• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, October 14, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Siyasa

Gwamna Radda Ya Cancanci Maimaita Kujerarsa

- Dakta Aminu Waziri

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 14, 2026
in Siyasa
0
Gwamna Radda Ya Cancanci Maimaita Kujerarsa

Hagu-Dama: Gwamna Dakta Dikko Umaru Radda da Dakta Aminu Waziri

14
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamna Radda Ya Cancanci Maimaita Kujerarsa – Aminu Waziri

Hagu-Dama: Gwamna Dakta Dikko Umaru Radda da Dakta Aminu Waziri

 

Related posts

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

October 10, 2026
Fati Muhammad ‘Yar Fim Ta Taro Fushin Mabiya Atiku

Fati Muhammad ‘Yar Fim Ta Taro Fushin Mabiya Atiku

October 8, 2026

__________

Dakta Aminu Waziri, ɗaya ne daga jigajigan ‘ya’yan Jam’iyyar APC a Jihar Katsina. A makon jiya ne ya tattauna da Mujallar Taskar Gizago, inda ya amsa tambayoyin Bashir Yahuza Malumfashi dangane da takarar Gwamna Malam Dikko Umaru Radda a karo na biyu. Ga yadda tattaunawar ta gudana:

_________

Ga shi dai an fara yaƙin neman zaɓe kuma Gwamna Malam Dikko Radda yana neman kujerarsa a karo na biyu, shin kana ganin ya cancanci al’umma su sake ba shi dama?

Dakta Waziri: Babu ko shakka, Dakta Dikko Umaru Radda, PhD. CON ya cancanci ya maimaita kujerarsa, domin kuwa ya yi mun gani kuma yana kan yi. Shi ne jagoranmu kuma jigon gwagwarmayar assasa fandeshin na bunƙasa sabuwar Jihar Katsina, domin amfanin yau da gobe da jibi, zuwa jikoki da tattaɓa kunne da umhumhum, abin da ake kira da Turanci “Building Your Future.”

Ko za ka ba mu misalin ayyukan da ya yi a wannan zango, da har ya cancanci a sake zaɓen shi?

Dakta Waziri: Malam Dikko, koda ya amshi ragamar mulki, da ilimi yake aiki, na gano abin da zai amfani al’ummar Jihar Katsina. Ya tattara ƙwararrun masu ilimi domin su taya shi gano abin da talakan Katsina ke buƙata, tare da tanadin magance su. Ɓangaren Lafiya, an ɗauki ƙwararrun ma’aikatan lafiya sama da dubu goma sha kuma a yanzu haka an tallata guraben ma’aikatan lafiya, domin a ɗauke su aiki. Ya samar da na’urarorin aikin lafiya daban-daban, musamman cibiyar da ake ginawa a Asibitin Ƙashi na Katsina. Duk Afirka ta Yamma, idan aka kammala ta, ita ce za ta zama mafi girma da inganci.

Malam Dikko ya bunƙasa asibitoci da ɗakunan shan magani a dukkan ƙananan hukumomin Jihar Katsina. A dukka Mazaɓu 361 na jihar, an samar masu wuraren kula da lafiya. An gina wa ma’aikatan lafiya gidaje sannan kuma ya kawo motocin ɗaukar majinyata (ambulance) masu ƙafa uku, domin shiga lungu da saƙon karkara. Motoci ne na tafi da gidanka, masu ɗauke da kayan aiki.

Matsalar tsaro na daga cikin manyan matsalolin da suka addabi Jihar Katsina, wace rawa Gwamna ya taka a wannan ɓangaren, a zangon nasa na farko?

Dakta Waziri: Babu shakka matsalar tsaro tana gaba-gaba a matsalolin da Gwamna ya gada. Ma’ana, sanannar matsala ce da ta addabi kusan ko’ina a Arewa. Amma alhamdu lillahi, Gwamna yana aiki bakin rai bakin fama. Ya kafa dakarun tsaro na Community Watch. An ba su horo kuma an baza su ko’ina a Jihar Katsina, wuraren da suka fi fuskantar barazanar ‘yan bindiga. Gwamna yana amfani da sanyi da zafi, wato sasanci da wuta (stick and carrot) wajen magance wannan babbar matsala. Don haka bai zauna haka nan ba, yana iyaka ƙoƙarinsa. Kuma kada mu manta, harkar tsaro ta kowa ce, don haka dole kowa ya sa hannu domin cin ma nasara.

Dakta, yaya batun ayyukan raya ƙasa, me Gwamna ya yi a wannan ɓangare?

Dakta Waziri: A wannan batu, Gwamna shi ne “Master of Urban Renewal.” Ma’ana, shi ne jigon raya birane da karkara. Batun hanyoyi da sauran ayyukan bunƙasa ƙasa, Katsina a yanzu ana bunƙasa da faɗaɗa hanyoyi, haka sauran sassan Jihar Katsina. Ga Funtua, an shinfiɗa hanyoyi, Malumfashi, ba a fi wata uku ba, an ƙaddamar da aikin hanyoyin cikin gari. Haka Mashi da Daura da sauran sassan jiha. Yanzu haka ana aikin hanyar da ta kai kilomita 43 tun daga Kuraye, ta tafi ta fita har zuwa Dutsin-ma. Wannan kaɗan ke nan na gutsuro maka.

Yaya batun ilimi kuwa a Jihar Katsina?

Dakta Waziri: Daga hawansa, Dakta Umaru Radda ya ɗauki malaman makaranta sama da dubu 20. An fiddo da manhaja wacce ke ɗauke da darussan da ake koya wa yara, an raba wa malamai, domin sauƙaƙa masu bincike da nazari – kai tsaye za su koyar da yara cikin sauƙi. Ya bunƙasa ilimi, inda ya gina makarantu daban-daban. Kai akwai ma makarantu na musamman da ya gina, domin ɗalibai masu hazaƙa ta musamman. An tanade a sassa uku na Jihar Katsina, wato a yankin Katsina, yankin Daura da yankin Funtua. Ya zuwa yanzu ma ta Radda har an fara karatu. Nan da shekara 10, idan ka yi nazari, abin da makarantun nan za su samar na amfani Allah kaɗai ya san iyakarsa. Ni har mamaki nake yadda Gwamna Radda ya cin ma wannan gagarumin aiki a cikin shekaru uku da rabi.

To, yaya ɓangaren bunƙasa rayuwar al’umma, musamman mata da matasa?

Dakta Waziri: A wannan ɓangare, Malam Dikko, hukuma ya kafa ta musamman domin wannan, wato KASEDA. Ko a makon da ya gabata, Gwamna ya buɗe irin wannan cibiyoyin na gina matasa, maza da mata, a ƙarƙashin Ƙungiyar Gina Matasa ta Andaje, a garin Malumfashi. Sama da matasa 200 aka yaye, bayan an koya masu sana’o’i iri daban-daban, aka ba su kayan sana’a da kuɗi a matsayin jari da za su fara gudanar da abin da suka koya.

An taimaka wa manya da masu matsakaitan sana’o’i da tallafin kuɗi masu yawa, domin bunƙasa masana’antu da sauransu. Ta ɓangaren bunƙasa rayuwar mata ma ana yi. Ko a makon jiya, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya buɗe wani tsari na tallafa wa mata ta wannan ɓangare a Katsina. Hatta Bankin Duniya yana da hannu a wannan shiri tare da Gwamnatin Jihar Katsina. Al’umma za su ci gaba da cin gajiyar wannan shiri har iyaka inda Allah ya nufa.

Daga ƙarshe, mene ne saƙonka ga al’ummar Jihar Katsina?

Dakta Waziri: Kirana ga al’ummar Jihar Katsina, ƙwai da kwarkwata, mu fito mu ba Malam Dikko Radda ƙuri’unmu. Ya yi abin kirki mun gani, domin dai da wayonmu, ba a taɓa gwamnati a Jihar Katsina da ta cin ma nasara a zangon farko na mulki ba, cikin shekaru uku da rabi, kamar wannan gwamnati ta Malam Dokko Umaru Radda. A halin yanzu dai, babu wani ɗan takarar gwamna da za ka kwatanta shi da Malam Dikko, tun da ya yi mun gani. Don haka ina sanar da al’umma cewa, da sabon gini, gara yaɓe. Mu ci gaba da ba shi haɗin kai, ya dawo karo na biyu, domin ya ci gaba da bunƙasa al’umma. Hatta su ma ‘yan adawa, ina kira da su ajiye komai, su zo a mara wa Malam Dikko baya, su jira zuwa 2031 sai su nema, domin kuwa al’ummar Jihar Katsina Dikko Umaru Radda suke da buƙata.

__________

Previous Post

NASIHARMU TA YAU (21)

Related Posts

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami
Siyasa

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

October 10, 2026
Fati Muhammad ‘Yar Fim Ta Taro Fushin Mabiya Atiku
Siyasa

Fati Muhammad ‘Yar Fim Ta Taro Fushin Mabiya Atiku

October 8, 2026
Darasin Rayuwa Daga Al’amarin Malam Nasir El-Rufa’i
Siyasa

Darasin Rayuwa Daga Al’amarin Malam Nasir El-Rufa’i

September 28, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Matasa Masu Fusata Sun Ƙone Ofishin ’Yan Sanda

Matasa Masu Fusata Sun Ƙone Ofishin ’Yan Sanda

June 20, 2026
Minista Ya Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Zuba Jari Don Haɓaka Shirin Iskar Gas Na CNG

Minista Ya Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Zuba Jari Don Haɓaka Shirin Iskar Gas Na CNG

January 2, 2024
Matsalar Tsaro A Najeriya: Madalla Da Majalisar Dokokin Amurka

Matsalar Tsaro A Najeriya: Madalla Da Majalisar Dokokin Amurka

November 26, 2025
Har Yanzu Akwai Cutar AIDS Kuma Za Mu Taru Mu Yaƙe Ta Da Gaske – Dokta Bala Nuhu

Har Yanzu Akwai Cutar AIDS Kuma Za Mu Taru Mu Yaƙe Ta Da Gaske – Dokta Bala Nuhu

July 6, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Gwamna Radda Ya Cancanci Maimaita Kujerarsa
  • NASIHARMU TA YAU (21)
  • An Appeal to Northern Nigeria’s Social Media Activists

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Gwamna Radda Ya Cancanci Maimaita Kujerarsa

Gwamna Radda Ya Cancanci Maimaita Kujerarsa

October 14, 2026
NASIHARMU TA YAU (21)

NASIHARMU TA YAU (21)

October 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.