RAMADAN KARIM: 05-1447
__________

‘Yan uwa, ina yi maku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Bayan haka, a yau Allah ya nuna mana rana ta 5 a Ramadan, don haka bari mu ribaci wannan rana da ‘yar nasiha:
Wani babban al’amari da ke wahalar da mu shi ne harshe, ma’ana maganganunmu ga juna. A yayin da muke azumi, yana da kyau mu ladabtu da tsare harsunanmu daga sakakkun kalamai. Hakan kuma ya kamata mu kasance a dukkan rayuwarmu. Mu kiyayi yin ƙarya, zunɗe, gulma da yaɗa jita-jita.
Allah (swt) a cikin Suratul Ahzab 33:70 ya umurci mutane da cewa: “Ku faɗi magana madaidaiciya.” Ma’ana, a duk lokacin da za mu yi magana, mu yi magana mai adalci, ba karkatattar magana ba.
Manzon Allah (saw), kamar yadda Bukhari a Hadisi mai lamba 10 da Muslim a Hadisi mai lamba 40 suka ruwaito, ya ce: “Musulmi shi ne wanda mutane suka tsira daga sharrinsa.”
Hakan yana nufin a matsayinmu na Musulmi, wajibi ne mu kiyaye gaɓoɓinmu da harshenmu daga cutar da mutane. Idan kowa ya kame kansa daga cutar da ɗan uwansa, babu shakka za a zauna lafiya.
Allah ya ba mu ikon kame kanmu da bakunanmu daga cutar da juna. Amin-Summa-Amin!
__________













