai, sun farkar da tunanin ’yan Najeriya da sauran ’yan Afirka, suka fara rubuce-rubuce da himma bisa fahimtarsu da irin abubuwan da suke fuskanta, tare da shigar da ayyukansu cikin tsarin manhajar makarantu.

Saboda haka, ɗaliban da suka fara karatu daga shekarun 1970 zuwa gaba sun samu damar karanta littattafan marubutan Najeriya da sauran ƙasashen Afirka. Abin lura a nan shi ne, tun daga matakin firamare har zuwa jami’a (1951–1969), ban samu damar karanta wani littafi da marubucin Najeriya ko wani ɗan Afirka ya rubuta ba, sai dai littattafan Hausa na Abubakar Imam.

Daga baya kuma sai aka ƙara samun wani sabon ɓangare na adabi, wato adabin baka. Ana ganin cewa adabin baka ya riga rubutaccen adabin da na karanta. Wannan ne ya haifar da ƙirƙiro kalmar “Orature” a fannin nazarin adabi, musamman wajen nazarin tatsuniyoyi, labaran gargajiya da sauran hikimomin da ake isarwa ta baki daga tsara zuwa tsara, musamman a nahiyar Afirka.

Kafin zuwan ilimin boko, al’adun baka su ne hanyoyin da kakanninmu suke amfani da su wajen isar da hikima da ilimi a cikin al’umma, ba tare da tsarin karatun makaranta ba. Haka kuma, wannan hanya ce ta tarbiyyar yaro tun yana ƙarami, ta hanyar koya masa ƙimomin zamantakewa da ya kamata ya riƙe har ya girma.

Idan aka yi la’akari da duk waɗannan bayanai, fahimtata mai sauƙi game da adabi ita ce, ya ƙunshi tattara da adana tarihin ƙoƙarin ɗan Adam da abubuwan da ya fuskanta tun a da can har zuwa yanzu, ta hanyar rubutu ko baka, duk da cewa a yau rubutaccen adabi ya fi adabin baka yaɗuwa.

Tsaron Ƙasa:

Batun tsaro yana da matuƙar muhimmanci a gare ni, domin ya kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da na mayar da hankali a kansu a tsawon shekarun da na yi ina aiki a ma’aikatar gwamnati ta wannan ƙasa.

Ɗaya daga cikin muhimman ɓangarorin tsaro, shi ne kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasa daga barazanar cikin gida da ta waje. Haka kuma, tsaro ya ƙunshi samar da walwala da jin daɗin al’umma. Wani ɓangaren kuma shi ne kare gwamnatin da ke kan mulki daga ayyukan da za su iya kawo mata cikas ko kifar da ita, tare da kare ƙasar kanta daga barazanar waje da za ta iya tauye cikakken ikon mallakarta da iyakokinta.

Tsaron ƙasa a matsayinsa na babban ginshiƙi, ya shafi karewa da tabbatar da kiyaye muradun ƙasa, waɗanda suka ƙunshi manufofi da ƙimomin al’umma. Haka kuma, yana nufin tabbatar da tsaron ƙasa, al’ummarta, muhimman ababen more rayuwarta da cibiyoyinta cikin ɗorewa. A taƙaice, ingantaccen tsaron ƙasa shi ne ginshiƙin ci gaban ƙasa.

A halin yanzu, manyan ƙalubalen tsaro da Najeriya take fuskanta a cikin gida sun ta’allaƙa ne kan rikice-rikicen al’umma, fashi da makami, ayyukan ’yan bindiga, garkuwa da mutane, rikicin makiyaya da manoma, rikice-rikicen da suka shafi zaɓe da tashe-tashen hankulan siyasa, yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago, zanga-zangar ɗalibai da kuma saɓanin da ya shafi iyakokin ƙasa.

Saboda haka, kamar sauran ƙasashe masu tasowa da waɗanda suka ci gaba, babu shakka Najeriya tana fuskantar ƙalubalen tsaro masu fuskoki da dama a halin yanzu.

Wasu masu sharhi kan al’amuran ƙasa, sun ɗora alhakin waɗannan matsaloli kan gazawar tsarin tsaro na ƙasa, wanda a ganin su ya kasa bai wa hukumomin tsaro damar shawo kan matsalolin yadda ya kamata. Saboda haka, sun yi kira da a sake fasalin tsarin tsaron baki ɗaya. Wasu kuma suna ganin matsalar ta samo asali ne daga ƙarancin horar da jami’an tsaro da kuma rashin ingantaccen haɗin kai da daidaito a tsakanin hukumomin tsaro. Wasu da dama kuma suna ɗora laifin kan rashin wadatattun kayan aiki na zamani.

A gaskiya, duk waɗannan abubuwan da aka ambata suna iya haifar da mummunan tasiri ga inganci da ƙwarewar jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu. Saboda haka, akwai buƙatar a magance su, ciki har da ƙara yawan ma’aikatan tsaro, la’akari da yadda yawan al’umma ke ƙaruwa cikin sauri da kuma yadda tsarin zamantakewar al’umma ke ƙara sarƙaƙiya.

Ƙoƙarin da ake yi a yanzu na karkasa tsarin aikin ’yan sanda, abin farin ciki ne ƙwarai. Sai dai, a gani na, ya kamata wannan tsari ya kai har matakin ƙananan hukumomi, ba wai ya tsaya a matakin jihohi ba, domin tsarin da zai tsaya a jihohi zai iya ci gaba da kasancewa mai nauyin gudanarwa a matakin sama.

Matsayin Najeriya A Duniya:

Wasu nazarce-nazarce, galibinsu daga ƙasashen waje, sun yi ƙoƙarin sanya ƙasashen duniya a jerin matsayi bisa la’akari da yawan tashe-tashen hankula, talauci, ma’aunin ci gaba, mace-macen mata masu juna biyu ko masu haihuwa da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Duk da cewa akwai yiwuwar amfani da ƙididdiga ta hanyar da ba ta dace ba, ko kuma samun kura-kurai a cikinta, matsayin Nijeriya a waɗannan jerin ƙasashe ba abin alfahari ba ne sosai. Akwai abubuwa da dama da ya kamata a inganta, duk da cewa waɗannan matsaloli ba su taso cikin dare ɗaya ba.

Sai dai, akwai buƙatar gaggauta magance waɗannan matsaloli a cikin ƙoƙarin da ake yi na bunƙasa ƙasa. Wannan kuwa ya kamata ya zama ɗaya daga cikin abubuwan da waɗanda suke gudanar da ayyukan adabi za su mayar da hankali a kansu, ta hanyar jawo hankalin hukumomin da abin ya shafa zuwa ga waɗannan matsaloli.

Bayan na bayyana waɗannan abubuwa, ina ganin bai dace a riƙa sanya ƙasashe a jerin matsayi bisa la’akari da yanayin tsaronsu ba, domin kowace ƙasa tana da irin nata yanayin da kuma ƙalubalen da suka bambanta da na sauran ƙasashe.

Adabin Najeriya Da Ƙalubalen Da Ƙasar Take Fuskanta:

Akwai manyan fannoni guda shida da suka shafi zamantakewa, siyasa da tattalin arzikin Najeriya, waɗanda suka ja hankalin marubutan Najeriya ta fuskar fasaha da nazari tun bayan samun ’yancin kai a shekarar 1960, har ma da wasu ’yan shekarun da suka gabaci wannan lokaci.

Waɗannan batutuwa da suka zama abin damuwa, waɗanda fitattun ayyukan adabi suka yi nazari a kansu, sun haɗa da:

• Rikicin da ke tsakanin al’adun mulkin mallaka da na gargajiyar ’yan ƙasa.

• Cin hanci da rashawa.

• Mulkin soja.

•Yaƙin basasa

• Rikice-rikicen ƙabilanci da na addini.

• ’Yancin ɗan Adam da batutuwan da suka shafi jinsi.

Kare Martabar Najeriya:

Idan aka yi nazari cikin adalci da rashin son rai, kan ayyukan adabi da aka samar a Najeriya tsawon shekaru, za a fahimci cewa marubutan Najeriya sun yi wa kansu da ƙasarsu abin alfahari.

A halin yanzu, Najeriya tana fuskantar ƙalubale masu yawa, har ta kai ga wasu daga cikinsu za su iya sa mutum ya fara kallon ƙasar da mummunan zato, har ya rubuta abubuwa cikin fushi da ɗacin rai game da ita.

A matsayimmu na marubuta, za mu iya taimaka wa ƙasar nan wajen shawo kan wasu daga cikin waɗannan ƙalubale, ta hanyar fito da su fili cikin hikima da manufa ta gyara.

Adabi zai ci gaba da kasancewa wata hanya ta bayyanawa, rubutawa da adana abubuwan da suka faru a baya da kuma waɗanda suke faruwa a yanzu, domin wadatar da tunaninmu da kuma yi mana jagora a rayuwarmu ta ƙashin kai da ta al’umma, a harkokin mulki da kuma wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa.

A lokutan tarurruka, muna rera taken ƙasarmu cikin girmamawa, ko kuma mu saurare shi ta kafafen watsa labarai, inda muke yabon Najeriya a matsayin ‘Ƙasarmu Uwa,’ tare da alƙawarin kare haɗin kan ƙasar.

Saboda haka, duk da cewa mutum na iya samun dalilan yin shakku ko rashin jin daɗi game da wasu abubuwan da suke faruwa a wasu lokuta da kuma a wasu matakai, ba abin karɓuwa ba ne mutum ya riƙa zagin iyayensa ko kuma ya yi watsi da su.

Duk irin ɗacin ran da mutum zai ji, ya kamata ya bayyana shi cikin natsuwa da hanyar da za ta kawo gyara, kamar yadda yaro zai yi magana da iyayensa ko wani babba cikin ladabi da girmamawa.

Bugu da ƙari, rubutu game da ƙasarka baki ɗaya ya kamata ya kasance cikin hanyar da ba za ta saɓa wa dokokin da suke aiki a ƙasar ba, musamman dokokin da suka haramta cin amanar ƙasa da ayyukan kifar da gwamnati.

Haka kuma, idan rubutun ya shafi wasu mutane ne kai tsaye, ya kamata marubuci ya yi taka-tsan-tsan, don kada ya faɗa cikin laifin ɓata suna. Domin tabbatar da cewa mutum yana bin doka, dole ne ya tabbatar da sahihancin bayanan da yake amfani da su.

’Yancin faɗar albarkacin baki da Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar, ba cikakken ’yanci ba ne wanda ba shi da iyaka.

Akwai darasi da ya kamata mu koya daga wani abin da yake cikin tarihin da muke iya tunawa, game da wani fitaccen ɗan ƙasar waje wanda ya yi amfani da baiwar rubuce-rubucensa, ta hanyar da ba ta dace ba, har ya taimaka wajen wargaza ƙasarsa.

Haka kuma, ya kamata mu fahimci cewa salon yaƙi a wannan zamani ba lallai ne ya buƙaci manyan tankokin yaƙi da manyan makaman atilare ba. Domin farfaganda da yaɗa bayanan ƙarya ta hanyar rubuce-rubuce, suna iya yin mummunar illa, har ta kai ga cin ma irin wannan manufa ta lalata ƙasa.

Ya kamata mu fahimci wannan haɗari kuma mu kasance masu taka-tsan-tsan da bin shawarwarin da suka dace.

Kammalawa:

Abin lura ne cewa, tun bayan samun ’yancin kai, Najeriya ta ci gaba da kiyaye cikakken ikon mallakarta da kuma iyakokinta, duk da ƙalubalen da ta fuskanta.

Kodayake har yanzu tana fuskantar wasu daga cikin waɗannan ƙalubale, ya kamata masu kishin ƙasa su ɗauke su a matsayin wani lokaci ne da zai wuce, a cikin ƙoƙarin da ake yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar.

Saboda haka, dangane da matsayin Najeriya a duniya ta fuskar adabi, ya kamata a yi amfani da adabi ne wajen gina ƙasa, ba wai rusa ta ba. Wannan kuwa yana nufin yin duk mai yiwuwa, wajen bunƙasa zaman lafiya, kwanciyar hankali, tsaron ƙasa da kuma gina al’umma mai ƙarfi.

Ya kamata a yaba wa shugabannin da suka jagoranci Ƙungiyar Marubuta ta Najeriya (Association of Nigerian Authors – ANA) a lokuta daban-daban, bisa jajircewarsu da hangen nesa wajen kafa wannan katafaren gini, tare da samar da damammaki na yau da kullum, domin tattaunawa da musayar ra’ayoyi kan adabi da kuma amfani da sakamakon waɗannan tattaunawa wajen ci gaban Najeriya da al’umma baki ɗaya.

Wannan muhalli abin alfahari ne kuma wata babbar alama ce ta martabar Najeriya a duniyar adabi.

Sun yi nasarar aza tubali mai ƙarfi, wanda al’ummomin da za su zo nan gaba, za su iya ci gaba da ginawa a kansa.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya yi masu albarka, ya kuma ci gaba da ƙarfafa su, domin su ɗore da wannan kyakkyawan aiki.

Na gode.

__________

Dr. Bukar Usman, OON, tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, kuma Shugaban Ƙungiyar Nazarin Fasaha da Adabin Baka ta Najeriya (Nigerian Folklore Society), daga shekarar 2014 zuwa 2026.

__________

Previous Post

Galadiman Katsina Commends Governor Dikko Radda’s Development Agenda

Related Posts

Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa
Adabi

Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa

November 1, 2026
Fatima Gana: Marubuciya Mai Alƙalami Biyu
Adabi

Fatima Gana: Marubuciya Mai Alƙalami Biyu

September 25, 2026
ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)
Adabi

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

March 29, 2026
Bago Ya Taya Ndace, Sabon Shugaban VON Murna

Bago Ya Taya Ndace, Sabon Shugaban VON Murna

October 21, 2023
Gwamnan Jigawa Ya Kama Ma’aikatan Asibiti Suna Sayar Da Magungunan Gwamnati

Gwamnan Jigawa Ya Kama Ma’aikatan Asibiti Suna Sayar Da Magungunan Gwamnati

July 5, 2023
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Adabi, Tsaron Ƙasa Da Matsayin Najeriya A Duniya
  • Galadiman Katsina Commends Governor Dikko Radda’s Development Agenda
  • NASIHARMU TA YAU (43)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Adabi, Tsaron Ƙasa Da Matsayin Najeriya A Duniya

Adabi, Tsaron Ƙasa Da Matsayin Najeriya A Duniya

November 6, 2026
Galadiman Katsina Commends Governor Dikko Radda’s Development Agenda

Galadiman Katsina Commends Governor Dikko Radda’s Development Agenda

November 5, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.