Hattara Da Munafukan ‘Yan Siyasa A Jihar Kebbi
Daga Malam Abdullahi Idris Zuru

•••••••
Yayin da kakar zaɓuɓɓukan 2027 suke ƙara tunkarowa, ta bayyana a fili cewa wasu ’yan siyasa masu ƙarancin kamun kai a Jihar Kebbi suna ta ƙoƙarin amfani da siyasar munafunci da yaudara wajen cin ma burin siyasarsu a baɗi.
Kamar yadda lamarin ya nuna, mai nufin takarar Gwamna a Jihar Kebbi, a jam’iyyar ADC, Abubakar Malami, kamar yadda ake zargi, ya fara hilata da jan hankalin wasu ’ya’yan Jam’iyyar APC da na PDP da alƙawuran abin duniya, domin su ba shi goyon baya a asirce, da nufin cika burin nasa na siyasa, musamman ganin yadda ya gaza canza ra’ayin al’ummar Jihar Kebbi, dangane da cikakken goyon baya da amincin da suke da shi ga Gwamna Nasir Idris, wanda yake gudanar da sahihin jagoranci da jajircewar ayyukan da ke haifar da ingantaccen sakamako ga al’umma.
Daga cikin waɗannan munafunce-munafunce da suka gaza, akwai ɗaukar nauyin ’yan daba da baragurbi, domin ƙirƙirar yanayin cewa jihar na fama da rashin tsaro.
A ƙarƙashin sabbin dabarun yaƙin ɓata suna, ana zargin cewa ’yan siyasar da ake jan hankalinsu da waɗannan alƙawura, za su kasance jagora wajen aiwatar da wannan mummunan yunƙuri na ɓata sunan Gwamna Nasir Ƙauran Gwandu da gwamnatinsa. An ce matsalar ta’addancin ’yan bindiga da ta addabi kusan dukkan jihohin Arewa, ita ce makamin da suka zaɓa, za su yi amfani da ita domin, yaƙar gwamnatin da al’umma ke so a Jihar Kebbi.
A tunanin waɗannan ‘yan baƙar adawa masu son kai, matsalar tsaro da ake fama da ita a jihar tana cutar da Gwamna Nasir Idris, alhali shi Gwamnan ya ɗauke ta a matsayin annobar da ta shafi al’umma kuma ya himmatu matuƙa wajen ganin an shawo kanta ta kowane hali.
Wata sabuwar dabara da ‘yan adawar za su yi amfani da ita, ita ce ta amfani da wasu kafafen watsa labarai, domin ƙirƙirar labarun bogi da yaɗa ƙarairayi da kiraye-kirayen bogi da zarge-zarge marasa tushe balle makama; duk domin su haifar da matsala kan takarar wa’adi na biyu na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Nasir Idris.

Domin cin ma wannan baƙar manufa tasu, sun shirya za su riƙa rarraba waɗannan ƙarairayi da farfaganda ga gidajen rediyo da kafafen Soshalmidiya. Haka kuma rahotanni sun nuna cewa tuni sun riga sun tura sama da Naira miliyan 100 zuwa ofishin gudanarwarsu na Abuja, waɗanda za a riƙa biyan waɗannan kafafen watsa labarai da na Soshalmidiya.
Yayin da mai son takarar gwamnan na ADC ke jiran amsar waɗansu ’yan siyasar masu son zuciya, wasu ragowar mambobin PDP sun bayyana cewa suna son su ci gaba da kasancewa a jam’iyyarsu, maimakon su shiga jam’iyyar da ba ta da wata sahihiyar makoma. Tsoron da suke yi shi ne, kada su sake gamuwa da mummunan kaye, fiye da wanda suka sha a 2023, duba da gagarumin aikin da Gwamna Nasir Idris ya riga ya gudanar a Jihar Kebbi.
Duk da haka, ana zargin cewa wasu baragurbin ’ya’yan APC, marasa tasiri kuma marasa hangen nesa, saboda son zuciya, suna tunanin haɗa kai da Abubakar Malami domin cin ma manufar hana Shugaba Tinubu da Gwamna Nasir Idris sake samun nasarar zaɓe a 2027.
A ‘yan kwanakin nan, ɓangaren adawa a Jihar Kebbi ya mayar da hankali ne kan siyasantar da matsalar tsaron da ke addabar ƙasa baki ɗaya. A cikin wata sabuwar kinayarsu, ana zargin cewa suna ɗaukar hayar matasa ‘yan zaman banza da ’yan daba da karuwai, domin aiwatar da wannan mummunan ƙuduri da suka kitsa.

An ce matasan da suka ɗauka, musamman daga yankin Bena, ana kwaso su ne daga titi ba tare da sanin iyayensu ba, sannan ake jefa su cikin aika-aikar shaye-shaye. An kuma ce an ba su wayoyin hannu masu tsada, domin amfani da Shoshalmidiya wajen sukar ayyukan ci gaban gwamnati da aibata jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyya, tare da wuce gona da iri wajen ƙirƙirar labaran ƙarya game da hare-haren ’yan bindiga a jihar.
Kodayake ba a ga wani muhimmin martani daga ɓangaren Jam’iyyar APC a kan wannan kiran na ADC ba amma wani jigo a jam’iyyar da ake zargin ya amince da haɗa kai da ADC, ya bayyana suka a kan aikin gyaran hanyoyi da gina makarantu, yana iƙirarin cewa matsalar tsaro ce ta fi damunsa.
Ana da sahihin bayanin cewa Gwamna Nasir Idris ya nuna jajircewa wajen neman mafita ga matsalar ’yan bindiga, ta hanyar tarurruka da manyan masu ruwa da tsaki a harkar tsaron ƙasa. Waɗannan sun haɗa da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa, ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar tare da tsohon Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Christopher Musa, a matsayin babban baƙo da Ƙungiyar Gwamnonin APC da Kwamitin Dattawan Jihar Kebbi, ƙarƙashin Janar Muhammadu Magoro.
Sauran tarukan sun haɗa da na addu’o’in haɗin kai da suka haɗa malaman Musulunci da limaman Kirista daga faɗin jihar da kuma babban taron neman mafita a kan matsalolin tsaro, wanda Ƙungiyar Mamallaka Gidajen Rediyo da Talabijin na Arewa suka shirya. A taron, wanda ya gudana a makon jiya, ya samu halartar tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya, Laftanar-Janar Abdulrahman Danbazau (mai ritaya) da tsohon Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Sani Usman Kukasheƙa da tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega.
Baya ga waɗannan taruka, Gwamna Nasir ya bai wa hukumomin tsaro tallafin kayan aiki da suka haɗa da motocin Hilux 100 da babura 5,000. A ƙarshe, dukkan mahalarta waɗannan tarurruka sun yaba da jajircewar Gwamna Nasir Idris tare da sauran ɓangarorin tsaron ƙasa, wajen neman mafita ga matsalar tsaro.
Babu shakka, wannan yunƙurin ɓata suna da ake ƙullawa daga ɓangaren adawa, ya samo asali ne daga marasa kishin ƙasa, masu mummunar fata da karayar zuciya. Kuma manufarsa ita ce, su karkatar da hankalin Gwamna Nasir Idris daga ci gaba da gudanar da shirye-shiryen ayyukan ci gaban jihar. Kuma ina sha Allahu ba za su yi nasara ba.
__________
Malam Abdullahi Idris, Sadaukin Zuru, shi ne Mai Ba Gwamnan Jihar Kebbi Shawara Kan Harkoki Da Dubarun Sadarwa.













