Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Mutane da dama sun kaɗu kuma sun yi mamakin yadda furodusa Aminu Saira ya wallafa fim ɗin Labarina a jiya Juma’a, duk da cewa a ranar ce ɗaya daga cikin ‘yan wasan fim ɗin, Jidda Fulani ta rasu kuma aka yi jana’izarta.
An yi zaton Furodusa Saira zai ɗan jinkirta fitar da fim ɗin a wannan makon, ko domin jimami da ta’aziyyar ta, amma bai yi haka ba. Ya saki fim ɗin a lokacin da take kwanciyarta a ranar farko a ƙabari.
Wasu na ganin cewa gaskiya Furodusa bai kyauta ba. Wasu kuma suna ganin kamar babu wata damuwa saboda dai aiki ne da ta yi kuma aka biya ta.
Jama’a yaya kuke ganin wannan lamari?
__________













