Albarkar Hausa

_________
Amintattun aminan Aminu Aminulla,
Allah ya amintalalaye.
Balbalin bala’in balbalon balala
Allah ya balalaye.
Dandalin dalolin dabdalar dalala,
Allah ya dalalaye.
Falfalon falalan falfalin falala,
Allah ya falalaye.
Gangaran gararan gargaron galala,
Allah ya galalaye.
Hargitsan hargitsatsan hargitsalala,
Allah ya hargitsalalaye.
Ingantattun ingititin ingatatan ingatalalan,
Allah ya ingatalalaye.
Jajirtattun jajiratan jajiratun jajiratalalan,
Allah ya jajirtalalaye.
Karkatattun karkitatan karkikatatun karkitalalan,
Allah ya karkitalalaye.
Ƙanƙararrun ƙarƙitatan ƙaƙiƙatatun ƙarƙitalalan,
Allah ya ƙarƙitalalaye.
Lallaɓaɓɓun lallaɓaɓan lallaɓaɓun lalliɓalalan,
Allah ya lallaɓalalaye.
Mammagaggun mammagagan mammagagun mammagalalan,
Allah ya mammagalalaye.
Nannagaggun nannagagan nannagagagun nannagalala,
Allah ya nannagalalaye.
__________
© Bashir Yahuza Malumfashi
Ranar Hausa ta Duniya,
Laraba 13-03-1448 (Hijiriyya)
26-08-2026
__________












