• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, April 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sinadarin Rayuwa

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

SINADARIN RAYUWA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 30, 2025
in Sinadarin Rayuwa
0
Kada Ka Karaya Da Rayuwa

Kada ka karaya da rayuwa!

19
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

November 24, 2025
A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne

A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne

November 11, 2025
Kada ka karaya da rayuwa!

 

                               •••••••
Sallama da aminci da fatan alheri ga ‘yan uwa. A ci gaba da zizara mana sinadaran yauƙaƙa rayuwa, maudu’inmu na yau yana mana ishara ne game da ita kanta rayuwa – cewa ita ƙalubale ce kuma ba a karaya da ita, muddin dai ana son a cin ma nasara.

Ɗan uwa, ‘yar uwa, ko kun san cewa rayuwarmu tana cike da ƙalubale? Babu shakka, rayuwarmu ba aljanna ba ce. Rayuwa ce mai taken faɗuwa da tashi, hawa da sauka, nasara da asara, daɗi da wahala. Rayuwa ce ta dacewa, kamar kuma yadda take rayuwar nadama.

Ɗan uwa, ka taɓa shiga wani yanayi na ƙunci? ‘Yar uwa, ke ma ba za ki rasa shiga wani yanayi mara daɗi ba a rayuwarki. Wataƙila kin taɓa fuskantar rabuwa da miji ko masoyi. Wataƙila kin taɓa samun faɗuwa a harkar kasuwanci ko kuma kika rasa aikinki a wata ma’aikata ko hukumar gwamnati.

Ɗan uwa, shin kai ɗalibi ne? Wataƙila ka taɓa faɗuwa jarabawa, ko kuma an taɓa korar ka ma gaba ɗaya daga makarantar saboda wani dalili. Kada ka saduda, ka ce shi ke nan rayuwarka ta neman ilimi ta ƙare. A’a, ba ta ƙare ba. A lokacin da ka faɗi jarabawa ko kuma a wani dalili aka kore ka daga makaranta, me ya kamata ka yi?

Maimakon ka shiga alhini da takaici, wuri za ka samu ka zauna, ka shiga nazarin abin da ya kai kuma ya komo, har wannan al’amari ya faru. Ka faɗi jarabawa, to me ya sa ka faɗi? Ka fara tunanin abin da ya haddasa faɗuwar taka, alhali sauran ɗalibai da dama sun cinye, wasu ma har da yabo. Watakila ba ka yi karatu da nazarin darussan da aka koya maka ba. Wataƙila ma tun da farko ba ka fahimci darussan ba ko kuma ka tsaya wasa da sauran shugulan da suka kawar da hankalinka ga karatu. Idan ka gano dalilin, sai ka kakkaɓe rigarka, ka ɗauki aniyar gyara kuskurenka, domin gaba.

Haka lamarin yake ga dukkan sassan rayuwa. A duk lokacin da ka kasa cin ma biyan wata buƙata ta rayuwa, akwai dalilin faruwar haka. Idan rayuwa ta kakkarya ka, hakan na nufin ka shirya a sake ɗora ka ta wata hanya daban. A matsayinka na ɗan kasuwa, a lokacin da ka kasa cin riba ko ka gamu da wata asara, lallai akwai dalili. Ka yi saurin binciko dalilin, kuma a nan maganinka yake.

Wataƙila ma ba ka san kan sana’ar ba tun da farko. Ka shiga harkar ce a ido rufe, ba tare da ka koya daga masananta ba. Don haka sai ka koma ka koye ta yadda ya dace, sannan ka ci gaba. Har kullum dai, ka koyi sana’a ko aiki, kafin ma ka fara. Amma lallai kada ka sake ka karaya.

A lokacin da ka fuskanci wata matsala ko wani ƙalubale, ka amince cewa a ɓangarorin da matsalar ta bayyana, ta haska maka wata sabuwar fahimta ce. A yayin da kika samu matsala da mijinki, har aurenku ya rabu. Da kin zauna kika nazarci yadda matsalar ta faru, nan da nan za ki samu waraka, domin gyaran irin wannan matsala a gaba.

A lokacin da wani dalili ya sanya aka kore ka daga wurin aikinka. Da zarar ka natsu, za ka gane dalilin faruwar haka. Ke nan sai ka ɗauki ɗamarar gyarawa don gaba. Nan gaba idan ka samu wani aikin, ba za ka sake maimaita wannan kuskuren ba, domin ka san abin da ya haifar maka a baya.

Abin fahimta dai shi ne, rayuwa na ɗauke da ƙalubale iri-iri. Don haka ka zama cikin shirin fuskantar kowane irin canji da ta bijiro maka da shi. Rayuwa, hagu ce da dama, sama ce da ƙasa, zafi ce da sanyi, inuwa ce da rana. A duk lokacin da ta bijiro maka da rana, maza ka nemi inuwa. Amma kada ka sake ka karaya da ita.
_______________

Previous Post

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

Next Post

SAKAMAKON FARKO NA GASAR RUBUTUN HAUSA TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

Related Posts

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara
Sinadarin Rayuwa

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

November 24, 2025
A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne
Sinadarin Rayuwa

A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne

November 11, 2025
A Rayuwa Babu Abin Da Ya Kai Haƙuri
Sinadarin Rayuwa

A Rayuwa Babu Abin Da Ya Kai Haƙuri

November 9, 2025
Next Post
SAKAMAKON FARKO NA GASAR RUBUTUN HAUSA TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON FARKO NA GASAR RUBUTUN HAUSA TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

Kasafin N18b: INEC za ta biya ma’aikata 16,000 alawus ɗin su, ba a zaɓen Bayelsa, Imo da Kogi za ta kashe kuɗaɗen ba – Yakubu

November 4, 2023
Dharmendra: Ta’aziyyar Bankwana Da Mashahurin Afto

Dharmendra: Ta’aziyyar Bankwana Da Mashahurin Afto

November 25, 2025
BINTA OLA: Allah Ji Ƙan Ki Da Rahama

BINTA OLA: Allah Ji Ƙan Ki Da Rahama

October 4, 2023
SASSANYAN AMINCI (3)

SASSANYAN AMINCI (3)

September 6, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai (A Poem)
  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai (A Poem)

General Buratai (A Poem)

April 26, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.