• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, July 30, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama

RAHOTON MUSAMMAN

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 30, 2026
in Babban Labari
0
Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama

Riƙe da sandar mulki, mai martaba Oba Adekunle Makama ne, tare da Janar Buratai da sauran manyan baƙi, a yayin bikin A'isha Tukur Buratai da Umar Abba Zoru

6
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne
– Oba Adekunle Makama

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Mai martaba, Olowu na Al’ummar Owu-Kuta, Dakta Adekunle Makama Oyelude, CON kuma Tegbosun III, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa ta Najeriya, Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai, CFR (mai ritaya), tsohon Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Betaran Biu kuma Garkuwan Keffi, mutum ne da za a iya kira da babban ɗan kishin ƙasa, musamman irin yadda yake mu’amalar alheri da dukkan alummomin da suke a faɗin Najeriya, har ma da na ƙasashen waje.

Related posts

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

July 28, 2026
Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026

Mai sarauta Adekunle, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar Osun, ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da wakilanmu a garin Keffi, a yayin shagulgulan bikin auren A’isha Tukur Buratai da angonta, Umar Abba Zoru.

Da yake bayyana dangantakarsa da Janar Buratai, Oba Adekunle ya bayyana cewa: “Buratai aminina ne, amana ce ke tsakaninmu. Duk hidimarsa, ina ciki. Haka shi ma, duk hidimata yana ciki. Shi nagartaccen mutum ne, wanda ake dawwamammen zumunci da shi, ba tare da tsoron komai ba. Wannan shi ne babban dalilin amana da zumunci a tsakaninmu.”

Hotuna daban-daban, a yayin bikin A’isha Tukur Buratai da Umar Abba Zoru

Da ya juya kan ma’auratan, Oba ya ce: “Ita ɗiyarmu A’isha, ta samu tarbiyya mai kyau. Ina da yaƙinin ba za ta ba mijinta damuwa ba. Haka shi ma ango, ya fito daga gidan mutunci. Don haka, ina yi masu fatan alheri da addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.”

Game da halin da ƙasa take ciki, yadda ake samun matsalolin tsaro a sassa daban-daban, Oba Adekunle Makama ya yi kira ga al’ummar ƙasa da su sanya ido sosai a yankunansu, inda ya ce idan sun ga wani abu na rashin tsaro, su sanar wa hukuma kuma su riƙa ba jami’an tsaro haɗin kai a aikinsu.

“Su kuma masu mulki, ina kira a gare su, da su ji tsoron Allah, su yi mana adalci. Idan suka yi mana adalci, da Kudu da Arewa, Gabas da Yamma sai a samu zaman lafiya da ci gaba,” in ji mai martaba.

Ga malaman addini kuwa, Oba Adekunle ya ce: “Ina kira a gare ku, ku ci gaba da wa’azi da jan hankalin jama’a da ayoyin Allah amma ku kauce wa shiga lamarin siyasa. Mu a Kudu, malamai ba su tsoma baki a sha’anin siyasa.”

Haka kuma ya yi kira ga al’ummar ƙasa gaba ɗaya da su daina nuna wariya da ƙabilanci ga juna. “Mu yi koyi da rayuwar Janar Buratai, wanda shi cikakken ɗan kishin ƙasa ne, mai son mutane. Kudu da Arewa, Gabas da Yamma, kowa nasa ne. Dubi dai misalin yadda aka gudanar da bikin nan na ɗiyarmu, duk Najeriya an taru,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “don haka, babu abin da ya fi zumunci, domin Manzon Allah (saw) ya yi kira da a yi zumunci. Saboda haka a ci gaba da zumunci.”

A ranar Asabar da ta gabata ce dai, aka gudanar da gagarumin bikin aure da hawan dawaki, wanda aka shirya domin taya murnar auren A’ishatu Tukur Buratai da Umar Abba Zoru. An gudanar da wannan babban taro ne a Gidan Gonar Tukur and Tukur Farms, da ke Gora, Jihar Nasarawa, inda fitattun baƙi daga sassa daban-daban na Najeriya da ma ƙasashen waje suka hallara domin taya amarya da ango murna.
__________

Previous Post

General Buratai Is a Great Patriot — Oba Adekunle Makama

Next Post

Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

Related Posts

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja
Babban Labari

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

July 28, 2026
Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista
Babban Labari

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo
Babban Labari

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026
Next Post
Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Ruhin Bukar Usman

Ruhin Bukar Usman

May 11, 2024
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

June 10, 2025
I Will Tackle Banditry Head-on – Governor Radda

I Will Tackle Banditry Head-on – Governor Radda

August 24, 2024
AIKIN RUWA A MALUMFASHI: AN BUƘACI AL’UMMA SU BA HUKUMA HAƊIN KAI

AIKIN RUWA A MALUMFASHI: AN BUƘACI AL’UMMA SU BA HUKUMA HAƊIN KAI

June 16, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?
  • Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama
  • General Buratai Is a Great Patriot — Oba Adekunle Makama

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

July 30, 2026
Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama

Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama

July 30, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.