William Ekong: Tsohon Kyaftin Ɗin Super Eagles Ya Musulunta
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Tsohon kyaftin ɗin Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Super Eagles ta Najeriya, kuma ɗan wasan Ƙungiyar Al-Ahli, William Troost-Ekong, ya musulunta.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ɗan wasa Troost-Ekong ya ambata Kalmar Shahada a birnin Doha na ƙasar Qatar, inda yake buga wasa a ƙungiyar Al-Ahli ta Qatar Stars League. Jaridar Qatar mai suna Al-Arab ce ta wallafa labarin tun da farko a jiya Laraba.
Wani mashahurin malamin addinin Musulunci, Dakta Muhammad Salah, shi ma ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook da aka tabbatar da sahihancinsa, inda aka ga ɗan wasan yana karanta kalmomin Shahada.
Ɗan wasan mai shekaru 33 ya fara komawa yankin Larabawa ne a lokacin bazarar shekarar 2024, lokacin da ya sanya hannu kan kwantiragi da Ƙungiyar Al-Khaleej ta ƙasar Saudiyya.
Daga nan ya koma ƙungiyar Al-Ahli ta Qatar a watan Janairun 2026, inda ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara ɗaya da rabi. Tun daga lokacin ya buga wasanni 14 a dukkan gasa, ciki har da wasa guda da ya buga a kakar wasa ta bana.
A fagen wasannin ƙasa da ƙasa kuwa, Ekong ya buga wa Najeriya wasanni 83 tsakanin shekarar 2015 zuwa 2025, inda ya zura ƙwallaye 8.
Ya kai wasan ƙarshe na gasar Africa Cup of Nations (AFCON) ta 2023 da aka gudanar a Côte d’Ivoire kuma an zaɓe shi a matsayin ɗan wasan da ya fi ƙwarewa a gasar.
Troost-Ekong ya kuma wakilci Najeriya a gasar FIFA World Cup da kuma Wasannin Olympics, inda ya kafa kansa a matsayin ɗaya daga cikin ƙwararrun ‘yan wasan baya da Najeriya ta samu a cikin shekaru goma da suka gabata.
Ya yi fitacciyar rayuwar wasa tare da Super Eagles a matakin ƙasa da ƙasa, inda ya buga wa Ƙungiyar Super Eagles wasanni sama da 70.
__________












